Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Shahararrun ayoyin Littafi Mai Tsarki › Ibraniyawa 13:5

Ayar Littafi Mai Tsarki · SRK

Ibraniyawa 13:5

Ku kiyaye kanku daga yawan son kuɗi, ku kuma gamsu da abin da kuke da shi, gama Allah ya ce, “Ba zan taɓa bar ka ba; ba zan taɓa yashe ka ba.”

Karanta dukan babin: Ibraniyawa 13

A cikin mahallinsa

2Kada ku manta da yin alheri ga baƙi, gama ta yin haka ne waɗansu suka yi wa mala’iku hidima, ba da saninsu ba.

3Ku riƙa tunawa da waɗanda suke a kurkuku kamar tare kuke a kurkuku, da kuma waɗanda ake gwada musu azaba, kamar ku ake yi wa.

4Aure yă zama abin girmamawa ga kowa, a kuma kiyaye gadon aure da tsabta, gama Allah zai hukunta masu zina da kuma dukan masu fasikanci.

5Ku kiyaye kanku daga yawan son kuɗi, ku kuma gamsu da abin da kuke da shi, gama Allah ya ce, “Ba zan taɓa bar ka ba; ba zan taɓa yashe ka ba.”

6Saboda haka muna iya fitowa gabagadi, mu ce, “Ubangiji ne mai taimakona; ba zan ji tsoro ba. Me mutum zai iya yi mini?”

7Ku tuna da shugabanninku, waɗanda suka faɗa muku maganar Allah. Ku dubi irin rayuwar da suka yi ku kuma yi koyi da bangaskiyarsu.

8Yesu Kiristi ba ya sākewa, shi ne a jiya, shi ne a yau, shi ne kuma har abada.

Ibraniyawa 13

Da Turanci

Berean Standard BibleHebrews 13:5Keep your lives free from the love of money and be content with what you have, for God has said: “Never will I leave you, never will I forsake you.”

Ambato daga Tsohon Alkawari

M Sh 31:6Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Kada ku ji tsoro, ko ku firgita saboda su, gama Ubangiji Allahnku yana tafe tare da ku, ba zai taɓa barinku ko yă yashe ku ba.”
Yosh 1:5Ba wanda zai yi tsayayya da kai dukan kwanakin ranka. Yadda na kasance tare da Musa, haka zan kasance tare da kai; ba zan taɓa rabuwa da kai ba; ba zan yashe ka ba.

Nassoshi masu alaƙa

Sassan da masu karatu suka fi danganta wa da wannan.

M Sh 31:8Ubangiji kansa yana tafe a gabanka, zai kuma kasance tare da kai, ba zai taɓa barinka ko yă yashe ka ba. Kada ka ji tsoro; kada kuma ka karai.”
1Sam 12:22Saboda suna mai girma da Ubangiji yake da shi, ba zai taɓa ƙin mutanensa ba. Gama Ubangiji ya ji daɗi da ya yi ku mutanensa.
Ish 41:17“Matalauta da mabukata suna neman ruwa, amma babu kome; harsunansu sun bushe saboda ƙishi. Amma Ni Ubangiji zan amsa musu; Ni, Allah na Isra’ila, ba zan yashe su ba.
Zab 37:25Dā ni yaro ne amma yanzu na tsufa, duk da haka ban taɓa ganin an yashe masu adalci ba ko a ce ’ya’yansu suna roƙon burodi.
Ish 41:10Saboda haka kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai; kada ka karai, gama ni ne Allahnka. Zan ƙarfafa ka in kuma taimake ka; zan riƙe ka da hannun damana mai adalci.
1Tar 28:20Dawuda ya kuma ce wa Solomon ɗansa, “Ka yi ƙarfin hali, ka kuma yi aikin. Kada ka ji tsoro ko ka fid da zuciya, gama Ubangiji Allah, Allahna, yana tare da kai. Ba zai bari ka ji kunya ko yă yashe ka ba, sai an gama dukan aikin saboda hidimar haikalin Ubangiji.

Tushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi