Bible Explorer

Bincika › Sarakuna da Tarihi gefe da gefe › Shawulu da Dawuda

Sarakuna da Tarihi gefe da gefe · Shawulu da Dawuda

Alkawarin Ubangiji ga Dawuda

2Sam 7:1–17 · 1Tar 17:1–15

2 Sama’ila

2Sam 7:1–17

1Bayan sarki ya kama zama a fadansa Ubangiji kuma ya hutashe shi daga dukan abokan gābansa da suke kewaye da shi,

2sai ya ce wa annabi Natan, “Ga ni, ina zama a fadar katakon al’ul, amma akwatin alkawarin Allah yana zaune a tenti.”

3Natan ya amsa wa sarki ya ce, “Duk abin da yake a zuciyarka, sai ka yi, gama Ubangiji yana tare da kai.”

4A daren nan maganar Ubangiji ta zo wa Natan cewa,

5“Je ka faɗa wa bawana Dawuda, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce, kai ne za ka gina mini gida in zauna?

6Ban taɓa zama a gida ba tun daga ranar da na fito da Isra’ilawa daga Masar har yă zuwa yau. Ina dai kai da kawowa a tenti, a matsayin mazaunina.

7A cikin kaiwa da kawowar da nake yi cikin dukan Isra’ilawa, na taɓa ce wa wani shugabanninsu wanda na umarta su lura da mutanena Isra’ila, “Don me ba ku gina mini mazauni da katakon al’ul ba?” ’

8“Yanzu, ka gaya wa bawana Dawuda ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, na ɗauko ka daga makiyaya, daga kuma garken tumaki ka zama sarki bisan mutane Isra’ila.

9Na kasance tare da kai duk inda ka tafi, na kuma kawar da dukan abokan gābanka a gabanka. Yanzu zan sa sunanka yă shahara kamar sunayen shahararrun mutanen duniya.

10Zan kuma tanada wa mutanena Isra’ila wuri, in kuma dasa su yadda za su kasance da gida kansu ba tare da an ƙara damunsu ba. Mugayen mutane ba za su ƙara wahalshe su kamar dā ba,

11yadda suka yi tun lokacin da na naɗa shugabanni bisan mutanena Isra’ila, zan kuma hutashe ka daga hannun abokan gābanka. “ ‘ Ubangiji ya furta maka cewa Ubangiji kansa zai kafa maka gida.

12Sa’ad da kwanakinka suka ƙare, za ka huta tare da kakanninka, zan tā da zuriyarka, na cikinka, zan kuma sa mulkinsa ya kahu.

13Shi zai gina gida domin Sunana, zan kuwa kafa gadon sarautarsa har abada.

14Zan zama Ubansa, shi kuma yă zama ɗana. Idan ya yi laifi, zan yi amfani da mutane in hukunta shi. Mutane ne za su zama bulalata.

15Amma ba za a taɓa ɗauke ƙaunata daga gare shi yadda na ɗauke ta daga wurin Shawulu ba, shi wannan wanda na kawar daga gabanka.

16Gidanka da kuma masarautarka za su dawwama har abada a gabana; gadon sarautarka kuma zai kahu har abada.’ ”

17Natan ya gaya wa Dawuda dukan abin da Allah ya bayyana masa.

1 Tarihi

1Tar 17:1–15

1Bayan Dawuda ya zauna a fadansa, sai ya ce wa annabi Natan, “Ga ni, ina zama a fadar da aka yi da al’ul, yayinda akwatin alkawarin Ubangiji yana a ƙarƙashin tenti.”

2Natan ya amsa wa Dawuda ya ce, “Duk abin da kake tunani a zuciya, ka yi, gama Allah yana tare da kai.”

3A daren nan maganar Allah ta zo wa Natan cewa,

4“Ka tafi ka faɗa wa bawana Dawuda, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce ba kai ba ne za ka gida mini gidan da zan zauna a ciki.

5Ban taɓa zama a gida daga ranar da na fito da Isra’ila daga Masar ba har wa yau. Na yi ta yawo daga gefen da aka kafa tenti zuwa wani, daga wannan wuri zuwa wancan.

6Duk inda na tafi tare da Isra’ilawa, na taɓa ce wa wani daga cikin shugabanninsu waɗanda na umarta su yi kiwon mutanena, “Don me ba ku gida mini gidan al’ul ba?” ’

7“Yanzu, ka faɗa wa bawana Dawuda, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, na ɗauke ka daga makiyaya da kuma daga bin garke, don ka zama mai mulki a bisa mutanena Isra’ila.

8Na kasance tare da kai ko’ina ka tafi, na kuma yanke dukan abokan gābanka a gabanka. Yanzu zan sa sunanka kamar sunayen mutane mafi girma na duniya.

9Zan kuma tanada wuri domin mutanena Isra’ila, zan kuma kafa su saboda za su kasance da gidan kansu ba kuwa za a ƙara damunsu ba. Mugayen mutane ba za su ƙara zaluntar su ba, yadda suka yi da farko

10da kuma suka yi tun lokacin da na sa shugabanni a bisa mutanen Isra’ila. Zan rinjaye dukan abokan gābanka. “ ‘Na furta maka cewa Ubangiji zai gina maka gida,

11sa’ad da kwanakinka suka ƙare ka kuma tafi don ka kasance da kakanninka, zan tā da ɗaya cikin ’ya’yanka maza, daga zuriyarka yă gāje ka, zan kuma kafa mulkinka.

12Shi ne zai gina gida domina, zan kuma kafa sarautarsa har abada.

13Zan zama Ubansa, zai kuma zama ɗana. Ba zan taɓa ɗauke ƙaunata daga gare shi, kamar yadda na ɗauke ta daga wanda ya riga ka ba.

14Zan sa shi a bisa gidana da mulkina har abada; kujerar sarautarsa za tă kahu har abada.’ ”

15Natan ya faɗa wa Dawuda dukan kalmomin wahayin nan.

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY