Gida › Shahararrun ayoyin Littafi Mai Tsarki › Kolossiyawa 2:8
Ayar Littafi Mai Tsarki · SRK
Kolossiyawa 2:8
Ku lura kada wani yă ruɗe ku da ilimin banza da wofi. Wannan koyarwa ta mutane ce kawai. Ta fito daga ikokin wannan duniya ne ba daga Kiristi ba.
Karanta dukan babin: Kolossiyawa 2
A cikin mahallinsa
5Gama ko da yake ba na nan tare da ku a cikin jiki, ina tunaninku kullum, ina kuma farin ciki da gani kuna rayuwa yadda ya kamata, kuna kuma dāgewarku a kan bangaskiyarku a cikin Kiristi.
6To, da yake kun karɓi Kiristi Yesu a matsayin Ubangiji, sai ku ci gaba da rayuwa a cikinsa,
7ku tsaya daram ku kuma ginu a cikinsa, ku sami ƙarfafawa a cikin bangaskiya kamar yadda aka koya muku, kuna kuma cike da godiya.
8Ku lura kada wani yă ruɗe ku da ilimin banza da wofi. Wannan koyarwa ta mutane ce kawai. Ta fito daga ikokin wannan duniya ne ba daga Kiristi ba.
9Gama a cikin Kiristi cikin jiki dukkan cikar Allahntaka take tabbata,
10an kuma mai da ku cikakku a cikin Kiristi, wanda yake shi ne kai a kan kowane iko da kuma hukuma.
11A cikinsa ne kuma aka yi muku kaciya, ba kuwa yin mutum ba, amma wadda Kiristi ya yi muku, ta wurin tuɓe halinku na mutuntaka.
Da Turanci
See to it that no one takes you captive through philosophy and empty deception, which are based on human tradition and the spiritual forces of the world rather than on Christ.Nassoshi masu alaƙa
Sassan da masu karatu suka fi danganta wa da wannan.
Timoti, ka lura da abin da aka danƙa maka amana. Ka yi nesa da masu maganganun rashin tsoron Allah da kuma yawan mūsu da ake ƙarya, ake ce da shi ilimi,Kada wani yă ruɗe ku da kalmomin wofi, gama saboda waɗannan abubuwa ne fushin Allah yake zuwa a kan marasa biyayya.“Ku yi hankali da annabawan ƙarya. Sukan zo muku da kamannin tumaki, amma daga ciki mugayen kyarketai ne.Amma yanzu da kuka san Allah, ko kuma a ce Allah ya san ku, yaya kuke sāke komawa ga ƙa’idodin duniya marasa ƙarfi, abin tausayi kuma? Kuna so ku sāke komawa ga bautarsu ne?Kada ku ruɗi kanku. In waninku yana tsammani cewa yana da hikima, yadda duniya ta ɗauki hikima, to, sai ya mai da kansa “wawa” don yă zama mai hikima. Gama hikimar duniyan nan, wauta ce a gaban Allah, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yakan kama masu hikima a cikin makircinsu”;Gama ko da yake sun san Allah, ba su ɗaukaka shi a matsayin Allah ko su gode masa ba, sai dai tunaninsu ya zama banza, zukatansu masu wauta kuma suka duhunta. Ko da yake sun ɗauka su masu hikima ne, sai suka zama wawaye,Kun mutu tare da Kiristi. Yanzu ƙa’idodin wannan duniya ba su da iko a kanku. Don me kuke zama har yanzu kamar ku nasu ne? Kuna biyayya da umarnansu cewa,Mugayen mutane da masu ruɗi kuwa, ƙara muni za su riƙa yi, suna yaudara, ana kuma yaudararsu.Tushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi