Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Afirilu 2027 › Afirilu 1
Kalandar Ortodoks · 19 ga Maris (tsohon lissafi)
Karatun Orthodox na ranar — Afirilu 1, 2027
Alhamis · Mako na 3 na Babban Azumi · Sauti na 2
Bukukuwa da waliyyai
Holy Martyrs Chrysanthus and Daria and with them Martyrs Claudius the Tribune with his wife Hilaria and their sons Jason and Maurus, and Diodorus the Priest and Marianus the Deacon at Rome († 283)
Babban Azumi
Azumi mai tsanani (busasshen abinci: burodi, ganye, ’ya’yan itace)
Wannan yana bin dokar gidan zuhudu. A cikin ikkilisiya, ana tsara gwargwadon azumi tare da mai sauraron furcin zunubi, bisa ga lafiya, shekaru da yanayi.
Karatun yini
Sa’a ta 6
10A wannan rana Saiwar Yesse zai miƙe kamar tuta don mutanenta; al’ummai za su tattaru wurinsa, wurin hutunsa kuma zai zama mai daraja. 11A wannan rana Ubangiji zai miƙa hannunsa sau na biyu don yă maido da raguwar da ta rage na mutanensa daga Assuriya, daga Masar ta Ƙasa, daga Masar ta Bisa, daga Kush, daga Elam, daga Babiloniya, daga Hamat da kuma daga tsibiran teku. 12Zai tā da tuta saboda al’ummai yă kuma tattara masu zaman bauta na Isra’ila; zai tattara mutanen Yahuda da suke a warwatse kusurwoyi huɗu na duniya. 13Kishin Efraim zai ɓace, za a kuma kau da abokan gāban Yahuda; Efraim ba zai yi kishin Yahuda ba, haka ma Yahuda ba zai yi gāba da Efraim ba. 14Tare za su fāɗa wa Filistiyawa da yaƙi daga yamma; tare za su washe mutane wajen gabas. Za su ɗibiya hannuwa a kan Edom da Mowab, Ammonawa kuma za su yi musu biyayya. 15Ubangiji zai busar da bakin tekun Masar; da iska mai zafi zai share hannunsa a bisa Kogin Yuferites Zai rarraba shi yă zama ƙanana rafuffuka bakwai saboda mutane su iya hayewa da ƙafa. 16Za a yi babbar hanya saboda raguwa mutanensa da ta rage daga Assuriya, kamar yadda ta kasance wa Isra’ila sa’ad da suka fito daga Masar. 12:1A wannan rana za ku ce, “Zan yabe ka, ya Ubangiji. Ko da yake a dā ka yi fushi da ni, amma yanzu ka daina fushi da ni ka kuwa ta’azantar da ni. 2Tabbatacce Allah shi ne mai cetona; zan dogara gare shi ba kuwa zan ji tsoro ba. Ubangiji, Ubangiji, ne ƙarfina da waƙata; ya zama mai cetona.”
Addu’ar yamma: karatu
11A ranar sha bakwai ga wata na biyu, na shekara ta ɗari shida na rayuwar Nuhu, a ran nan sai dukan maɓuɓɓugai na manyan zurfafa suka fashe, tagogin sammai suka buɗe. 12Ruwa yana ta kwararowa bisa duniya, yini arba’in da dare arba’in. 13A wannan rana Nuhu tare da matarsa da ’ya’yansa maza, Shem, Ham da Yafet da matansu uku suka shiga jirgi. 14Tare da su kuwa, akwai kowane naman jeji bisa ga irinsa, da dukan dabbobin gida bisa ga irinsu, da kowace halitta mai rarrafe a ƙasa bisa ga irinta, da kowane tsuntsun gida da na jeji bisa ga irinsa, da dukan abu mai fiffike. 15Biyu-biyu na dukan halittu masu numfashi suka zo wurin Nuhu, suka shiga jirgi. 16Dabbobi da kowane abu mai rai da suka shiga ciki, namiji ne da ta mace, yadda Allah ya umarci Nuhu. Sa’an nan Ubangiji ya kulle jirgin daga baya. 17Kwana arba’in ambaliya ta yi ta saukowa a duniya, sa’ad da ruwa ya yi ta ƙaruwa sai ya yi ta ɗaga jirgin sama, ya kuwa tashi can bisa duniya. 18Ruwa ya taso, ya ƙaru ƙwarai a duniya, jirgin kuma ya yi ta yawo a bisa ruwa. 19Ruwa ya ƙaru ƙwarai a duniya, ya kuma rufe dukan duwatsu masu tsawo a ƙarƙashin sammai. 20Ruwan ya taso ya rufe duwatsu, zurfin ruwa daga duwatsun zuwa inda jirgin yake ya fi ƙafa ashirin. 21Kowane abu mai rai da yake tafiya a duniya ya hallaka, tsuntsaye, dabbobin gida, namun jeji, da dukan masu rarrafe waɗanda suke rarrafe a duniya, da kuma dukan mutane. 22Kome a busasshiyar ƙasa da yake numfashi a hancinsa ya mutu. 23Aka kawar da kowane abu mai rai, mutane da dabbobi da halittu masu rarrafe a ƙasa, da tsuntsayen sama a doron ƙasa, duka aka kawar da su daga duniya. Nuhu kaɗai aka bari da waɗanda suke tare da shi a cikin jirgi. 24Ruwa ya mamaye duniya har kwana ɗari da hamsin. 8:1Amma Allah ya tuna da Nuhu da dukan namun jeji da dabbobin da suke tare da shi a cikin jirgi, ya kuma aika da wata iska ta hura dukan duniya, ruwan kuwa ya janye. 2Aka toshe maɓuɓɓugan zurfafa da ƙofofin ambaliyar sammai, ruwan sama kuma ya daina saukowa daga sarari. 3Ruwan ya janye a hankali daga ƙasa. A ƙarshen kwanaki ɗari da hamsin ɗin, ruwan ya ragu.
Addu’ar yamma: karatu
1Karin maganar Solomon. Ɗa mai hikima yakan kawo wa mahaifinsa farin ciki, amma wawan ɗa kan sa wa mahaifiyarsa baƙin ciki. 2Dukiyar da aka samu a hanyar da ba tă dace ba, ba ta da albarka, amma adalci kan ceci mutum daga mutuwa. 3Ubangiji ba ya barin mai adalci da yunwa amma yakan lalace burin mugu. 4Ragwanci kan sa mutum yă zama matalauci, amma aiki tuƙuru kan ba da dukiya. 5Shi da ya tattara hatsi da rani ɗa ne mai hikima, amma shi da yakan yi barci a lokacin girbi ɗa ne wanda ya zama abin kunya. 6Albarka kan zauna a kan mai adalci kamar rawani, amma rikici kan sha bakin mugu. 7Tunawa da mai adalci albarka ne amma sunan mugu zai ruɓe. 8Mai hikima a zuciya yakan yarda da umarni amma surutun wawa kan kai ga lalaci. 9Mai mutunci yana tafiya lafiya, amma shi da yake tafiya a karkatattun hanyoyi za a kama shi. 10Shi da ya ƙyifta ido da mugunta kan jawo baƙin ciki surutun wawa kuma kan zo da lalaci. 11Bakin adali maɓulɓulan rai ne, amma kalmar mugun takan ɓoye makircinsa. 12Ƙiyayya kan haddasa wahala, amma ƙauna kan rufe dukan laifofi. 13Ana samun hikima a leɓunan masu fahimi, amma bulala domin bayan marasa azanci ne. 14Mai hikima kan yi ajiyar sani, amma bakin wawa kan gayyaci lalaci. 15Dukiyar masu arziki yakan zama mafakar birninsu, amma talauci shi ne lalacin matalauci. 16Hakkin adalai kan kawo musu rai, amma albashin mugaye kan kawo musu hukunci. 17Duk wanda ya mai da hankali ga horo kan nuna hanyar rai, amma duk wanda ya ƙyale gyara kan sa waɗansu su kauce. 18Duk wanda ya ɓoye ƙiyayyarsa yana da ƙarya a leɓunansa, duk kuma wanda yake baza ƙarairayi wawa ne. 19Sa’ad da magana ta yi yawa, ba a rasa zunubi a ciki, amma shi da ya ƙame harshensa mai hikima ne. 20Harshen adali azurfa ce zalla, amma zuciyar mugu ba ta da wani amfani. 21Leɓunan adalai kan amfane yawanci, amma wawa kan mutu saboda rashin azanci. 22Albarkar Ubangiji kan kawo wadata, ba ya kuma ƙara wahala a kai.
Kwanakin suna bin kalandar Julian ta Ikilisiyar Rasha (kamar Ikilisiyoyin Serbia da Georgia da Dutsen Athos): Maris 19 a kalandar ikilisiya shi ne Afirilu 1 a kalandar gari. Ikilisiyoyin da ke amfani da sabuwar kalanda (Girka, Romania, Bulgaria, Ukraine…) suna yin bukukuwan da ba sa canzawa da na tsarkaka a ainihin ranar gari, kwanaki 13 kafin haka, kuma wasu karatunsu sun bambanta; Ista da kwanakin da suka dogara da ita iri ɗaya ne.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi