Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Nuwamba 2027 › Nuwamba 11

Kalandar Katolika

Karatun Mass (Katolika) — Nuwamba 11, 2027

Alhamis · Mako na 32 na lokacin yau da kullum

Bukukuwa da waliyyai

Alhamis a mako na 32 na lokacin yau da kullum

Tunawa · Launin ibada: fari

Waliyyi Martin na Tours, bishop · Tunawa

Karatun yini

Karatu na farko

Ba ya cikin wannan fassara

Zaburar amsawa

Zab 119:89–91, 130, 135, 175

89Maganarka, ya Ubangiji madawwamiya ce; tana nan daram a cikin sammai. 90Amincinka yana cin gaba cikin dukan zamanai; ka kafa duniya ta kuma dawwama. 91Dokokinka sun dawwama har yă zuwa yau, gama dukan abubuwa suna maka hidima. 130Fassarar maganganunka sukan ba da haske; sukan ba da ganewa ga marar ilimi. 135Ka sa fuskarka ta haskaka a kan bawanka ka kuma koya mini ƙa’idodinka. 175Bari in rayu don in yabe ka, bari kuma dokokinka su raya ni.

Bishara

Luk 17:20–25

20Wata rana, Farisiyawa suka tambaye shi lokacin da mulkin Allah zai zo, Yesu ya amsa ya ce, “Ai, mulkin Allah ba takan zo ta wurin yin kallon ku ba. 21Mutane kuma ba za su ce, ‘Ga shi nan,’ ko kuma, ‘Ga shi can’ ba, domin mulkin Allah yana cikinku ne.” 22Sai ya ce wa almajiransa, “Lokaci yana zuwa da za ku yi marmarin ganin rana ɗaya cikin ranakun Ɗan Mutum, amma ba za ku gani ba. 23Mutane za su ce muku, ‘Ga shi can!’ Ko kuma, ‘Ga shi nan!’ Kada ku yi hanzarin binsu. 24Gama Ɗan Mutum, a cikin ranarsa, zai zama kamar walƙiya da take walƙawa, da take kuma haskaka sararin sama, daga wannan kusurwa zuwa wancan kusurwa. 25Amma da fari, dole yă sha wahaloli masu yawa, kuma mutanen zamanin nan su ƙi shi.

Tsarkakan ranar

Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi