Bible Explorer

Bincika › Littattafan Bishara gefe da gefe › A Galili

Littattafan Bishara gefe da gefe · A Galili

An ƙi Yesu a Nazaret

Mat 13:53–58 · Mar 6:1–6 · Luk 4:16–30

Mattiyu

Mat 13:53–58

53Sa’ad da Yesu ya gama ba da waɗannan misalai, sai ya ci gaba daga can.

54Yana isowa garinsa, sai ya fara koya wa mutane a cikin majami’arsu, suka kuwa yi mamaki. Suka yi ta tambaya suna cewa, “Ina wannan mutum ya sami irin wannan hikima da kuma ayyukan banmamaki haka?

55Wannan ba shi ne ɗan kafinta nan ba? Ba mahaifiyarsa ba ce Maryamu, ’yan’uwansa kuma Yaƙub, Yusuf, Siman da Yahuda ba?

56Duk ’yan’uwansa mata kuma ba tare da mu suke ba? To, a ina wannan mutum ya sami dukan waɗannan abubuwa?”

57Sai suka ji haushinsa. Amma Yesu ya ce musu, “Sai a garinsa da kuma a gidansa na kaɗai annabi ba ya samun girma.”

58Bai kuwa yi abubuwan banmamaki da yawa a can ba saboda rashin bangaskiyarsu.

Markus

Mar 6:1–6

1Yesu ya tashi daga can ya tafi garinsa, tare da almajiransa.

2Da Asabbaci ya kewayo, sai ya fara koyarwa a cikin majami’a, mutane da yawa da suka saurare shi, suka yi mamaki. Suna tambaya, “Ina mutumin nan ya sami waɗannan abubuwa? Wace hikima ce wannan da aka ba shi, har da yana yin ayyukan banmamaki haka!

3Ashe, wannan ba shi ne kafinta nan ba? Shin, ba shi ne ɗan Maryamu ba, ba shi ne ɗan’uwan su Yaƙub, Yusuf, Yahuda da kuma Siman ba? Ashe, ’yan’uwansa mata kuma ba suna nan tare da mu ba?” Sai suka ji haushinsa.

4Yesu ya ce musu, “Sai a garinsa kaɗai, da kuma cikin ’yan’uwansa, da cikin gidansa ne, annabi ba shi da daraja.”

5Bai iya yin ayyukan banmamaki a wurin ba, sai dai ɗibiya hannuwansa da ya yi a kan mutane kima da suke da cututtuka, ya kuwa warkar da su.

6Ya kuwa yi mamaki ƙwarai don rashin bangaskiyarsu. Sai ya Yesu zazzaga ƙauyuka yana koyarwa.

Luka

Luk 4:16–30

16Ya tafi Nazaret, inda aka yi renonsa. A ranar Asabbaci kuma, ya shiga majami’a kamar yadda ya saba. Sai ya miƙe don yă yi karatu.

17Aka kuwa ba shi naɗaɗɗen littafin annabi Ishaya. Da ya buɗe, sai ya sami wurin da aka rubuta,

18“Ruhun Ubangiji yana kaina, domin ya shafe ni, in yi wa matalauta wa’azin bishara. Ya aiko ni in yi shelar ’yanci ga ’yan kurkuku, in kuma buɗe idanun makafi, in ba da ’yanci ga waɗanda aka danne.

19In yi shelar shekarar tagomashin Ubangiji.”

20Sai ya naɗe naɗaɗɗen littafin ya mayar wa mai hidimar, ya kuma zauna. Dukan idanun waɗanda suke a majami’ar, suka koma a kansa.

21Sai ya fara ce musu, “A yau, Nassin nan, ya cika a kunnenku.”

22Duk suka yabe shi, suka yi mamakin kalmomin alheri da suke fitowa daga bakinsa. Suka yi tambaya, suna cewa, “Anya, wannan ba ɗan Yusuf ba ne?”

23Yesu ya ce musu, “Tabbatacce, na san za ku faɗa mini karin maganan nan, ‘Likita, warkar da kanka! Ka kuma yi abin da muka ji ka yi a Kafarnahum, a nan garinka.’ ”

24Ya ci gaba, da ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, babu annabin da ake yarda da shi a garinsa.

25Ina tabbatar muku a zamanin Iliya, akwai gwauraye da yawa a Isra’ila, sa’ad da aka rufe sararin sama har shekara uku da rabi, aka kuma yi yunwa mai tsanani ko’ina a ƙasar.

26Duk da haka, ba a aiki Iliya ga ko ɗaya a cikinsu ba. Sai dai zuwa ga wata gwauruwa da take a Zarefat, a yankin Sidon.

27Akwai kuma mutane da yawa a Isra’ila masu kuturta a zamanin annabi Elisha, amma ba ko ɗayansu da aka tsarkake sai Na’aman mutumin Suriyan nan kaɗai.”

28Dukan mutanen da suke cikin majami’a suka fusata ƙwarai da jin wannan.

29Suka tashi, suka fitar da Yesu bayan gari, suka kai shi goshin tudun da aka gina garin, don su ture shi ƙasa,

30amma sai ya bi ta tsakiyar taron ya yi tafiyarsa.

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY