Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Mayu 2027 › Mayu 20
Kalandar Ortodoks · 7 ga Mayu (tsohon lissafi)
Karatun Orthodox na ranar — Mayu 20, 2027
Alhamis · Mako na 3 na lokacin Ista · Sauti na 2
Bukukuwa da waliyyai
Commemoration of the Apparition of the Sign of the Precious Cross Over Jerusalem in 351 AD
Azumi
Babu azumi
Wannan yana bin dokar gidan zuhudu. A cikin ikkilisiya, ana tsara gwargwadon azumi tare da mai sauraron furcin zunubi, bisa ga lafiya, shekaru da yanayi.
Karatun yini
Wasiƙa
26To wani mala’ikan Ubangiji ya ce wa Filibus, “Ka yi kudu zuwa hanyar, hanyar hamada, da ta gangara daga Urushalima zuwa Gaza.” 27Saboda haka ya kama hanya, a kan hanyarsa kuwa sai ya sadu da wani mutumin Itiyofiya, wanda yake bābā, hafsa mai muhimmanci wanda yake lura da dukan ma’ajin Kandas (wanda yake nufin “sarauniyar mutanen Itiyofiya”). Mutumin nan ya tafi Urushalima ne domin yin sujada, 28a kan hanyarsa ta komawa gida kuwa yana zaune bisan keken yaƙinsa yana karatun littafin annabin Ishaya. 29Sai Ruhu ya ce wa Filibus, “Matsa wurin kekunan yaƙin nan ka yi kusa da ita.” 30Sai Filibus ya ruga zuwa wajen keken yaƙin ya kuma ji mutumin yana karatun littafin annabin Ishaya. Filibus ya yi tambaya ya ce, “Ka fahimci abin da kake karantawa?” 31Sai ya ce, “Ina fa zan iya, in ba dai wani ya fassara mini ba?” Saboda haka sai ya gayyaci Filibus yă hau yă zauna tare da shi. 32Bābān yana karanta wannan Nassin, “An ja shi kamar tunkiya zuwa mayanka, kuma kamar ɗan rago a hannun mai askin gashinsa yake shiru, haka kuwa bai buɗe bakinsa ba. 33A cikin wulaƙacinsa aka hana masa gaskiya. Wa zai iya yin zancen zuriyarsa? Gama an ɗauke ransa daga duniya.” 34Sai bābān ya tambayi Filibus ya ce, “Ka gaya mini, ina roƙonka, annabin yana magana a kan wane ne, kansa ne, ko kuwa wani dabam?” 35Sa’an nan Filibus ya fara da wannan Nassi ɗin ya kuma faɗa masa labari mai daɗi game da Yesu. 36Yayinda suke cikin tafiya a kan hanya, sai suka iso wani wurin ruwa bābān nan ya ce, “Duba, ga ruwa. Me zai hana a yi mini baftisma?” 38Ya kuwa ba da umarni a tsai da keken yaƙin. Sa’an nan da Filibus da bābān suka gangara zuwa cikin ruwan Filibus kuwa ya yi masa baftisma. 39Sa’ad da suka fita daga cikin ruwan, sai Ruhun Ubangiji ya fyauce Filibus, bābān kuwa bai ƙara ganinsa ba, amma ya ci gaba da tafiyarsa yana farin ciki.
Bishara
40Gama nufin Ubana shi ne, duk wanda yake duban Ɗan, ya kuma gaskata shi zai sami rai madawwami, ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe.” 41Da jin haka, Yahudawa suka fara gunaguni a kansa, domin ya ce, “Ni ne burodin da ya sauka daga sama.” 42Suka ce, “Kai, wannan ba Yesu ba ne, ɗan Yusuf, wanda mahaifinsa da mahaifiyarsa duk mun san su? Yaya yanzu zai ce, ‘Na sauko daga sama?’ ” 43Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ku daina gunaguni a junanku. 44Ba mai iya zuwa wurina, sai dai in Uban da ya aiko ni ya jawo shi, ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe.
Kwanakin suna bin kalandar Julian ta Ikilisiyar Rasha (kamar Ikilisiyoyin Serbia da Georgia da Dutsen Athos): Mayu 7 a kalandar ikilisiya shi ne Mayu 20 a kalandar gari. Ikilisiyoyin da ke amfani da sabuwar kalanda (Girka, Romania, Bulgaria, Ukraine…) suna yin bukukuwan da ba sa canzawa da na tsarkaka a ainihin ranar gari, kwanaki 13 kafin haka, kuma wasu karatunsu sun bambanta; Ista da kwanakin da suka dogara da ita iri ɗaya ne.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi