Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Afirilu 2027 › Afirilu 2

Kalandar Ortodoks · 20 ga Maris (tsohon lissafi)

Karatun Orthodox na ranar — Afirilu 2, 2027

Juma’a · Mako na 3 na Babban Azumi · Sauti na 2

Bukukuwa da waliyyai

Venerable Fathers slain at the Monastery of Saint Sabbas: John, Sergius, Patrick and others († 796)

Babban Azumi

Azumi mai tsanani (busasshen abinci: burodi, ganye, ’ya’yan itace)

Wannan yana bin dokar gidan zuhudu. A cikin ikkilisiya, ana tsara gwargwadon azumi tare da mai sauraron furcin zunubi, bisa ga lafiya, shekaru da yanayi.

Karatun yini

Sa’a ta 6

Ish 13:2–13

2A tā da tuta a kan tudun da yake mai fili, ka tā da murya gare su; ka ɗaga hannu ka ba su alama don su shiga ƙofofi masu alfarma. 3Na umarci tsarkakana; na umarci jarumawan yaƙina su gamsar da fushina, waɗanda suke farin ciki a nasarata. 4Ka saurara, akwai surutu a kan duwatsu, sai ka ce na babban taron jama’a! Ka saurara, akwai hayaniya a cikin mulkoki, sai ka ce al’ummai ne suna ta tattaruwa! Ubangiji Maɗaukaki yana shirya mayaƙa don yaƙi. 5Suna zuwa daga ƙasashe masu nesa, daga iyakokin duniya, Ubangiji da kuma fushinsa, zai hallaka dukan ƙasar. 6Ku yi ihu, gama ranar Ubangiji ta yi kusa za tă zo kamar hallaka daga Maɗaukaki. 7Saboda wannan, hannun kowane mutum zai yi rauni, ƙarfin halin kowane mutum zai kāsa. 8Tsoro zai kama su, zafi da azaba za su ci ƙarfinsu; za su yi ta murɗewa kamar mace mai naƙuda. Za su dubi juna a tsorace, fuskokinsu a ɓace. 9Duba, ranar Ubangiji tana zuwa, muguwar rana, mai hasala da zafin fushi, don ta mai da ƙasar kango ta kuma hallakar da masu zunubi da suke cikinta. 10Taurarin sama da ƙungiyoyinsu ba za su ba da haskensu ba. Rana za tă yi duhu wata kuma ba zai ba da haskensa ba. 11Zan hukunta duniya saboda muguntarta, mugaye saboda zunubansu. Zan kawo ƙarshe ga girman kan masu taƙama in kuma ƙasƙantar da ɗaga kan marasa tausayi. 12Zan sa mutum yă fi zinariya zalla wuyar samuwa, fiye da zinariyar Ofir wuyan gani. 13Saboda haka zan sa sammai su yi rawar jiki; duniya kuma za tă girgiza daga inda take a fushin Ubangiji Maɗaukaki, a ranar fushinsa mai ƙuna.

Addu’ar yamma: karatu

Far 8:4–21

4A rana ta goma sha bakwai ga watan bakwai, jirgin ya sauka a duwatsun Ararat. 5Ruwan ya ci gaba da janyewa har watan goma. A rana ta fari ga watan goma kuwa ƙwanƙolin duwatsun suka bayyana. 6Bayan kwana arba’in, sai Nuhu ya buɗe tagar jirgin da ya yi, 7ya saki hankaka. Hankaka ya yi ta kai da kawowa har sai da ruwa ya shanye a duniya. 8Sai ya saki kurciya don yă ga in ruwan ya janye daga doron ƙasa. 9Amma kurciyar ba tă sami inda za tă sa ƙafafunta ba gama akwai ruwa a dukan doron ƙasa, saboda haka ta komo wurin Nuhu a jirgi. Ya miƙa hannunsa ya ɗauko kurciyar ya shigar da ita wurinsa a cikin jirgi. 10Ya ƙara jira kwana bakwai, sai ya sāke aiken kurciyar daga jirgi. 11Sa’ad da kurciya ta komo wurinsa da yamma, sai ga ɗanyen ganyen zaitun da ta tsinko a bakinta! Sa’an nan Nuhu ya san cewa ruwa ya janye daga duniya. 12Ya ƙara jira kwana bakwai, sai ya sāke aiken kurciyar, amma a wannan ƙaro ba tă komo wurinsa ba. 13A rana ta fari ga wata na fari wanda Nuhu ya cika shekaru 601, ruwa ya shanye a ƙasa. Sai Nuhu ya buɗe murfin jirgin, ya ga cewa doron ƙasa ya bushe. 14A ran ashirin da bakwai ga wata na biyu, ƙasa ta bushe ƙaƙaf. 15Sa’an nan Allah ya ce wa Nuhu, 16“Fito daga jirgin, kai da matarka da ’ya’yanka maza da matansu. 17Ka fitar da kowane iri halitta mai rai da take tare da kai waje, tsuntsaye, dabbobi, da dukan halittu masu rarrafe a ƙasa, don su yi ta haihuwa, su yi yawa, su ƙaru a duniya.” 18Sai Nuhu ya fito tare da matarsa da ’ya’yansa maza da matan ’ya’yansa, 19da kowace irin dabba, da kowane mai rarrafe, da kowane irin tsuntsu, da kowane irin abu da yake tafiya a bisa duniya, suka fito daga jirgi daki-daki bisa ga irinsu. 20Sai Nuhu ya gina bagaden hadaya ga Ubangiji, ya ɗiba waɗansu dabbobi da tsuntsaye masu tsabta, ya yi hadaya ta ƙonawa da su a kan bagaden. 21Da Ubangiji ya ji ƙanshi mai daɗi, sai ya ce a zuciyarsa, “Ba zan ƙara la’anta ƙasa saboda mutum ba, ko da yake dukan tunanin zuciyar mutum mugu ne tun yana ƙarami. Ba kuwa zan ƙara hallaka dukan halittu masu rai, kamar yadda na yi ba.

Addu’ar yamma: karatu

K Mag 10:31–11:12

31Bakin adalai kan fitar da hikima, amma za a dakatar da mugun harshe. 32Leɓunan adalai sun san abin da ya dace, amma bakunan mugaye sun san abin da yake mugu ne kawai. 11:1Ubangiji yana ƙyamar ma’aunan zamba, amma ma’aunin da suke daidai ne abin farin cikinsa. 2Sa’ad da girman kai ya zo, sai shan kunya ta zo, amma hikima kan zo tare da ƙasƙantar da kai. 3Mutuncin masu aikata gaskiya takan bi da su, amma marasa aminci sukan hallaka ta wurin cin amanar da suke yi. 4Dukiya ba ta da amfani a ranar fushi, amma adalci kan yi ceto daga mutuwa. 5Adalcin marasa laifi kan miƙe hanyarsu, amma akan ƙasƙantar da mugaye ta wurin muguntarsu. 6Adalcin masu aikata gaskiya kan cece su, amma rashin aminci tarko ne ga mugayen sha’awace-sha’awace. 7Sa’ad da mugu ya mutu, sa zuciyarsa kan hallaka; dukan abin da ya sa zuciya daga ikonsa ba ya amfana kome. 8Akan kuɓutar da mai adalci daga wahala, sai ta dawo wa mugu a maimako. 9Da bakinsa marar sanin Allah kan hallaka maƙwabcinsa, amma ta wurin sani mai adalci kan kuɓuta. 10Sa’ad da adali ya yi nasara, birnin kan yi farin ciki; sa’ad da mugu ya hallaka, akwai sowa ta farin ciki. 11Ta wurin albarkar mai aikata gaskiya birni kan ƙasaita, amma ta wurin bakin mugu akan hallaka birnin. 12Mutum da ba shi da azanci kan ki maƙwabci, amma mutum mai fahimi kan ƙame harshensa.

Kwanakin suna bin kalandar Julian ta Ikilisiyar Rasha (kamar Ikilisiyoyin Serbia da Georgia da Dutsen Athos): Maris 20 a kalandar ikilisiya shi ne Afirilu 2 a kalandar gari. Ikilisiyoyin da ke amfani da sabuwar kalanda (Girka, Romania, Bulgaria, Ukraine…) suna yin bukukuwan da ba sa canzawa da na tsarkaka a ainihin ranar gari, kwanaki 13 kafin haka, kuma wasu karatunsu sun bambanta; Ista da kwanakin da suka dogara da ita iri ɗaya ne.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi