Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Nuwamba 2027 › Nuwamba 10
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Nuwamba 10, 2027
Laraba · Mako na 32 na lokacin yau da kullum
Bukukuwa da waliyyai
Laraba a mako na 32 na lokacin yau da kullum
Tunawa · Launin ibada: fari
Waliyyi Leo Babba, Fafaroma kuma malamin Ikkilisiya · Tunawa
Karatun yini
Karatu na farko
Ba ya cikin wannan fassara
Zaburar amsawa
3Ku tsare mutuncin marasa ƙarfi da marayu; ku kāre hakkin matalauta da waɗanda ake danniya. 4Ku ceci marasa ƙarfi da masu bukata; ku kuɓutar da su daga hannun mugaye. 6“Na ce, ‘Ku “alloli” ne; dukanku ’ya’yan Mafi Ɗaukaka’ ne. 7Amma za ku mutu kamar mutum kurum; za ku fāɗi kamar duk wani mai mulki.”
Bishara
11Yesu yana kan hanyarsa zuwa Urushalima, sai ya bi takan iyakar Samariya da Galili. 12Da zai shiga wani ƙauye, sai maza goma da suke da kuturta suka sadu da shi. Suka tsaya da nesa, 13suka yi kira da babbar murya, suka ce, “Yesu, Ubangiji, ka ji tausayinmu!” 14Da ya gan su sai ya ce, “Ku je ku nuna kanku ga firistoci.” Suna kan hanyar tafiya sai suka tsabtacce. 15Da ɗayansu ya ga ya warke, sai ya koma, yana yabon Allah da babbar murya. 16Ya zo ya fāɗi a gaban Yesu, ya gode masa. Shi kuwa mutumin Samariya ne. 17Yesu ya yi tambaya ya ce, “Ba duka goma ne aka tsabtacce ba? Ina sauran taran? 18Ba wanda ya dawo don yă yabi Allah, sai dai wannan baƙon?” 19Sai ya ce masa, “Tashi, ka yi tafiyarka, bangaskiyarka ta warkar da kai.”
Tsarkakan ranar
- Waliyyi Leo Babba, Fafaroma kuma malamin Ikkilisiya
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi