Bible Explorer

Bincika › Sarakuna da Tarihi gefe da gefe › Shawulu da Dawuda

Sarakuna da Tarihi gefe da gefe · Shawulu da Dawuda

Jarumawan Dawuda

2Sam 23:8–39 · 1Tar 11:10–47

2 Sama’ila

2Sam 23:8–39

8Waɗannan su ne sunayen jarumawan Dawuda. Yosheb-Basshebet, mutumin Takemon ɗaya daga cikin shugabanni Uku; ya ɗaga māshinsa ya kashe mutum ɗari takwas a lokaci guda.

9Na biye da shi a matsayi cikin jarumawa ukun nan, shi ne Eleyazar ɗan Dodo, mutumin Aho. Eleyazar ya kasance tare da Dawuda sa’ad da suka fuskanci Filistiyawa waɗanda suka taru a Fas Dammim don yaƙi. Mutanen Isra’ila suka gudu,

10amma ya yi tsayi daka, ya bugi Filistiyawa sai da hannunsa ya gaji har ya liƙe wa māshinsa. Ubangiji kuwa ya sa aka yi babban nasara a ranar. Sauran sojoji suka komo wurin Eleyazar, don kawai su washe ganima.

11Na biye da Agiyi a matsayi, shi ne Shamma ɗan Agi, mutumin Harar. Sa’ad da Filistiyawa suka taru a wani wurin da take gona cike da waken barewa, sai rundunar Isra’ila suka gudu daga Filistiyawa.

12Amma Shamma ya yi tsayi daka a tsakiyar gonar. Ya kāre ta, ya kuma bugi Filistiyawa, Ubangiji kuwa ya sa aka yi babban nasara.

13A lokacin girbi, uku daga cikin shugabanni talatin suka gangaro zuwa wurin Dawuda a kogon Adullam. A lokacin kuwa sojojin Filistiyawa sun kafa sansani a Kwarin Refayim.

14Dawuda kuwa yana a mafaka. Wata ƙungiyar sojojin Filistiyawa kuma suna Betlehem.

15Dawuda ya ji ƙishirwa, sai ya ce, “Kash, da a ce wani yă samo mini ruwa daga rijiyar da take kusa da bakin ƙofar Betlehem mana!”

16Sai jarumawa ukun nan suka yi kukan ƙura, suka sheƙa a guje suka ratsa cikin sansanin Filistiyawa, suka ɗebo ruwa daga rijiyar da take kusa da bakin ƙofar Betlehem, suka kawo wa Dawuda. Amma Dawuda ya ƙi yă sha; a maimako sai ya zuba shi a gaban Ubangiji.

17Sai ya ce, “ Ubangiji yă sawwaƙe, in yi sha! Ba jinin mutanen da suka tafi a bakin ransu ba ne?” Dawuda kuwa bai sha ruwan ba. Irin abubuwan da jarumawa ukun nan suka yi ke nan.

18Abishai, ɗan’uwan Yowab, ɗan Zeruhiya shi shugaban Ukun nan. Ya ɗauki māshinsa ya kashe mutane ɗari uku, ta haka ya zama sananne kamar Ukun nan.

19Ashe, ba a girmama shi fiye da Ukun ba? Ya zama komandansu, ko da yake ba a haɗa shi a cikinsu ba.

20Benahiya, ɗan Yehohiyada mutumin Kabzeyel shi ma jarumi ne sosai, ya yi nasarori masu yawa. Ya bugi ƙwararrun jarumawan Mowab guda biyu. Ya kuma shiga rami wata ranar da ake ƙanƙara, ya kashe zaki.

21Ya kuma buge wani jibgaggen mutumin Masar. Duk da māshin da mutumin Masar yana riƙe a hannunsa, Benahiya ya kai masa hari da kulki. Ya ƙwace māshin daga hannunsa, ya kuma kashe shi da māshin.

22Irin nasarorin da Benahiya ɗan Yehohiyada ya yi ke nan; shi ma jarumi ne sosai kamar jarumawan nan uku.

23Aka fi ba shi girma fiye da talatin ɗin nan, amma ba ya cikin ukun. Dawuda ya sa shi yă zama ɗaya daga cikin masu tsaron lafiyarsa.

24Cikin talatin ɗin kuwa akwai, Asahel, ɗan’uwan Yowab, Elhanan, ɗan Dodo mutumin Betlehem,

25Shamma, mutumin Harod, Elika, mutumin Harod,

26Helez, mutumin Falti, Ira, ɗan Ikkesh mutumin Tekowa,

27Abiyezer, mutumin Anatot, da Mebunnai, mutumin Husha,

28Zalmon, mutumin Aho, da Maharai, mutumin Netofa,

29Heleb, ɗan Ba’ana daga Netofa, Ittai, ɗan Ribai mutumin Gibeya a Benyamin,

30Benahiya, mutumin Firaton, da Hiddai, daga rafuffukan Ga’ash,

31Abi-Albon, mutumin Arba, da Azmawet, mutumin Bahurim,

32Eliyaba, mutumin Sha’albo, ’Ya’yan Yashen, Yonatan,

33ɗan Shamma mutumin Harar, da Ahiyam, ɗan Sharar mutumin Harod.

34Elifelet, ɗan Ahasbai mutumin Ma’aka, Eliyam, ɗan Ahitofel mutumin Gilo,

35Hezro, mutumin Karmel, Fa’arai, mutumin Arbi,

36Igal, ɗan Natan mutumin Zoba, ɗan Hagiri,

37Zelek, mutumin Ammon Naharai, mutumin Beyerot mai ɗaukan wa Yowab, ɗan Zeruhiya makamai,

38Ira, mutumin Itra. Gareb, mutumin Itra,

39da kuma Uriya, mutumin Hitti. Su talatin da bakwai ne duka.

1 Tarihi

1Tar 11:10–47

10Waɗannan su ne manyan jarumawan Dawuda, su ne, tare da dukan Isra’ila, suka ba wa mulkinsa goyon baya mai ƙarfi da ya kai bisa dukan ƙasar, yadda Ubangiji ya yi alkawari.

11Ga jerin sunayen jarumawan Dawuda. Yashobeyam wani ɗan Hakmoni, shi ne babban shugaba; ya ɗaga māshinsa a kan mutum ɗari uku, waɗanda ya kashe a ƙarawa guda kawai.

12Biye da shi, shi ne Eleyazar ɗan Dodo mutumin Aho, ɗaya daga cikin jarumawa uku.

13Yana tare da Dawuda a Fas Dammim sa’ad da Filistiyawa suka taru can don yaƙi. A wani wuri inda akwai gona cike da sha’ir, sojoji suka gudu daga Filistiyawa.

14Sai shi da Dawuda suka shiga gonar sha’ir ɗin, suka tsaya ciki don su tsare ta. Suka ragargaza Filistiyawa, Ubangiji kuma ya kawo babban nasara.

15Wata rana uku cikin manyan mutanen nan talatin suka gangara wurin Dawuda zuwa dutse a kogon Adullam, yayinda ƙungiyar Filistiyawa suke sansani a Kwarin Refayim.

16A lokacin Dawuda yana cikin mafaka, sojojin Filistiyawa kuma suna a Betlehem.

17Dawuda ya ji marmarin ruwan sha sai ya ce, “Kash, a ce wani zai sami mini ruwan sha daga rijiya kusa da ƙofar Betlehem mana!”

18Sai Ukun suka kutsa kai cikin sansanin Filistiyawa, suka ja ruwa daga rijiyar da take kusa da ƙofar Betlehem suka ɗauko shi suka kawo wa Dawuda. Amma ya ƙi yă sha; a maimako, sai ya zubar da shi a gaban Ubangiji.

19Ya ce, “Allah yă sawwaƙe in yi haka, ya kamata in sha jinin waɗannan mutanen da suka yi kasai da rayukansu?” Domin sun yi kasai da rayukansu don su dawo da shi, Dawuda bai sha shi ba. Irin abubuwan da jarumawa ukun nan suka yi ke nan.

20Abishai ɗan’uwan Yowab shi ma babba ne cikin Ukun nan. Ya ɗaga māshinsa a kan mutum ɗari uku, waɗanda ya kashe, ya kuma zama sananne kamar Ukun.

21Aka ninka girmama shi bisa Ukun, sai ya zama shugaba, ko da yake ba a haɗa shi a cikinsu ba.

22Benahiya ɗan Yehohiyada shi ma wani barden yaƙi ne daga Kabzeyel, wanda ya yi manyan abubuwa. Ya bugi gwanayen Mowab biyu. Ya kuma gangara zuwa cikin rami a ranar da aka yi dusar ƙanƙara ya kashe zaki.

23Ya kuma kashe wani mutumin Masar mai tsayi ƙafa bakwai da rabi. Ko da yake mutumin Masar yana da māshi kamar sandan masaƙa a hannunsa, Benahiya ya yaƙe shi da kulki. Ya ƙwace māshin daga hannun mutumin Masar ya kuma kashe shi da māshin nan nasa.

24Irin abubuwan da Benahiya ɗan Yehohiyada ya yi ke nan; shi ma sananne ne kamar waɗannan jarumawa uku.

25Aka ɗauka shi da bangirma fiye da Talatin nan, amma ba a haɗa shi cikin Ukun ba. Dawuda kuwa ya sa shi yă lura da masu tsaron lafiyarsa.

26Jarumawan nan su ne, Asahel ɗan’uwan Yowab, Elhanan ɗan Dodo daga Betlehem,

27Shammot mutumin Haror, Helez mutumin Felon,

28Ira ɗan Ikkesh daga Tekowa, Abiyezer daga Anatot,

29Sibbekai mutumin Husha, Ilai mutumin Aho,

30Maharai mutumin Netofa, Heled ɗan Ba’ana mutumin Netofa,

31Ittai ɗan Ribai daga Gibeya a Benyamin, Benahiya mutumin Firaton,

32Hurai daga kogunan Ga’ash, Abiyel mutumin Arba,

33Azmawet mutumin Harum, Eliyaba mutumin Sha’albo,

34’ya’yan Hashem mutumin Gizon maza, Yonatan ɗan Shageye mutumin Harar,

35Ahiyam ɗan Sakar mutumin Harar, Elifal ɗan Ur,

36Hefer mutumin Mekerat, Ahiya mutumin Felon,

37Hezro mutumin Karmel, Na’arai ɗan Ezbai,

38Yowel ɗan’uwan Natan, Mibhar ɗan Hagiri,

39Zelek mutumin Ammon Naharai Baroti, mai ɗaukar kayan yaƙin Yowab ɗan Zeruhiya,

40Ira mutumin Itra, Gareb mutumin Itra,

41Uriya mutumin Hitti Zabad ɗan Alai,

42Adina ɗan Shiza mutumin Ruben, wanda shi ne babba na mutanen Ruben, kuma talatin suna tare da shi,

43Hanan ɗan Ma’aka, Yoshafat mutumin Mit,

44Uzziya mutumin Ashtarot, Shama da Yehiyel ’ya’yan Hotam mutumin Arower maza,

45Yediyayel ɗan Shimri, ɗan’uwansa Yoha mutumin Tiz,

46Eliyel mutumin Ma’aha, Yeribai da Yoshawiya ’ya’yan Elna’am maza, Itma mutumin Mowab,

47Eliyel, Obed da Ya’asiyel mutumin Mezob.

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY