Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Agusta 2027 › Agusta 12
Kalandar Ortodoks · 30 ga Yuli (tsohon lissafi)
Karatun Orthodox na ranar — Agusta 12, 2027
Alhamis · Mako na 8 bayan Fentekos · Sauti na 6
Bukukuwa da waliyyai
Holy Apostles of the 70: Silas and Sylvanus, and those with them: Criscentus, Epenetus and Andronicus (1st C)
Azumi
Babu azumi
Wannan yana bin dokar gidan zuhudu. A cikin ikkilisiya, ana tsara gwargwadon azumi tare da mai sauraron furcin zunubi, bisa ga lafiya, shekaru da yanayi.
Karatun yini
Wasiƙa
28Sai dai in wani ya ce muku, “Ai, wannan an miƙa ne wa gunki,” to, kada ku ci, saboda duban mutuncin wannan da ya gaya muku, don kuma lamiri yă kasance babu laifi 29ina nufin lamirin wancan mutum ne fa, ba naku ba. Don me lamirin wani zai shari’anta ’yancina? 30In na ci abinci da godiya, don me za a zarge ni a kan abin da na ci da godiya ga Allah? 31Saboda haka, duk abin da kuke yi, ko ci ko sha, ku yi shi duka saboda ɗaukakar Allah. 32Kada ku sa wani yă yi tuntuɓe, ko mutumin Yahuda ne, ko mutumin Al’ummai ko kuma ikkilisiyar Allah 33kamar dai yadda nake ƙoƙarin faranta wa kowa rai, ta kowace hanya. Gama ba don kaina kaɗai nake yi ba, sai dai don amfanin mutane da yawa, don su sami ceto. 11:1Ku bi gurbina, kamar yadda ni nake bin gurbin Kiristi. 2Ina yabonku saboda kuna tunawa da ni a cikin kowane abu, kuna kuma riƙe da koyarwar, yadda na ba ku. 3To, ina so ku gane cewa shugaban kowane namiji Kiristi ne, shugaban mace namiji ne, shugaban Kiristi kuma Allah ne. 4Kowane namijin da ya yi addu’a ko annabci da kansa a rufe ya jawo kunya wa kansa. 5Duk macen da ta yi addu’a ko annabci da kanta a buɗe kuwa ta rena kanta, ya zama kamar an aske kanta ke nan. 6In mace ba ta so tă rufe kanta, to, sai tă aske gashinta; in kuwa abin kunya ne mace tă yanke ko tă aske gashinta, to, sai tă rufe kanta. 7Namiji kuwa bai kamata ya rufe kansa ba, da yake shi kamannin Allah ne, da kuma darajar Allah, amma mace dai, darajar namiji ne.
Bishara
24Sa’an nan Yesu ya ce wa almajiransa, “Duk mai son bina, dole yă ƙi kansa, yă ɗauki gicciyensa, yă bi ni. 25Gama duk mai son ceton ransa zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni, zai same shi. 26Me mutum zai amfana in ya sami duniya duka, amma ya rasa ransa? Ko kuwa me mutum zai bayar a bakin ransa? 27Gama Ɗan Mutum zai zo cikin ɗaukakar Ubansa, tare da mala’ikunsa, sa’an nan zai ba wa kowane mutum lada gwargwadon abin da ya yi. 28“Gaskiya nake gaya muku, akwai waɗansu da suke tsaitsaye a nan da ba za su mutu ba sai sun ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin mulkinsa.”
Kwanakin suna bin kalandar Julian ta Ikilisiyar Rasha (kamar Ikilisiyoyin Serbia da Georgia da Dutsen Athos): Yuli 30 a kalandar ikilisiya shi ne Agusta 12 a kalandar gari. Ikilisiyoyin da ke amfani da sabuwar kalanda (Girka, Romania, Bulgaria, Ukraine…) suna yin bukukuwan da ba sa canzawa da na tsarkaka a ainihin ranar gari, kwanaki 13 kafin haka, kuma wasu karatunsu sun bambanta; Ista da kwanakin da suka dogara da ita iri ɗaya ne.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi