Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Faburairu 2027 › Faburairu 16
Kalandar Ortodoks · 3 ga Faburairu (tsohon lissafi)
Karatun Orthodox na ranar — Faburairu 16, 2027
Talata · Mako na 38 bayan Fentekos · Sauti na 4
Bukukuwa da waliyyai
Afterfeast of the Meeting of the Lord
Azumi
Babu azumi
Wannan yana bin dokar gidan zuhudu. A cikin ikkilisiya, ana tsara gwargwadon azumi tare da mai sauraron furcin zunubi, bisa ga lafiya, shekaru da yanayi.
Karatun yini
Wasiƙa (domin Litinin)
21Ga wannan ne aka kira ku, domin Kiristi ya sha wahala dominku, ya bar muku gurbin da ya kamata ku bi. 22“Bai taɓa yin laifi ba sam, ba a kuma sami ƙarya a bakinsa ba.” 23Sa’ad da suka zazzage shi, bai rama ba; sa’ad da ya sha wahala, bai yi barazana ba. A maimakon haka, ya miƙa kansa ga wanda yake shari’ar adalci. 24Shi kansa ya ɗauki zunubanmu a jikinsa a kan itace, domin mu mutu ga zunubai mu kuma rayu ga adalci; ta wurin raunukansa ne kuka sami warkarwa. 25Gama dā kuna kama da tumakin da suka ɓace, amma yanzu kun dawo ga Makiyayi da kuma Mai lura da rayukanku. 3:1Haka ma, ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, domin in waɗansunsu ba su gaskata maganar ba, wataƙila a shawo kansu ba tare da magana ba 2sa’ad da suka ga rayuwarku mai tsabta da kuma na ladabi. 3Kyanku bai kamata yă zama na adon jiki ba, kamar kitso da sa kayan ado na zinariya da kuma sa kaya masu tsada. 4Maimakon haka, kyanku ya kamata yă zama ainihi na halinku na ciki, kyan da ba ya koɗewa na tawali’u da kuma na natsattsen ruhu, wanda yake mai daraja a gaban Allah. 5Gama haka matan masu tsarki na dā waɗanda suka sa begensu ga Allah suka yi wa kansu ado. Sun yi wa mazansu biyayya, 6kamar Saratu, wadda ta yi biyayya ga Ibrahim, har ta kira shi maigidanta. Ku ’ya’yanta ne mata in kun aikata abin da yake daidai, ba ku kuma ba tsoro dama ba. 7Mazan aure, ku ma, ku yi zaman sanin ya kamata yayinda kuke zama da matanku, ku girmama su a matsayin abokan zama marasa ƙarfi da kuma a matsayin magādan kyautar rai na alheri tare da ku, don kada wani abu yă hana addu’o’inku. 8A ƙarshe, dukanku ku zauna lafiya da juna; ku zama masu juyayi, kuna ƙaunar juna kamar ’yan’uwa, ku zama masu tausayi da kuma tawali’u. 9Kada ku rama mugunta da mugunta ko zagi da zagi, sai dai ku sa albarka, gama ga wannan ne aka kira ku, ku kuma gāji albarka.
Wasiƙa
10Gama, “Duk wanda yake so yă ji daɗin rayuwa, yă kuma ga kwanaki masu kyau dole yă ƙame harshensa daga mugunta leɓunansa kuma daga maganar yaudara. 11Dole yă juye daga mugunta, ya aikata nagarta; dole yă nemi salama yă kuma bi ta. 12Gama idanun Ubangiji suna a kan masu adalci kunnuwansa kuma suna jin addu’arsu, amma fuskar Ubangiji tana gāba da masu mugunta.” 13Wa zai yi muku lahani in kun himmantu ga yin nagarta? 14Amma ko da za ku sha wahala saboda abin da yake daidai, ku masu albarka ne. “Kada ku ji tsoron abin da suke tsoro; kada kuma ku firgita.” 15Sai dai a cikin zukatanku ku keɓe Kiristi a matsayin Ubangiji. A kullum, ku kasance a shirye ku ba da amsa ga duk wanda yake neman ku ba da dalilin wannan begen da kuke da shi. Amma ku yi wannan cikin tawali’u da ladabi, 16tare da lamiri mai kyau, saboda waɗanda suke maganganun banza a kan kyawawan ayyukanku cikin Kiristi su ji kunya da irin ɓata suna da suke yi. 17Ya fi kyau, in nufin Allah ne, a sha wahala don yin nagarta fiye da yin mugunta. 18Gama Kiristi ya mutu domin zunubi sau ɗaya tak, mai adalci saboda marasa adalci, don yă kawo ku ga Allah. An kashe shi a cikin jiki, amma an rayar da shi a Ruhu, 19ta wurin wanda kuma ya tafi ya yi wa ruhohin da suke a kurkuku wa’azi 20waɗanda dā ba su yi biyayya ba sa’ad da Allah ya jira da haƙuri a kwanaki Nuhu yayinda ake sassaƙa jirgi. A cikinsa mutane kima ne kawai, su takwas, aka kuɓutar ta ruwa, 21ruwan nan kuwa kwatancin baftisma ne da yanzu ya cece ku ku ma, ba kawar da dauda daga jiki ba, sai dai yin alkawari na lamiri mai kyau ga Allah. Ya cece ku ta wurin tashin Yesu Kiristi daga matattu, 22wanda ya tafi sama, yana kuma a hannun dama na Allah, mala’iku, mulkoki da kuma masu iko suna masa biyayya.
Wasiƙa (domin Waliyyi Siman da Waliyya Anna)
11Sa’ad da Kiristi ya zo a matsayin babban firist na kyawawan abubuwan da suka riga suka kasance a nan, ya bi ta cikin tabanakul mafi girma da kuma mafi cikakke wanda ba mutum ne ya yi ba, wato, ba na wannan halitta ba. 12Bai shiga ta wurin jinin awaki da na maruƙa ba; amma ya shiga Wuri Mafi Tsarki sau ɗaya tak ta wurin jininsa, bayan ya samo madawwamiyar fansa. 13In har akan yayyafa jinin awaki da na bijimai da kuma tokar karsanar a kan waɗanda suke marasa tsabta bisa ga al’ada, a tsarkake su yadda za su zama masu tsabta a waje, 14balle jinin Kiristi, wanda ta wurin Ruhu madawwami ya miƙa kansa marar aibi ga Allah, ai, zai tsabtacce lamirinmu daga ayyukan da suke kai ga mutuwa, don mu bauta wa Allah mai rai!
Bishara (domin Litinin)
13Daga baya, sai suka tura waɗansu Farisiyawa da mutanen Hiridus zuwa wurin Yesu, domin su sa masa tarko a cikin maganarsa. 14Suka zo wurinsa suka ce, “Malam, mun san kai mutum ne mai mutunci. Ba ka bin ra’ayin mutane, don ba ka nuna bambanci. Amma kana koyar da hanyar Allah bisa ga gaskiya. Daidai ne a biya wa Kaisar haraji, ko babu? 15Mu biya ko kada mu biya?” Amma Yesu ya san munafuncinsu, sai ya yi tambaya ya ce, “Don me kuke ƙoƙarin sa mini tarko? Ku kawo mini dinari in ga.” 16Suka kawo masa kuɗin, sai ya tambaye, su ya ce, “Hoton wane ne wannan? Kuma rubutun wane ne wannan?” Suka ce, “Na Kaisar.” 17Sai Yesu ya ce musu, “Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku ba wa Allah kuma abin da yake na Allah.” Suka yi mamakinsa ƙwarai.
Bishara
18Sa’an nan Sadukiyawa da suke cewa, babu tashin matattu, suka zo masa da tambaya. 19Suka ce, “Malam, Musa ya rubuta mana cewa, in ɗan’uwan wani mutum ya mutu, ya bar mata babu ’ya’ya, dole mutumin ya auri gwauruwar, yă kuma samo wa ɗan’uwansa ’ya’ya. 20To, an yi waɗansu ’yan’uwa guda bakwai. Na fari ya yi aure, ya mutu babu ’ya’ya. 21Na biyun ya auri gwauruwar, sai shi ma ya mutu, babu ’ya’ya. Haka kuma na ukun. 22A gaskiya, ba ko ɗaya daga cikin bakwai ɗin da ya bar ’ya’ya. Daga ƙarshe, macen ta mutu. 23To, a tashin matattu, matar wa za tă zama, don duk su bakwai nan sun aure ta?” 24Yesu ya ce, “Ashe, ba a cikin kuskure kuke ba saboda rashin sanin Nassi, ko ikon Allah? 25Sa’ad da matattu suka tashi, ba za su yi aure ba, ba kuwa za a ba da su ga aure ba. Za su zama kamar yadda mala’iku suke a cikin sama. 26Game da tashin matattu kuwa, ashe, ba ku karanta a cikin littafin Musa ba, game da labarin ɗan kurmin nan mai cin wuta da Musa ya gani a jeji, yadda Allah ya yi magana da shi ya ce, ‘Ni ne Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub’? 27Shi ba Allah na matattu ba ne, shi Allah na masu rai ne. Kun yi mummunan kuskure!”
Bishara (domin Waliyyi Siman da Waliyya Anna)
25To, akwai wani mutum a Urushalima mai suna Siman, shi mai adalci da kuma mai ibada. Yana jiran fansar Isra’ila, Ruhu Mai Tsarki kuwa yana tare da shi. 26An bayyana masa ta wurin Ruhu Mai Tsarki cewa ba zai mutu ba sai ya ga Kiristi na Ubangiji. 27Da Ruhu ya iza shi, sai ya shiga cikin filin haikali. Sa’ad da iyayen suka kawo jaririn nan Yesu don su yi masa abin da al’adar Doka ta bukaci, 28sai Siman ya karɓi yaron a hannuwansa ya yabi Allah, yana cewa, 29“Ya Ubangiji Mai Iko Duka, kamar yadda ka yi alkawari, yanzu ka sallami bawanka lafiya. 30Gama idanuna sun ga cetonka, 31wanda ka shirya a gaban dukan mutane, 32haske don bayyanawa ga Al’ummai da kuma ɗaukaka ga mutanenka Isra’ila.” 33Mahaifin yaron da kuma mahaifiyarsa suka yi mamaki abin da aka faɗa game da shi. 34Sa’an nan Siman ya sa musu albarka ya ce wa Maryamu mahaifiyarsa, “An ƙaddara yaron nan yă zama sanadin fāɗuwa da tashin mutane da yawa a Isra’ila, zai kuma zama alamar da mutane ba za su so ba, 35ta haka za a fallasa tunanin zukatan mutane da yawa. Ke ma, takobi zai soki zuciyarki.” 36Akwai wata annabiya ma, mai suna Anna, diyar Fanuwel, na kabilar Asher. Ta tsufa kutuf; ta yi zama da mijinta shekaru bakwai bayan sun yi aure, 37ta kuwa zama gwauruwa sai da ta kai shekaru tamanin da huɗu. Ba ta taɓa barin haikali ba, tana sujada dare da rana, tana kuma azumi da addu’a. 38Tana haurawa wurinsu ke nan a wannan lokaci, sai ta yi wa Allah godiya ta kuma yi magana game da yaron nan ga dukan waɗanda suke sauraron fansar Urushalima.
Kwanakin suna bin kalandar Julian ta Ikilisiyar Rasha (kamar Ikilisiyoyin Serbia da Georgia da Dutsen Athos): Faburairu 3 a kalandar ikilisiya shi ne Faburairu 16 a kalandar gari. Ikilisiyoyin da ke amfani da sabuwar kalanda (Girka, Romania, Bulgaria, Ukraine…) suna yin bukukuwan da ba sa canzawa da na tsarkaka a ainihin ranar gari, kwanaki 13 kafin haka, kuma wasu karatunsu sun bambanta; Ista da kwanakin da suka dogara da ita iri ɗaya ne.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi