Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Nuwamba 2026 › Nuwamba 8

Kalandar Katolika

Karatun Mass (Katolika) — Nuwamba 8, 2026

Lahadi · Mako na 32 na lokacin yau da kullum

Bukukuwa da waliyyai

Lahadi ta 32 ta lokacin yau da kullum

Lahadi · Launin ibada: kore

Karatun yini

Karatu na farko

Ba ya cikin wannan fassara

Zaburar amsawa

Zab 63:1–7

1Zabura ta Dawuda. Sa’ad da yake a hamadar Yahuda. Ya Allah, kai ne Allahna, da nacewa na neme ka; raina yana ƙishinka, jikina yana marmarinka, cikin busasshiyar ƙasar da ta zozaye inda babu ruwa. 2Na gan ka a wuri mai tsarki na kuma dubi ikonka da ɗaukakarka. 3Domin ƙaunarka ta fi rai kyau, leɓunana za su ɗaukaka ka. 4Zan yabe ka muddin raina, kuma a cikin sunanka zai ɗaga hannuwana. 5Raina zai ƙoshi kamar da abinci mafi kyau; da leɓunan rerawa bakina zai yabe ka. 6A gadona na tuna da kai; ina tunaninka dukan dare. 7Domin kai ne mai taimakona, ina rera a cikin inuwar fikafikanka.

Karatu na biyu

1Tes 4:13–18

13’Yan’uwa, ba ma so ku kasance cikin jahilci game da waɗanda suka yi barci, ko kuwa ku yi baƙin ciki kamar sauran mutanen da ba su da bege. 14Mun gaskata cewa Yesu ya mutu ya tashi kuma daga matattu, ta haka muka gaskata cewa Allah zai kawo waɗanda suka yi barci a cikinsa tare da Yesu. 15Bisa ga maganar Ubangiji kansa, muna gaya muku cewa mu da muke raye har yanzu, waɗanda aka bari har dawowar Ubangiji, tabbatacce ba za mu riga waɗanda suka yi barci tashi ba. 16Gama Ubangiji kansa zai sauko daga sama, da umarni mai ƙarfi, da muryar babban mala’ika da kuma busar ƙahon Allah, waɗanda suka mutu kuwa cikin Kiristi za su tashi da farko. 17Bayan haka, mu da muke da rai da aka bari, za a ɗauke mu tare da su a cikin gizagizai don mu sadu da Ubangiji a sararin sama. Ta haka za mu kasance tare da Ubangiji har abada. 18Saboda haka ku ƙarfafa juna da waɗannan kalmomi.

Bishara

Mat 25:1–13

1“A lokacin mulkin sama zai zama kamar budurwai goma waɗanda suka ɗauki fitilunsu suka fita don su taryi ango. 2Biyar daga cikinsu wawaye ne, biyar kuma masu hikima. 3Wawayen sun ɗauki fitilunsu, sai dai ba su riƙe mai ba. 4Masu hikimar kuwa suka riƙo tulunan mai da fitilunsu. 5Ango ya yi jinkirin zuwa, sai duk suka shiga gyangyaɗi har barci ya kwashe su. 6“Can tsakar dare, sai aka ji kira, ana cewa, ‘Ga ango nan! Ku fito, ku tarye shi!’ 7“Sai dukan budurwan nan suka farka suka kuna fitilunsu. 8Sai wawayen suka ce wa masu hikimar, ‘Ku ɗan sassam mana manku; fitilunmu suna mutuwa.’ 9“Su kuwa suka amsa, suka ce, ‘A’a, wataƙila ba zai ishe mu da ku ba. Gara ku je wurin masu sayarwa ku sayo.’ 10“Amma yayinda suke kan tafiya garin sayen mai, sai ango ya iso. Budurwai da suke a shirye, suka shiga wajen bikin auren tare da shi. Aka kuma kulle ƙofa. 11“An jima can, sai ga sauran sun iso. Suka ce, ‘Ranka yă daɗe! Ranka yă daɗe! Ka buɗe mana ƙofa!’ 12“Amma ya amsa ya ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, ban san ku ba.’ 13“Saboda haka sai ku zauna a faɗake, don ba ku san ranar ko sa’ar ba.

Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi A, shekarar ranakun mako II.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi