Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Nuwamba 2027 › Nuwamba 16
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Nuwamba 16, 2027
Talata · Mako na 33 na lokacin yau da kullum
Bukukuwa da waliyyai
Talata a mako na 33 na lokacin yau da kullum
Tunawa da ba dole ba · Launin ibada: kore
Waliyya Gertrude Babba, budurwa · Tunawa da ba dole ba
Waliyya Margaret ta Scotland · Tunawa da ba dole ba
Karatun yini
Karatu na farko
Ba ya cikin wannan fassara
Zaburar amsawa
1Zabura ta Dawuda. Sa’ad da ya gudu daga ɗansa Absalom. Ya Ubangiji, abokan gābana nawa ne! Su nawa suke gāba da ni! 2Da yawa suna magana a kaina suna cewa, “Allah ba zai cece shi ba.” Sela 3Amma kai ne garkuwa kewaye da ni, ya Ubangiji; ka ba ni ɗaukaka ka kuma ɗaga kaina. 4Ga Ubangiji na yi kuka mai ƙarfi, ya kuwa amsa mini daga tudunsa mai tsarki. Sela 5Na kwanta na yi barci; na kuma farka, gama Ubangiji yana kiyaye ni. 6Ba zan ji tsoro ko dubu goma suka ja dāgā gāba da ni a kowane gefe ba. 7Ka tashi Ya Ubangiji! Ka cece ni, ya Allahna! Ka bugi dukan abokan gābana a muƙamuƙi; ka kakkarya haƙoran mugaye.
Bishara
1Yesu ya shiga Yeriko, yana ratsa ta cikinta. 2Akwai wani mutum a garin, mai suna Zakka. Shi shugaban masu karɓar haraji ne, mai arziki kuma. 3Ya so yă ga ko wane ne Yesu, amma saboda taron, bai iya ba, domin shi gajere ne. 4Saboda haka, ya yi gaba da gudu, kuma ya hau itacen sikamo, don yă gan shi, tun da Yesu zai bi wannan hanyar ne. 5Da Yesu ya iso wurin, sai ya ɗaga ido sama, ya ce masa, “Zakka, ka yi maza ka sauka. Ni kam, dole in sauka a gidanka yau.” 6Sai ya sauka nan da nan, ya karɓe shi da murna. 7Dukan mutane suka ga haka, kuma suka fara gunaguni, suka ce, “Ya je don yă zama baƙon ‘mai zunubi.’ ” 8Amma Zakka ya tashi a tsaye, ya ce wa Ubangiji, “Duba, Ubangiji! Nan take, rabin dukiyar da nake da shi, na ba wa matalauta. In kuma na taɓa cutan wani, a kan wani abu, zan mayar da shi ninki huɗu.” 9Sai Yesu ya ce masa, “Yau, ceto ya zo gidan nan, domin wannan mutum shi ma ɗan Ibrahim ne. 10Saboda Ɗan Mutum ya zo ne, domin yă nemi abin da ya ɓata, yă cece shi kuma.”
Tsarkakan ranar
- Waliyya Gertrude Babba, budurwa
- Waliyya Margaret ta Scotland
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi