Gida › Shahararrun ayoyin Littafi Mai Tsarki › Kolossiyawa 3:21
Ayar Littafi Mai Tsarki · SRK
Kolossiyawa 3:21
Ubanni, kada ku matsa wa yaranku lamba, don kada su fid da zuciya.
Karanta dukan babin: Kolossiyawa 3
A cikin mahallinsa
18Mata, ku yi biyayya ga mazanku, yadda ya dace cikin Ubangiji.
19Maza, ku ƙaunaci matanku kada ku nuna musu hali marar tausayi.
20’Ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku cikin kome, gama wannan yakan gamshi Ubangiji.
21Ubanni, kada ku matsa wa yaranku lamba, don kada su fid da zuciya.
22Bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya cikin kome; kada ku yi aikin ganin ido kamar masu neman yabon mutane, sai dai ku yi aiki tsakaninku da Allah, kamar masu tsoron Ubangiji.
23Kome kuke yi, ku yi shi da dukan zuciyarku, sai ka ce ga Ubangiji kuke yi, ba ga mutum ba.
24Kun san cewa zai ba ku gādo a matsayin ladanku. Ubangiji Kiristi ne fa kuke bauta wa.
Da Turanci
Fathers, do not provoke your children, so they will not become discouraged.Nassoshi masu alaƙa
Sassan da masu karatu suka fi danganta wa da wannan.
Ku saurara ’ya’yana ga koyarwar mahaifinku; ku mai da hankali, ku sami fahimi. Ina ba ku sahihiyar koyarwa, saboda haka kada ku ƙyale koyarwata. Sa’ad da nake yaro a gidan mahaifina, yaro kaɗai kuma na mahaifiyata, ya koya mini ya ce, “Ka riƙe kalmomina da dukan zuciyarka; ka kiyaye umarnaina za ka kuwa rayu.Ku kuma iyaye, kada ku tsokane ’ya’yanku. Ku yi musu reno mai kyau. Ku koyar da su, ku kuma gargaɗe su game da Ubangiji.Tushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi