Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Satumba 2027 › Satumba 20
Kalandar Ortodoks · 7 ga Satumba (tsohon lissafi)
Karatun Orthodox na ranar — Satumba 20, 2027
Litinin · Mako na 14 bayan Fentekos · Sauti na 4
Bukukuwa da waliyyai
Forefeast of the Nativity of the Theotokos
Azumi
Babu azumi
Wannan yana bin dokar gidan zuhudu. A cikin ikkilisiya, ana tsara gwargwadon azumi tare da mai sauraron furcin zunubi, bisa ga lafiya, shekaru da yanayi.
Karatun yini
Wasiƙa
10Shi ya sa nake murna cikin rashin ƙarfi, da zagi, da shan wahaloli, da tsanantawa, da matsaloli, saboda Kiristi. Don a sa’ad da nake marar ƙarfi a nan ne nake da ƙarfi. 11Na yi wauta kam, amma ku ne kuke tilasta mini, ku ne kuwa ya kamata ku yaba mini, domin ba inda na kāsa waɗannan mafiffitan manzanni, ko da yake ni ba kome ba ne. 12Abubuwan da suke tabbatar da manzo, alamu, abubuwa da kuma ayyukan banmamaki, an aikata su a cikinku da matuƙar nacewa. 13Ta yaya ne darajarku ba tă kai ta sauran ikkilisiyoyi ba, ko kuwa don dai ban nawaita muku ba ne? Ku gafarta mini wannan laifi! 14Yanzu a shirye nake in ziyarce ku sau na uku, ba zan kuma nawaita muku ba, don ba kayanku nake so ba, ku nake so. Gama ba yara ne da ɗaukar nauyin iyayensu ba, sai dai iyaye ne da ɗaukar nauyin yaran. 15Don haka ina farin ciki in kashe dukan abin da nake da shi a kanku, har in ba da kaina ma dominku. In na ƙaunace ku fiye da haka, za ku rage ƙaunarku gare ni ne? 16To, shi ke nan, ban nawaita muku ba. Ashe, sai ku ce dabara na yi muku, na shawo kanku ta hanyar yaudara! 17Na cuce ku ne ta wurin wani daga cikin waɗanda na aiko a gare ku? 18Na roƙi Titus ya zo wurinku. Na kuma aiki ɗan’uwanmu tare da shi. Ko Titus ya cuce ku ne? Ba ruhu ɗaya yake bi da mu ba? Ba kuma hanya guda muka bi ba? 19Ko tun dā can, kuna tsammani muna kāre kanmu a gare ku ne? A gaban Allah muke magana, kamar waɗanda suke cikin Kiristi. Ƙaunatattuna, kome da muke yi, muna yi ne don inganta ku ne.
Wasiƙa (domin Talata)
20Gama ina tsoro, in na zo, in tarar da ku dabam da yadda nake so, ku ma ku tarar da ni dabam da yadda kuke so. Ina tsoro kada yă zama akwai faɗa, da kishi, da fushi mai zafi, da tsattsaguwa, da ɓata suna, da gulma, da girman kai, da hargitsi. 21Ina tsoro kada sa’ad da na sāke zuwa, Allahna zai ƙasƙantar da ni a gabanku, kuma in yi baƙin ciki saboda waɗanda suka yi zunubi a dā, ba su kuma tuba daga aikin ƙazanta, da na fasikanci, da kuma lalata da suka sa kansu a ciki ba. 13:1Wannan za tă zama ziyarata ta uku a wurinku ke nan. “Dole a tabbatar da kowace magana ta bakin shaidu biyu ko uku.” 2Na riga na yi muku gargaɗi sa’ad da nake tare da ku a zuwana na biyu. Yanzu da ba na nan tare da ku, ina maimaita irin gargaɗin nan domin in na zo ba wanda zai kuɓuce wa horon nan,
Bishara
10Lokacin da yake shi kaɗai, Sha Biyun, da kuma waɗanda suke kewaye da shi, suka tambaye shi game da misalan. 11Sai ya ce musu, “An ba ku sanin asirin mulkin Allah. Amma ga waɗanda suke waje kuwa, kome sai da misalai. 12Saboda, “ ‘ko sun dinga duba, ba za su taɓa gane ba, kuma ko su dinga ji, ba za su taɓa fahimta ba, in ba haka ba, mai yiwuwa, su tuba, a gafarta musu!’ ” 13Sai Yesu ya ce musu, “Ba ku fahimci wannan misali ba? Yaya za ku fahimci wani misali ke nan? 14Manomi yakan shuka maganar Allah. 15Waɗansu mutane suna kama da irin da ya fāɗi a kan hanya, inda akan shuka maganar Allah. Da jin maganar, nan da nan sai Shaiɗan yă zo yă ɗauke maganar da aka shuka a zuciyarsu. 16Waɗansu suna kama da irin da aka shuka a wurare masu duwatsu, sukan ji maganar Allah, sukan kuma karɓe ta nan da nan da farin ciki. 17Amma da yake ba su da saiwa, ba sa daɗewa. Da wahala ko tsanani ya tashi saboda maganar, nan da nan, sai su ja da baya. 18Har yanzu, waɗansu kamar irin da aka shuka cikin ƙaya, sukan ji maganar, 19amma damuwar wannan duniya, da son dukiya, da kuma kwaɗayin waɗansu abubuwa, sukan shiga, su shaƙe maganar, har su mai da ita marar amfani. 20Waɗansu mutane kuwa suna kama da irin da aka shuka a ƙasa mai kyau, sukan ji maganar Allah, su kuma karɓa, sa’an nan kuma su fid da amfani riɓi talatin-talatin, ko sittin-sittin, ko ɗari-ɗari.” 21Sai ya ce musu, “Ko kukan kawo fitila ku rufe ta da murfi ko kuma ku sa ta a ƙarƙashin gado ne? Ba kukan sa ta a kan wurin ajiye fitila ba? 22Duk abin da yake a ɓoye, dole za a fallasa shi. Duk abin da kuma yake a rufe, dole za a fitar da shi a fili. 23Duk mai kunnen ji, bari yă ji.”
Bishara (domin Talata)
24Ya ci gaba da cewa, “Ku lura da abin da kuke ji da kyau. Mudun da ka auna da shi, da shi za a auna maka, har ma a ƙara. 25Duk wanda yake da shi, za a ƙara masa, duk wanda kuma ba shi da shi, ko abin da yake da shi ma, za a karɓe daga gare shi.” 26Ya sāke cewa, “Mulkin Allah yana kama da haka. Wani mutum ya yafa iri a gona. 27A kwana a tashi har irin yă tsiro, yă yi girma, bai kuwa santa yadda aka yi ba. 28Ƙasar da kanta takan ba da ƙwaya, da farko takan fid da ƙara, sa’an nan ta fid da kai, sa’an nan kan yă fid da ƙwaya. 29Da ƙwayan ya nuna, sai yă sa lauje yă yanka, domin lokacin girbi ya yi.” 30Ya kuma ce, “Da me za mu kwatanta mulkin Allah, ko kuwa da wane misali za mu bayyana shi? 31Yana kama da ƙwayar mustad, wadda ita ce ƙwaya mafi ƙanƙanta da akan shuka a gona. 32Duk da haka, in aka shuka ƙwayar, sai tă yi girma, tă zama mafi girma a itatuwan lambu. Har itacen yă kasance da manyan rassa, inda tsuntsayen sararin sama sukan iya huta a inuwarsa.” 33Da misalai da yawa irin waɗannan, Yesu ya yi magana da su, daidai yadda za su iya fahimta. 34Ba abin da ya faɗa musu, da ba da misali ba. Amma lokacin da yake shi kaɗai tare da almajiransa, sai yă bayyana kome.
Kwanakin suna bin kalandar Julian ta Ikilisiyar Rasha (kamar Ikilisiyoyin Serbia da Georgia da Dutsen Athos): Satumba 7 a kalandar ikilisiya shi ne Satumba 20 a kalandar gari. Ikilisiyoyin da ke amfani da sabuwar kalanda (Girka, Romania, Bulgaria, Ukraine…) suna yin bukukuwan da ba sa canzawa da na tsarkaka a ainihin ranar gari, kwanaki 13 kafin haka, kuma wasu karatunsu sun bambanta; Ista da kwanakin da suka dogara da ita iri ɗaya ne.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi