Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Nuwamba 2027 › Nuwamba 15
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Nuwamba 15, 2027
Litinin · Mako na 33 na lokacin yau da kullum
Bukukuwa da waliyyai
Litinin a mako na 33 na lokacin yau da kullum
Tunawa da ba dole ba · Launin ibada: kore
Waliyyi Albert Babba, bishop kuma malamin Ikkilisiya · Tunawa da ba dole ba
Karatun yini
Karatu na farko
Ba ya cikin wannan fassara
Zaburar amsawa
Zab 119:53, 61, 134, 150, 155, 158
53Fushi ya kama ni saboda mugaye, waɗanda suka keta dokokinka. 61Ko da yake mugaye sun ɗaura ni da igiyoyi, ba zan manta da dokokinka ba. 134Ka fanshe ni daga mutane masu danniya, don in yi biyayya da farillanka. 150Waɗanda suke ƙirƙiro mugayen dabaru suna nan kusa, amma suna nesa da dokarka. 155Ceto yana nesa da mugaye, gama ba sa neman ƙa’idodinka. 158Na dubi marasa aminci da ƙyama, gama ba sa yin biyayya da maganarka.
Bishara
35Da Yesu ya yi kusa da Yeriko, akwai wani makaho da yake zaune a gefen hanya, yana bara. 36Da ya ji taron suna wucewa, sai ya yi tambaya ko mene ne ke faruwa. 37Suka ce masa, “Ai, Yesu Banazare ne ke wucewa.” 38Sai ya yi kira ya ce, “Yesu, Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!” 39Mutane da suke gaba suka kwaɓe shi, suka ce masa ya yi shiru. Amma sai ya ƙara ɗaga murya, yana cewa, “Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!” 40Sai Yesu ya tsaya, ya ba da umarni a kawo mutumin wurinsa. Da ya zo kusa, Yesu ya tambaye shi ya ce, 41“Me kake so in yi maka?” Sai ya amsa ya ce, “Ubangiji, ina so in sami ganin gari.” 42Yesu ya ce masa, “Ka sami ganin garinka; bangaskiyarka ta warkar da kai.” 43Nan da nan, ya sami ganin garinsa, kuma ya bi Yesu, yana yabon Allah. Da dukan mutane suka ga wannan, sai su ma suka yabi Allah.
Tsarkakan ranar
- Waliyyi Albert Babba, bishop kuma malamin Ikkilisiya
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi