Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Maris 2027 › Maris 25
Kalandar Ortodoks · 12 ga Maris (tsohon lissafi)
Karatun Orthodox na ranar — Maris 25, 2027
Alhamis · Mako na 2 na Babban Azumi · Sauti na 1
Bukukuwa da waliyyai
Venerable Theophanes the Confessor of Sigriane († 818)
Babban Azumi
Azumi mai tsanani (busasshen abinci: burodi, ganye, ’ya’yan itace)
Wannan yana bin dokar gidan zuhudu. A cikin ikkilisiya, ana tsara gwargwadon azumi tare da mai sauraron furcin zunubi, bisa ga lafiya, shekaru da yanayi.
Karatun yini
Sa’a ta 6
1A shekarar da Sarki Uzziya ya mutu, na ga Ubangiji zaune a kan kujerar sarauta a sama cike da ɗaukaka, zatinsa ya cika haikali. 2A bisansa akwai serafofi, kowanne yana da fikafikai shida. Fikafikai biyu sun rufe fuskokinsu, da biyu suka rufe ƙafafunsu, biyu kuma da su suke tashi. 3Suna kiran juna, “Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki! Ubangiji Maɗaukaki ne; duniya ta cika da ɗaukakarsa.” 4Da jin ƙarar muryoyinsu madogarai da madogaran ƙofa suka girgiza, haikali kuma ya cika da hayaƙi. 5Sai na tā da murya na ce, “Kaitona! Na shiga uku! Gama ni mutum ne mai leɓuna marar tsarki, kuma ina raye a cikin mutane masu leɓuna marasa tsarki, idanuna kuma sun ga Sarki, Ubangiji Maɗaukaki.” 6Sai ɗaya daga cikin serafofin ya yi firiya zuwa wurina tare da garwashi mai wuta a hannunsa, wanda ya ɗiba da arautaki daga bagade. 7Da shi ne ya taɓa bakina ya ce, “Duba, wannan ya taɓa leɓunanka, yanzu fa an kawar da laifofinka, an kuma gafarta maka zunubanka.” 8Sa’an nan na ji muryar Ubangiji tana cewa, “Wa zan aika? Wa zai tafi mana?” Sai na ce, “Ga ni! Ka aike ni!” 9Ya ce, “Je ka ka faɗa wa wannan mutane, “ ‘Kome yawan kasa kunne da za ku yi, ba za ku fahimta ba; Kome yawan dubar da za ku yi, ba za ku san abin da yake faruwa ba.’ 10Ka sa zuciyar mutanen nan ta dushe; kunnuwansu su kurunce, idanunsu kuma su makance. In ba haka ba za su iya gani da idanunsu, su ji da kunnuwansu, su fahimta da zuciyarsu, su kuma juyo a kuma warkar da su.” 11Sa’an nan na ce, “Har yaushe, ya Ubangiji?” Ya kuma amsa, “Sai an lalatar da biranen ba kowa a ciki, sai an mai da gidaje kangwaye ƙasa kuma ta zama kango ba amfani, 12sai lokacin da Ubangiji ya kori kowa aka kuma yashe ƙasar gaba ɗaya.
Addu’ar yamma: karatu
1Wannan shi ne rubutaccen tarihin zuriyar Adamu. Sa’ad da Allah ya halicci mutum, ya yi shi cikin kamannin Allah. 2Ya halicce su namiji da ta mace, ya kuma albarkace su. Sa’ad da kuma aka halicce su, ya kira su “Mutum.” 3Sa’ad da Adamu ya yi shekaru 130, sai ya haifi ɗa wanda ya yi kama da shi, ya kuma kira shi Set. 4Bayan an haifi Set, Adamu ya yi shekaru 800, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. 5Gaba ɗaya dai, Adamu ya yi shekaru 930, sa’an nan ya mutu. 6Sa’ad da Set ya yi shekara 105, sai ya haifi Enosh. 7Bayan ya haifi Enosh, Set ya yi shekara 807, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. 8Gaba ɗaya dai, Set ya yi shekaru 912, sa’an nan ya mutu. 9Sa’ad da Enosh ya yi shekara 90, sai ya haifi Kenan. 10Bayan ya haifi Kenan, Enosh ya yi shekara 815, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. 11Gaba ɗaya dai, Enosh ya yi shekaru 905, sa’an nan ya mutu. 12Sa’ad da Kenan ya yi shekara 70, sai ya haifi Mahalalel. 13Bayan ya haifi Mahalalel, Kenan ya yi shekara 840, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata 14Gaba ɗaya dai, Kenan ya yi shekara 910, sa’an nan ya mutu. 15Sa’ad da Mahalalel ya yi shekara 65, sai ya haifi Yared. 16Bayan ya haifi Yared, Mahalalel ya yi shekara 830, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata 17Gaba ɗaya dai, Mahalalel ya yi shekara 895, sa’an nan ya mutu. 18Sa’ad da Yared ya yi shekara 162, sai ya haifi Enok. 19Bayan ya haifi Enok, Yared ya yi shekaru 800, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. 20Gaba ɗaya dai, Yared ya yi shekara 962, sa’an nan ya mutu. 21Sa’ad da Enok ya yi shekara 65, sai ya haifi Metusela. 22Bayan ya haifi Metusela, Enok ya kasance cikin zumunci da Allah shekaru 300, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. 23Gaba ɗaya dai, Enok ya yi shekaru 365. 24Enok ya kasance cikin zumunci da Allah, sa’an nan ba a ƙara ganinsa ba. Saboda Allah ya ɗauke shi.
Addu’ar yamma: karatu
3to, sai ka yi haka, ɗana don ka ’yantar da kanka; da yake ka shiga hannuwan maƙwabcinka, ka tafi ka ƙasƙantar da kanka; ka roƙi maƙwabcinka! 4Ka hana kanka barci, ko gyangyaɗi a idanunka ma. 5Ka ’yantar da kanka, kamar barewa daga hannun mai farauta, kamar tsuntsu daga tarkon mai kafa tarko. 6Ku tafi wurin kyashi, ku ragwaye; ku lura da hanyoyinsa ku zama masu hikima! 7Ba shi da jagora ba shugaba ko mai mulki, 8duk da haka yakan yi tanade-tanadensa da rani ya kuma tattara abincinsa a lokacin girbi. 9Har yaushe za ku kwanta a can, ku ragwaye? Yaushe za ku farka daga barcinku? 10Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi, ɗan naɗin hannuwa don a huta, 11talauci kuwa zai zo kamar ’yan hari rashi kuma kamar ɗan fashi. 12Sakare da mutumin banza wanda yana yawo da magana banza a baki, 13wanda yake ƙyifce da ido, yana yi alama da ƙafafunsa yana kuma nuni da yatsotsinsa, 14wanda yake ƙulla mugunta da ruɗu a cikin zuciyarsa, kullum yana tā-da-na-zaune-tsaye 15Saboda haka masifa za tă fāɗa farat ɗaya; za a hallaka shi nan da nan, ba makawa. 16Akwai abubuwa shida da Ubangiji ya ƙi, abubuwa bakwai da suke abin ƙyama gare shi, 17duban reni, harshe mai ƙarya, hannuwa masu zub da jinin marar laifi, 18zuciyar da take ƙulla mugayen dabaru, ƙafafun da suke sauri zuwa aikata mugunta, 19mai shaidar ƙarya wanda yake zuba ƙarairayi, da kuma mutumin da yake tā-da-na-zaune-tsaye a cikin ’yan’uwa. 20Ɗana, ka kiyaye umarnan mahaifinka kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.
Kwanakin suna bin kalandar Julian ta Ikilisiyar Rasha (kamar Ikilisiyoyin Serbia da Georgia da Dutsen Athos): Maris 12 a kalandar ikilisiya shi ne Maris 25 a kalandar gari. Ikilisiyoyin da ke amfani da sabuwar kalanda (Girka, Romania, Bulgaria, Ukraine…) suna yin bukukuwan da ba sa canzawa da na tsarkaka a ainihin ranar gari, kwanaki 13 kafin haka, kuma wasu karatunsu sun bambanta; Ista da kwanakin da suka dogara da ita iri ɗaya ne.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi