Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Nuwamba 2026 › Nuwamba 8
Kalandar Ortodoks · 26 ga Oktoba (tsohon lissafi)
Karatun Orthodox na ranar — Nuwamba 8, 2026
Lahadi · Sauti na 6
Bukukuwa da waliyyai
Lahadi ta 23 bayan Fentekos
Azumi
Babu azumi
Wannan yana bin dokar gidan zuhudu. A cikin ikkilisiya, ana tsara gwargwadon azumi tare da mai sauraron furcin zunubi, bisa ga lafiya, shekaru da yanayi.
Karatun yini
Addu’ar yamma: karatu
15Ka duba daga sama ka gani daga kursiyinka da yake bisa, mai tsarki da kuma mai ɗaukaka. Ina kishinka da kuma ikonka? Ka janye juyayi da kuma tausayin da kake yi mana daga gare mu. 16Amma kai Ubanmu ne, ko Ibrahim bai san mu ba Isra’ila kuma bai yarda da mu ba; kai, ya Ubangiji, kai ne Ubanmu, Mai Fansarmu tun fil azal ne sunanka. 17Don me, ya Ubangiji, ka sa muna barin hanyoyinka muka kuma taurare zukatanmu don kada mu girmama ka? Ka komo domin darajar bayinka, kabilan da suke abin gādonka. 18Gama a ɗan lokaci mutanenka suka mallaki wurinka mai tsarki, amma yanzu abokan gābanmu sun tattake wurinka mai tsarki. 19Mu naka tun fil azal; ba ka taɓa yin mulki a kansu ba, ba a taɓa kira su da sunanka ba. 64:1Da ma za ka tsage sammai ka sauko, ai, da duwatsu za su yi rawar jiki a gabanka! 2Kamar sa’ad da wuta takan ci rassa ta sa ruwa ya tafasa, ka sauko ka sanar da sunanka ga abokan gābanka ka kuma sa al’ummai su yi rawan jiki a gabanka! 3Gama sa’ad da ka aikata abubuwan bantsoron da ba mu sa tsammani ba, ka sauko, duwatsu kuma suka yi rawar jiki a gabanka. 4Tun fil azal babu wanda ya taɓa ji, babu kunnen da ya gane, babu idon da ya ga wani Allah in ban da kai, wanda ya aikata waɗannan al’amura a madadin waɗanda suke sa zuciya a gare shi. 5Kakan taimaki waɗanda suke murnan yin abin da yake daidai, waɗanda sukan tuna da hanyoyinka. Amma sa’ad da muka ci gaba da yin zunubi, kakan yi fushi. Ta yaya za mu sami ceto ke nan? 8Duk da haka, Ubangiji, kai ne Ubanmu. Mu yumɓu ne, kai kuma mai ginin tukwane; dukanmu aikin hannunka ne. 9Kada ka yi fushi fiye da kima, ya Ubangiji; kada ka tuna da zunubanmu har abada. Da ma ka dube mu, muna roƙonka, gama dukanmu mutanenka ne.
Addu’ar yamma: karatu
2“Tafi ka yi shela a kunnuwar Urushalima cewa, “ ‘Na tuna da amincin ƙuruciyarki, yadda kamar amarya kika ƙaunace ni kika kuma bi ni cikin hamada, cikin ƙasar da ba a yi shuka ba. 3Isra’ila tsattsarka ce ga Ubangiji, nunan fari na girbinsa; dukan waɗanda suka cinye ta an same su da laifi, masifa kuwa ta same su,’ ” in ji Ubangiji. 4Ka saurari maganar Ubangiji, ya gidan Yaƙub, dukanku zuriyar gidan Isra’ila. 5Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Wane laifi ne kakanninku sun same ni da shi, da suka tsaya nesa da ni? Sun bi gumakan banza su kansu suka kuma zama banza da kansu. 6Ba su yi tambaya, ‘Ina Ubangiji, wanda ya fitar da su daga Masar ya bishe su cikin jeji cikin hamada da kwazazzabai ƙasa mai fări da kuma duhu, ƙasar da ba kowa mai ratsa ta ba kowa kuma mai zama a cikinta?’ 7Na kawo ku zuwa ƙasa mai albarka don ku ci amfaninta da abubuwa masu yalwar da take bayarwa. Amma kuka zo kuka ƙazantar da ƙasata kuka kuma mai da gādona abin ƙyama. 8Firistoci ba su yi tambaya, ‘Ina Ubangiji ba.’ Waɗanda suke amfani da doka ba su san ni ba; shugabanni suka yi mini tawaye. Annabawa suka yi annabci ta wurin Ba’al, suna bin gumakan banza. 9“Saboda haka ina sāke tuhumarku,” in ji Ubangiji. “Zan kuma tuhumi ’ya’ya ’ya’yanku. 10Ku ƙetare zuwa tsibiran Kittim ku gani, ku aika zuwa Kedar ku duba da kyau; ku ga ko an taɓa yin wani abu haka. 11Akwai wata al’ummar da ta canja allolinta? (Duk da haka su ba alloli ba ne sam.) Amma mutanena sun musayar da ɗaukakarsu da gumakan banza. 12Ku girgiza saboda wannan, ya sammai, ku kuma razana don tsoro mai girma,” in ji Ubangiji.
Addu’ar yamma: karatu
Ba ya cikin wannan fassara
Bisharar addu’ar asuba ta 1
16Sa’an nan almajiransa goma sha ɗaya, suka tafi Galili, suka je dutsen da Yesu ya gaya musu. 17Da suka gan shi, sai suka yi masa sujada, amma waɗansu suka yi shakka. 18Sai Yesu ya zo wurinsu ya ce, “An ba ni dukan iko a sama da kuma ƙasa. 19Saboda haka ku tafi, ku mai da dukan al’umman duniya su zama almajiraina, kuna yi musu baftisma a cikin sunan Uba, da na Ɗa, da na Ruhu Mai Tsarki, 20kuna kuma koya musu, su yi biyayya da duk abin da na umarce ku, kuma tabbatacce, ina tare da ku kullum, har ƙarshen zamani.”
Wasiƙa
4Amma saboda yawan ƙaunar da yake mana, Allah, wanda yake mai yawan jinƙai, 5ya ba mu rai sa’ad da ya tashe Kiristi daga matattu. Ta wurin alherin Allah ne aka cece ku. 6Allah ya tashe mu tare da Kiristi, ya kuma ba mu wurin zama tare da shi a cikin mulkin samaniya. 7Allah ya yi haka domin a tsararraki masu zuwa yă nuna yalwar alherinsa da ya wuce misali, an bayyana alheransa da ya yi mana ta wurin Kiristi Yesu. 8Allah ya cece ku ta wurin alheri sa’ad da kuka ba da gaskiya. Wannan kuwa ba yinku ba ne, kyauta ce daga Allah. 9Ba kuwa saboda aikin lada ba, don kada wani yă ɗaga kai. 10Ai, mu aikinsa ne, an sāke halittarmu a cikin Kiristi Yesu musamman domin mu yi kyawawan ayyuka, waɗanda Allah ya tanadar mana tun da fari, mu yi.
Wasiƙa (domin girgizar ƙasa)
6domin Ubangiji yakan hori waɗanda yake ƙauna, yakan kuma hori duk wanda yakan karɓa a matsayin ɗa.” 7Ku jimre shan wahala a matsayin horo; Allah yana yi da ku kamar ’ya’ya. Gama wane ɗa ne mahaifinsa ba ya horonsa? 8In ba a hore ku ba (kowa kuwa yakan sami horo), to, ku shegu ne ba ’ya’yan gida ba. 9Ban da haka ma, dukanmu mun kasance da ubannin jiki waɗanda suka hore mu muka kuma yi musu ladabi. Ashe, bai kamata mu yi wa Uban ruhohinmu biyayya mu kuwa rayu ba! 10Ubanninmu sun hore mu na ɗan lokaci yadda suka ga ya fi kyau; amma Allah yakan hore mu don amfaninmu, domin mu sami rabo cikin tsarkinsa. 11Babu horon da yake da daɗi a lokacin da ake yinsa, sai dai zafi. Amma daga baya waɗanda suka horu ta haka sukan sami kwanciyar rai wadda aikin adalci yake bayarwa. 12Saboda haka, sai ku ƙarfafa raunanan hannuwanku da gwiwoyinku marasa ƙarfi! 13“Ku shirya hanyoyi marasa gargaɗa saboda ƙafafunku,” don kada guragu su daɗa gurguntawa, sai dai su warke. 25Ku lura fa kada ku ƙi wanda yake magana. Gama in su ba su tsira sa’ad da suka ƙi wanda ya gargaɗe su a wannan duniya ba, to, ƙaƙa mu za mu tsira, in mun ƙi jin wannan da yake yi mana gargaɗi daga Sama? 26A lokacin nan muryarsa ta jijjiga duniya, amma yanzu ya yi alkawari cewa, “Har wa yau sau ɗaya tak zan ƙara jijjiga ba duniya kaɗai ba, amma har ma da sammai.” 27Wannan magana “sau ɗayan nan” sun nuna, kawar da abin da za a iya jijjigawa, wato, ƙirƙiro abubuwa, saboda abubuwan da ba a iya jijjigawa, su kasance.
Wasiƙa (domin Waliyyi Demetrius)
1Kai kuma, ɗana, ka yi ƙarfi cikin alherin da yake cikin Kiristi Yesu. 2Abubuwan da ka ji na faɗa a gaban shaidu masu yawa kuwa ka danƙa wa amintattun mutane waɗanda su ma za su iya koya wa waɗansu. 3Ka jure wa shan wahala tare da mu kamar soja mai kyau na Kiristi Yesu. 4Ba wanda yake aikin soja da zai sa kansa a sha’anin mutumin da ba ya aikin soja, domin yakan so yă gamshi wanda ya ɗauke shi soja. 5Haka ma, in wani ya yi gasa a matsayi shi ɗan wasa ne, ba ya sami rawanin nasara, sai in ya yi gasar bisa ga dokoki. 6Manomi mai aiki sosai ya kamata yă zama na fari wajen samun rabon amfanin gona. 7Ka yi tunani a kan abin da nake faɗi, gama Ubangiji zai ba ka ganewa cikin dukan wannan. 8Ka tuna da Yesu Kiristi, wanda aka tā da shi daga matattu, zuriyar Dawuda, wanda shi ne bisharata, 9wadda nake shan wahala har ga daurin sarƙa kamar mai laifi. Amma Maganar Allah ba a daure take ba. 10Saboda haka nake jure kome saboda zaɓaɓɓu, domin su ma su sami ceton da yake cikin Kiristi Yesu, tare da madawwamiyar ɗaukaka.
Bishara
19“An yi wani mutum mai arziki wanda yakan sa tufafi masu ruwan shunayya, da kuma na lallausan lilin, yana kuma cikin rayuwar jin daɗi kullum. 20A ƙofar gidansa kuma akan ajiye wani mai bara, mai suna Lazarus, wanda jikinsa duk gyambuna ne. 21Shi kuwa yakan yi marmarin cin abin da yakan fāɗi daga tebur na mai arzikin nan. Har karnuka ma sukan zo su lashe gyambunansa. 22“Ana nan, sai mai baran ya mutu, kuma mala’iku suka ɗauke shi zuwa gefen Ibrahim. Mai arzikin ma ya mutu, aka kuma binne shi. 23A cikin jahannama ta wuta, inda yana shan azaba, ya ɗaga kai ya hangi Ibrahim can nesa, da kuma Lazarus a gefensa. 24Sai ya yi masa kira ya ce, ‘Baba, Ibrahim, ka ji tausayina, ka aiki Lazarus ya sa ɗan yatsarsa a ruwa, ya ɗiga mini a harshe saboda in ji sanyi, domin ina shan azaba cikin wannan wuta.’ 25“Amma Ibrahim ya ce, ‘Ka tuna fa ɗana, a lokacin da kake duniya, ka sami abubuwa masu kyau naka, Lazarus kuwa ya sami munanan abubuwa. Amma yanzu ya sami ta’aziyya a nan, kai kuwa kana shan azaba. 26Ban da wannan duka ma, tsakaninmu da kai, akwai wani babban rami da aka yi, yadda waɗanda suke son ƙetarewa daga nan zuwa wurinku, ba za su iya ba, kuma ba mai iya ƙetarewa daga wurinku zuwa wurinmu.’ 27“Ya amsa ya ce, ‘To, ina roƙonka, ya uba, ka aiki Lazarus zuwa gidan mahaifina, 28gama ina da ’yan’uwana biyar maza. Bari yă ba su gargaɗi, don kada su ma su zo wurin nan mai azaba.’ 29“Ibrahim ya amsa ya ce, ‘Suna da Musa da Annabawa, ai, sai su saurare su.’ 30“Sai ya ce, ‘A’a, ya uba, Ibrahim, in dai wani ya tashi daga matattu ya je wurinsu, za su tuba.’ 31“Amma ya ce masa, ‘In ba su saurari Musa da Annabawa ba, kai, ko da wani ya tashi daga matattu ma, ba za su saurare shi ba.’ ”
Bishara (domin girgizar ƙasa)
23Sai ya shiga jirgin ruwa, almajiransa kuwa suka bi shi. 24Ba zato ba tsammani, sai wani babban hadari ya taso a tafkin, har raƙuman ruwan suka sha kan jirgin. Amma Yesu yana barci. 25Almajiran suka je suka tashe shi, suna cewa, “Ubangiji, ka cece mu! Za mu nutse!” 26Ya amsa ya ce, “Ku masu ƙarancin bangaskiya, me ya sa kuke tsoro haka?” Sa’an nan ya tashi ya tsawata wa iskar da kuma raƙuman ruwan, sai wuri ya yi tsit gaba ɗaya. 27Mutanen suka yi mamaki suka ce, “Wane irin mutum ne wannan? Har iska da raƙuman ruwa suna masa biyayya!”
Bishara (domin Waliyyi Demetrius)
17Umarnina ke nan. Ku ƙaunaci juna. 18“In duniya ta ƙi ku, ku san cewa ta fara ƙin na ne. 19Da ku na duniya ne, da ta ƙaunaci abinta. Kamar yadda yake, ku ba na duniya ba ne, na zaɓe ku daga duniya, shi ya sa duniya take ƙinku. 20Ku tuna da kalmomin da na yi muku cewa, ‘Ba bawan da ya fi maigidansa,’ In sun tsananta mini, ku ma za su tsananta muku. Da sun yi biyayya da koyarwata, da za su yi biyayya da taku ma. 21Za su yi muku haka saboda sunana, gama ba su san Wannan da ya aiko ni ba. 22Da a ce ban zo na yi musu magana ba, da ba su da zunubi. Yanzu kam, ba su da wata hujja a kan zunubinsu. 23Wanda ya ƙi ni ya ƙi ya ƙi Ubana ma. 24Da a ce ban yi ayyuka a cikinsu waɗanda babu wani da ya taɓa yi ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu sun ga waɗannan ayyukan banmamaki, duk da haka sun ƙi ni sun kuma ƙi Ubana. 25Amma wannan ya faru ne domin a cika abin da yake a rubuce cikin Dokarsu cewa, ‘Sun ƙi ni ba dalili.’ 26“Sa’ad da Mai Taimako ya zo, wanda zan aiko muku daga wurin Uba, Ruhun gaskiya wanda yake fitowa daga wurin Uba, zai ba da shaida game da ni. 27Ku ma dole ku ba da shaida, domin kun kasance tare da ni tun daga farko. 16:1“Na faɗa muku wannan duka, domin kada ku bauɗe. 2Za su kore ku daga majami’a; lalle, lokaci yana zuwa da duk wanda ya kashe ku, zai ɗauka yana yin wa Allah hidima ne.
Kwanakin suna bin kalandar Julian ta Ikilisiyar Rasha (kamar Ikilisiyoyin Serbia da Georgia da Dutsen Athos): Oktoba 26 a kalandar ikilisiya shi ne Nuwamba 8 a kalandar gari. Ikilisiyoyin da ke amfani da sabuwar kalanda (Girka, Romania, Bulgaria, Ukraine…) suna yin bukukuwan da ba sa canzawa da na tsarkaka a ainihin ranar gari, kwanaki 13 kafin haka, kuma wasu karatunsu sun bambanta; Ista da kwanakin da suka dogara da ita iri ɗaya ne.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi