Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Mayu 2027 › Mayu 19
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Mayu 19, 2027
Laraba · Mako na 7 na lokacin yau da kullum
Bukukuwa da waliyyai
Laraba a mako na 7 na lokacin yau da kullum
Ranar mako · Launin ibada: kore
Karatun yini
Karatu na farko
Ba ya cikin wannan fassara
Zaburar amsawa
Zab 119:165, 168, 171–172, 174–175
165Waɗanda suke ƙaunar dokarka suna da babban salama, kuma babu abin da zai sa su yi tuntuɓe. 168Ina biyayya da farillanka da kuma koyarwarka, gama dukan hanyoyina sanannu ne gare ka. 171Bari leɓunana su cika da yabonka, gama ka koya mini ƙa’idodinka. 172Bari harshena yă rera game da maganarka, gama dukan umarnanka masu adalci ne. 174Ina marmarin cetonka, ya Ubangiji, dokarka kuwa ita ce farin cikina. 175Bari in rayu don in yabe ka, bari kuma dokokinka su raya ni.
Bishara
38Yohanna ya ce, “Malam mun ga wani mutum yana fitar da aljanu a cikin sunanka, sai muka ce yă daina, domin shi ba ɗaya daga cikinmu ba ne.” 39Yesu ya ce, “Kada ku hana shi. Ba wanda yake yin ayyukan banmamaki a cikin sunana, nan take yă faɗi wani abu mummuna game da ni. 40Gama duk wanda ba ya gāba da mu, namu ne.
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi