Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Agusta 2027 › Agusta 12

Kalandar Katolika

Karatun Mass (Katolika) — Agusta 12, 2027

Alhamis · Mako na 19 na lokacin yau da kullum

Bukukuwa da waliyyai

Alhamis a mako na 19 na lokacin yau da kullum

Tunawa da ba dole ba · Launin ibada: kore

Waliyya Jane Frances de Chantal, mai zuhudu · Tunawa da ba dole ba

Karatun yini

Karatu na farko

Yosh 3:7–11, 13–17

7Ubangiji kuwa ya ce wa Yoshuwa, “Yau, zan fara ɗaukaka ka a gaban Isra’ilawa duka don su sani cewa ina tare da kai kamar yadda na kasance tare da Musa. 8Ka ce wa firistoci waɗanda suke ɗauke da akwatin alkawari, ‘Sa’ad da kuka kai bakin Urdun, ku shiga cikin ruwan ku tsaya.’ ” 9Yoshuwa ya ce wa Isra’ilawa, “Ku zo nan ku ji maganar Ubangiji Allahnku. 10Ta haka ne za ku san cewa Allah mai rai yana tare da ku, kuma ba shakka a gabanku za ku gani zai kore Kan’aniyawa, Hittiyawa, Hiwiyawa, Ferizziyawa, Girgashiyawa, Amoriyawa da Yebusiyawa. 11Ku duba, akwatin alkawarin Ubangiji na dukan duniya zai yi gaba cikin Urdun kafin ku. 13Kuma da firistoci waɗanda suke ɗauke da akwatin alkawarin Ubangiji, Ubangiji dukan duniya, sun sa ƙafa cikin ruwan kogin Urdun, ruwan da yake gudu a rafin zai tsaya cik yă taru a wuri ɗaya.” 14Saboda haka sa’ad da mutanen suka tashi don su ƙetare Urdun, firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawarin suka sha gaba. 15Da kaka Urdun yakan cika makil da ruwa. Duk da haka da zarar firistoci masu ɗauke da akwatin alkawari suka tsoma ƙafafunsu a gefen ruwa, 16sai ruwan da yake gangarowa ya tsaya, ya tattaru a wuri ɗaya ya yi tudu daga nan har zuwa wani garin da ake kira Adam kusa da Zaretan, ruwan da yake gangarowa zuwa Tekun Araba (Tekun Gishiri) kuma ya yanke gaba ɗaya. Sai mutane suka ƙetare kusa da Yeriko. 17Firistocin kuwa da suke ɗauke da akwatin alkawarin Ubangiji suka tsaya daram a kan busasshiyar ƙasa a tsakiyar Urdun a lokacin da Isra’ilawa suka ƙetarewa, har sai da dukan mutane suka gama ƙetarewa.

Zaburar amsawa

Zab 114:1–6

1Sa’ad da Isra’ila ya fito daga Masar, gidan Yaƙub daga mutane masu baƙon harshe, 2Yahuda ya zama wuri mai tsarki na Allah, Isra’ila mallakarsa. 3Teku ya kalla ya kuma gudu, Urdun ya juye da baya; 4duwatsu suka yi tsalle kamar raguna, tuddai kamar tumaki. 5Me ya sa, ya teku, kika gudu, Ya Urdun, ka juya baya, 6ku duwatsu, kuka yi tsalle kamar raguna, ku tuddai, kamar tumaki?

Bishara

Mat 18:21–19:1

21Sai Bitrus ya zo wurin Yesu ya yi masa tambaya ya ce, “Ubangiji, sau nawa zan yafe wa ɗan’uwana sa’ad da ya yi mini zunubi? Har sau bakwai?” 22Yesu amsa ya ce, “Ina gaya maka, ba sau bakwai ba, amma sau saba’in da bakwai. 23“Saboda haka, mulkin sama yana kama da wani sarki wanda ya so yă yi ƙididdigar dukiyarsa da take a hannun bayinsa. 24Da ya fara ƙididdigar, sai aka kawo masa wani wanda yake bin bashin talenti dubu goma. 25Da yake bai iya biya ba, sai maigida ya umarta a sayar da shi da matarsa da yaransa da kuma duk abin da yake da shi, a biya bashin. 26“Bawan ya durƙusa a gabansa. Ya yi roƙo ya ce, ‘Ka yi mini haƙuri, zan biya ka ƙaf.’ 27Maigidan bawan ya ji tausayinsa, ya yafe masa bashin, ya kuma sake shi. 28“Amma da wannan bawa ya fita, sai ya gamu da wani abokin bautarsa wanda yake binsa bashin dinari ɗari. Sai ya cafke shi, ya shaƙe shi a wuya yana cewa, ‘Biya ni abin da nake binka!’ 29“Wannan abokin bautarsa ya durƙusa ya roƙe shi, ‘Ka yi mini haƙuri, zan biya ka.’ 30“Amma ya ƙi. A maimako, sai ya je ya sa aka jefa shi a kurkuku, har yă biya bashin. 31Sa’ad da sauran bayin suka ga abin da ya faru, abin ya ɓata musu rai ƙwarai, sai suka tafi suka faɗa wa maigidansu dukan abin da ya faru. 32“Sai maigidan ya kira wannan bawa. Ya ce, ‘Kai mugun bawa, na yafe duk bashin da nake binka domin ka roƙe ni. 33Ashe, bai kamata kai ma ka ji tausayin abokin bautarka yadda na yi maka ba?’ 34Cikin fushi, maigidan ya miƙa shi ga ma’aikatan kurkuku su gwada masa azaba, har yă biya dukan bashin da ake binsa. 35“Haka Ubana da yake cikin sama zai yi da kowannenku, in ba ku yafe wa ’yan’uwanku daga zuciyarku ba.” 19:1Sa’ad da Yesu ya gama faɗin waɗannan abubuwa, sai ya bar Galili, ya tafi yankin Yahudiya a ɗaya gefen Urdun.

Tsarkakan ranar

Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi