Bincika › Hanyoyi › Tafiyar akwatin alkawari
Hanyoyi
Tafiyar akwatin alkawari
Filistiyawa sun ƙwace shi, an mayar da shi, an kawo shi Urushalima · tasha 7 · ≈ 110 km a layi madaidaici
Tashoshi
- Ebenezer1Sam 5:1
Bayan Filistiyawa sun ƙwace akwatin alkawarin Allah, sai suka ɗauke shi daga Ebenezer suka kai shi Ashdod.
- Gat1Sam 5:8
Saboda haka suka kira duka shugabannin Filistiyawa suka tambaye su, suka ce, “Me za mu da akwatin alkawarin Allahn Isra’ila?” Sai suka amsa suka ce, “A ɗauki akwatin alkawarin Allah na Isra’ila a kai shi Gat.” Sai suka ɗauki akwatin alkawarin Allah na Isra’ila.
- Ekron1Sam 5:10
Sai suka aika da akwatin alkawarin Allah zuwa Ekron. Yayinda akwatin alkawarin Allah yana shiga cikin Ekron, mutanen Ekron suka yi ihu, suka ce, “An kawo mana akwatin alkawarin Allah na Isra’ila domin yă kashe mu da mutanenmu.”
- Bet-Shemesh1Sam 6:12
Sai shanun suka miƙe zuwa Bet-Shemesh. Suka bi hanya daidai, ba su juya dama ko hagu ba. Shugabannin Filistiyawa suka bi har zuwa iyakar ƙasar Bet-Shemesh.
- Kiriyat Yeyarim1Sam 7:1
Mutanen Kiriyat Yeyarim suka ɗauki akwatin alkawarin Ubangiji. Suka kai a gidan Abinadab da ke kan tudu, suka keɓe Eleyazar ɗansa yă lura da akwatin alkawarin Ubangiji.
- Urushalima1Tar 15:3
Dawuda ya tattara dukan Isra’ila a Urushalima don su haura da akwatin alkawarin Ubangiji zuwa wurin da aka shirya dominsa.
Layukan suna haɗa tashoshin bisa ga jerin rubutun — ba a san hanyoyin kansu ba. Layin ɗigo-ɗigo: ta jirgin ruwa. Mara haske: ba a tabbatar da wurin ba.
Kowane digo shi ne wurin da ya fi yiwuwa (OpenBible.info); digo mara haske yana nufin ba a tabbatar da wurin ba. Wuraren da ba a san inda suke ba ba sa kan taswira.
Wurare: OpenBible.info Bible Geocoding Data (CC BY 4.0).
Iyakokin ƙasa: Natural Earth (mallakar jama’a).