Bible Explorer

Bincika › Sarakuna da Tarihi gefe da gefe › Shawulu da Dawuda

Sarakuna da Tarihi gefe da gefe · Shawulu da Dawuda

Addu’ar Dawuda

2Sam 7:18–29 · 1Tar 17:16–27

2 Sama’ila

2Sam 7:18–29

18Sa’an nan Sarki Dawuda ya je ya zauna a gaban Ubangiji ya ce, “Wane ne ni, ya Ubangiji Mai Iko Duka, ko gidana, har da ka ɗaga mu zuwa wannan matsayi?

19Har ya zama kamar wannan bai isa ba a gabanka, ya Ubangiji Mai Iko Duka, ka kuma yi magana game da nan gaba na gidan bawanka. Haka ka saba yi da mutane, ya Ubangiji Mai Iko Duka?

20“Me kuma Dawuda zai ce maka? Gama ka san bawanka, ya Ubangiji Mai Iko Duka.

21Gama saboda maganarka da kuma bisa ga nufinka, ka aikata wannan babban abu, ka kuma sanar da bawanka.

22“Kai mai girma ne, ya Ubangiji Mai Iko Duka! Babu wani kamar ka, babu kuma wani Allah sai kai; kamar yadda muka ji da kunnuwanmu.

23Wane ne kuma yake kamar da mutanenka Isra’ila, al’umma guda a duniya wadda Allah ya fita don yă kuɓutar wa kansa, ya kuma yi suna wa kansa, ya kuma aikata manyan abubuwa da kuma al’amuran banmamaki ta wurin korin al’ummai da allolinsu daga gaban mutanenka, waɗanda ka kuɓutar daga Masar?

24Ka kafa mutanenka Isra’ila kamar naka na kanka har abada, kai kuma, ya Ubangiji, ka zama Allahnsu.

25“Yanzu kuwa, ya Ubangiji Allah, ka cika alkawarin da ka yi game da bawanka da gidansa. Ka yi kamar yadda ka alkawarta,

26domin sunanka yă kasance da girma har abada. Sa’an nan mutane za su ce, ‘ Ubangiji Maɗaukaki, Allah ne a bisa Isra’ila!’ Kuma gidan bawanka Dawuda zai kahu a gabanka.

27“Ya Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, ka bayyana wa bawanka cewa, ‘Zan gina maka gida.’ Saboda haka bawanka ya sami ƙarfin hali yă miƙa maka wannan addu’a.

28Ya Ubangiji Mai Iko Duka, kai Allah ne! Maganarka da aminci take, ka kuma yi wa bawanka waɗannan abubuwa masu kyau.

29In ya gamshe ka, bari ka albarkaci gidan bawanka don yă dawwama a gabanka har abada; gama kai, ya Ubangiji Mai Iko Duka, ka riga ka yi magana, kuma saboda kai ka sa albarka ga gidan bawanka, lalle zai kasance da albarka har abada.”

1 Tarihi

1Tar 17:16–27

16Sai Sarki Dawuda ya shiga ya zauna a gaban Ubangiji ya ce, “Wane ne ni, ya Ubangiji Allah, kuma wane ne iyalina, da ka kawo ni har zuwa nan?

17Kuma sai ka ce wannan bai isa ba a idonka, ya Allah, ka yi magana game da nan gaba na gidan bawanka. Ka dube ni sai ka ce ni ne mafi ɗaukaka cikin mutane, ya Ubangiji Allah.

18“Me kuma Dawuda zai ce maka saboda girmamawar da ka yi wa bawanka? Gama ka san bawanka,

19Ya Ubangiji. Gama saboda bawanka da kuma bisa ga nufinka, ka yi wannan babban abu, ka kuma sanar da dukan manyan alkawura.

20“Babu wani kamar ka, ya Ubangiji, babu kuma Allah sai kai, kamar yadda muka ji da kunnuwanmu.

21Wane ne kuma yake kamar mutanenka Isra’ila, al’umma guda a duniya wadda Allahnta ya fita don yă fanshi mutane wa kansa, ya kuma yi suna wa kansa, ya kuma aikata manyan abubuwa masu banmamaki masu banrazana ta wurin korin al’ummai daga gaban mutanenka, waɗanda ka fansa daga Masar?

22Ka mai da mutanenka Isra’ila na kanka har abada, kuma kai, ya Ubangiji, ka zama Allahnsu.

23“Yanzu kuwa, Ubangiji, bari alkawarin da ka yi game da bawanka da gidansa yă kahu har abada. Yi kamar yadda ka yi alkawari,

24saboda zai kahu kuma sunanka zai zama mai girma har abada. Sa’an nan mutane za su ce, ‘ Ubangiji Maɗaukaki, Allah a bisa Isra’ila, Allahn Isra’ila ne!’ Kuma gidan bawanka Dawuda zai kahu a gabanka.

25“Kai, Allahna, ka bayyana ga bawanka cewa za ka gina gida dominsa. Ta haka bawanka ya sami ƙarfin gwiwa ya yi addu’a gare ka.

26Ya Ubangiji, kai ne Allah! Ka yi alkawari abubuwa masu kyau wa bawanka.

27Yanzu ka ji daɗi don ka albarkace gidan bawanka, don yă ci gaba har abada a gabanka; gama kai, ya Ubangiji, ka albarkace shi, ya kuma sami albarka ke nan har abada.”

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY