Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Faburairu 2027 › Faburairu 16
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Faburairu 16, 2027
Talata · Mako na 1 na lokacin Azumi
Bukukuwa da waliyyai
Talata a mako na 1 na lokacin Azumi
Ranar mako · Launin ibada: shunayya
Karatun yini
Karatu na farko
10Kamar yadda ruwan sama da dusar ƙanƙara suke saukowa daga sama, ba sa komowa ba tare da sun jiƙe duniya sun kuma sa su yi ’ya’ya su kuma yi toho, don su ba da iri ga mai shuki da kuma abinci ga mai ci, 11haka maganata da take fitowa daga bakina. Ba za tă koma gare ni wofi ba, amma za tă cika abin da nake so ta kuma cika abin da na aike ta tă yi.
Zaburar amsawa
3Ku ɗaukaka Ubangiji tare da ni; bari mu ɗaukaka sunansa tare. 4Na nemi Ubangiji, ya kuwa amsa mini; ya cece ni daga dukan tsoro. 5Waɗanda suke dubansa sukan haskaka; fuskokinsu ba sa rufuwa da kunya. 6Wannan matalauci ya yi kira, Ubangiji kuwa ya ji shi; ya cece shi daga dukan wahalarsa. 15Idanun Ubangiji suna a kan masu adalci kuma kunnuwansa suna sauraran kukansu; 16fuskar Ubangiji yana gāba da waɗanda suke aikata mugunta, don yă sa a manta da su a duniya. 17Adalai kan yi kuka, Ubangiji kuwa yakan ji su; yakan cece su daga dukan wahalarsu. 18Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai ya kuma cece waɗanda aka ragargaza a ruhu.
Bishara
7Sa’ad da kuma kuke addu’a, kada ku yi ta maimaita magana, kamar marasa sanin Allah, domin suna tsammani za a ji su saboda yawan maganarsu. 8Kada ku zama kamar su, gama Ubanku ya san abin da kuke bukata kafin ma ku roƙe shi. 9“To, ga yadda ya kamata ku yi addu’a. “ ‘Ubanmu wanda yake cikin sama, a tsarkake sunanka, 10mulkinka yă zo a aikata nufinka a duniya kamar yadda ake yi a sama. 11Ka ba mu yau abincin yininmu. 12Ka gafarta mana laifofinmu, kamar yadda mu ma muke gafarta wa masu yin mana laifi. 13Kada ka bari a kai mu cikin jarraba, amma ka cece mu daga mugun nan. ’ 14Gama in kuna yafe wa mutane sa’ad da suka yi muku laifi, Ubanku da yake cikin sama ma zai gafarta muku. 15Amma in ba kwa yafe wa mutane laifofinsu, Ubanku ma ba zai gafarta muku zunubanku ba.
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi