Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Afirilu 2027 › Afirilu 3

Kalandar Katolika

Karatun Mass (Katolika) — Afirilu 3, 2027

Asabar · Kwana takwas na Ista

Bukukuwa da waliyyai

Asabar a cikin kwana takwas na Ista

Babban biki · Launin ibada: fari

Karatun yini

Karatu na farko

Ayy M 4:13–21

13Da suka ga ƙarfin halin Bitrus da Yohanna suka kuma gane cewa su marasa ilimi ne, talakawa kuma, sai suka yi mamaki suka kuma lura cewa waɗannan mutane sun kasance tare da Yesu. 14Amma da yake sun ga mutumin da aka warkar yana tsaye a wurin tare da su, sai suka rasa abin faɗi. 15Saboda haka suka umarta a fitar da su daga Majalisar, sa’an nan suka yi shawara da juna. 16Suka ce, “Me za mu yi da waɗannan mutane? Kowa da yake zama a Urushalima ya san sun yi abin banmamaki, kuma ba za mu iya yin mūsu wannan ba. 17Amma don a hana wannan abu daga ƙara bazuwa cikin mutane, dole mu kwaɓe mutanen nan kada su ƙara yi wa kowa magana cikin wannan suna.” 18Sai suka sāke kiransu ciki suka kuma umarce su kada su kuskura su yi magana ko su ƙara koyarwa a cikin sunan Yesu. 19Amma Bitrus da Yohanna suka amsa, “Ku shari’anta da kanku ko daidai ne a gaban Allah mu yi muku biyayya maimakon Allah. 20Gama ba za mu iya daina yin magana game da abin da muka gani muka kuma ji ba.” 21Bayan ƙarin barazana sai suka bar su su tafi. Ba su iya yanke shawara yadda za a hore su ba, domin dukan mutane suna yabon Allah saboda abin da ya faru.

Zaburar amsawa

Zab 118:1, 14–16, 18–21

1Ku gode wa Ubangiji, gama nagari ne shi; ƙaunarsa madawwamiya ce har abada. 14Ubangiji ne ƙarfina da waƙata; ya zama mai cetona. 15Sowa ta farin ciki da nasara sun fito a cikin tentunan adalai, “Hannun dama na Ubangiji ya aikata manyan abubuwa! 16An ɗaga hannun dama na Ubangiji sama; hannun dama na Ubangiji ya aikata manyan abubuwa!” 18Ubangiji ya hore ni sosai, amma bai ba da ni ga mutuwa ba. 19Buɗe mini ƙofofin adalci; zan shiga in kuma yi godiya ga Ubangiji. 20Wannan ne ƙofar Ubangiji inda adalai za su shiga. 21Zan yi maka godiya, domin ka amsa mini; ka zama mai cetona.

Bishara

Mar 16:9–15

9Da Yesu ya tashi daga matattu da safe, a ranar farko ta mako, ya fara bayyana ga Maryamu Magdalin, wadda ya fitar da aljanu bakwai daga cikinta. 10Ta je ta gaya wa waɗanda dā suke tare da shi, waɗanda kuma suke makoki da kuka. 11Da suka ji cewa Yesu yana da rai, har ma ta gan shi, ba su gaskata ba. 12Daga baya Yesu ya bayyana a wani kamanni dabam ga biyunsu, yayinda suke tafiya ƙauye. 13Waɗannan kuwa suka koma suka shaida wa sauran, amma su ma ba su gaskata ba. 14Bayan haka, Yesu ya bayyana ga Sha Ɗayan, yayinda suke cin abinci. Ya tsawata musu a kan rashin bangaskiyarsu, da yadda suka ƙi gaskata waɗanda suka gan shi bayan ya tashi. 15Ya ce, musu, “Ku tafi cikin dukan duniya, ku yi wa’azin bishara ga dukan halitta.

Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi