Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Maris 2027 › Maris 22

Kalandar Ortodoks · 9 ga Maris (tsohon lissafi)

Karatun Orthodox na ranar — Maris 22, 2027

Litinin · Mako na 2 na Babban Azumi · Sauti na 1

Bukukuwa da waliyyai

The Holy Forty Martyrs of Sebaste († c.320): Cyrion, Candidus, Domnus, Hesychius, Iraclius, Smaragdus, Eunoicus, Valentus, Vivian, Claudius, Priskus, Theodulus, Eutichius, John, Xanthus, Ilian, Sisinius, Angius, Aetius, Flavius, Dometian, Gaius, Leontius, Athanasius, Cyrill, Sakerdonus, Nicholas, Valerius, Philoctimon, Seberian, Chudionus, Aglaius, and Meliton

Babban Azumi

Azumi: da mai

Wannan yana bin dokar gidan zuhudu. A cikin ikkilisiya, ana tsara gwargwadon azumi tare da mai sauraron furcin zunubi, bisa ga lafiya, shekaru da yanayi.

Karatun yini

Addu’ar asuba: Bishara (domin shahidai)

Luk 21:12–19

12“Amma kafin duk abubuwa nan, za a kama ku a tsananta muku. Za a kai ku majami’u, da kurkuku. Za a kuma kai ku gaban sarakuna da gwamnoni, kuma dukan waɗannan saboda sunana. 13Wannan zai sa ku zama shaidu a gare su. 14Amma ku yi ƙuduri, wato, ku shirya zuciyarku, a kan ba za ku damu ba kafin lokacin, game da yadda za ku kāre kanku. 15Gama zan ba ku kalmomi, da hikima waɗanda ba ko ɗaya daga cikin maƙiyanku, za su iya tsayayya da ku, ko su ƙaryata. 16Har iyayenku, da ’yan’uwanku maza, da danginku, da abokanku ma, duk za su bashe ku, su kuma kashe waɗansunku. 17Duk mutane za su ƙi ku saboda ni. 18Amma ko gashi ɗaya na kanku, ba zai hallaka ba. 19Ta wurin tsayawa da ƙarfi, za ku sami rai.

Sa’a ta 6

Ish 4:2–5:7

2A wannan rana Reshen Ubangiji zai zama kyakkyawa da kuma ɗaukaka, kuma amfanin ƙasar zai zama abin fariya da ɗaukakar waɗanda suka rayu a Isra’ila. 3Waɗanda suka rage a Sihiyona, waɗanda suka rage a Urushalima, za a ce da su masu tsarki, wato, dukan waɗanda aka rubuta a cikin masu rai a Urushalima. 4Ubangiji zai wanke duk wani ƙazantar matan Sihiyona; ya tsabtacce jinin da aka zubar daga Urushalima ta wurin ruhun hukunci da yake ƙuna kamar wuta. 5Sa’an nan Ubangiji zai sa girgijen hayaƙi da rana da harshen wuta da dare a bisa dukan Dutsen Sihiyona da kuma bisa waɗanda suka tattaru a can; a bisa duka kuwa ɗaukakar za tă zama rumfa. 6Za tă zama rumfa da inuwar da za tă tare zafin rana, da kuma mafaka da wurin ɓuya daga hadari da ruwan sama. 5:1Zan rera waƙa wa ƙaunataccena waƙa game da gonar inabinsa. Ƙaunataccena yana da gonar inabi a gefen tudu mai dausayi. 2Ya haƙa ƙasa ya kuma tsintsince duwatsun ya shuka mata inabi mafi kyau. Ya gina hasumiyar tsaro a cikinta ya kuma shirya wurin matsin ruwan inabi. Sa’an nan ya sa rai ga samun girbi mai kyau na inabin, amma sai ga shi inabin ya ba da munanan ’ya’ya. 3“Yanzu fa ku mazauna cikin Urushalima da mutanen Yahuda, ku shari’anta tsakanina da gonar inabina. 4Me kuma ya rage da za a yi wa gonar inabina fiye da abin da na yi mata? Da na nemi inabi masu kyau, me ya sa ta ba da munana ’ya’ya? 5Yanzu zan faɗa muku abin da zan yi da gonar inabina. Zan cire katangar da ta kewaye ta, za tă kuwa lalace; zan rushe bangonta, za a kuwa tattake ta. 6Zan mai da ita kango, ba zan aske ta ba, ba kuwa zan nome ta ba, sarƙaƙƙiya da ƙayayyuwa kuwa za su yi girma a can Zan umarci gizagizai kada su yi ruwan sama a kanta.” 7Gonar inabin Ubangiji Maɗaukaki ita ce gidan Isra’ila, mutanen Yahuda kuma su ne lambun farin cikinsa. Yana kuma nema ganin gaskiya, amma sai ga zub da jini; yana neman adalci, amma sai ga shi kukan azaba yake ji.

Addu’ar yamma: karatu

Far 3:21–4:7

21Ubangiji Allah ya yi tufafin fata domin Adamu da Hawwa’u, ya kuma yi musu sutura. 22Ubangiji Allah ya kuma ce, “To, fa, mutum ya zama kamar ɗaya daga cikinmu, ya san abin da yake mai kyau da abin da yake mugu. Kada a yarda yă miƙa hannunsa yă ɗiba daga itacen rai yă ci, yă kuma rayu har abada.” 23Saboda haka Ubangiji Allah ya kore shi daga Lambun Eden domin yă nome ƙasa wadda aka yi shi. 24Bayan da ya kori mutumin, sai ya sa kerubobi da takobi mai harshen wuta yana jujjuyawa baya da gaba a gabashin Lambun Eden don yă tsare hanya zuwa itacen rai. 4:1Adamu ya kwana da matarsa Hawwa’u, ta kuwa yi ciki ta haifi Kayinu. Sai ta ce, “Da taimakon Ubangiji na sami ɗa namiji.” 2Daga baya ta haifi ɗan’uwansa, ta kuma ba shi suna Habila. Sa’ad da suka yi girma sai Habila ya zama makiyayin tumaki, Kayinu kuwa ya zama manomi. 3Ana nan sai Kayinu ya kawo waɗansu amfanin gona a matsayin hadaya ga Ubangiji. 4Amma Habila ya kawo mafi kyau daga ’ya’yan fari na garkensa. Ubangiji ya yi farin ciki da sadakar da Habila ya kawo, 5amma bai yi farin ciki da sadakar da Kayinu ya kawo ba. Saboda haka Kayinu ya ji fushi sosai, fuskarsa kuma ta ɓace. 6Sai Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Don me kake fushi? Don me fuskarka ta ɓace? 7Da ka yi abin da yake daidai, ai, da ka sami karɓuwa. Amma tun da ba ka yi abin da ba daidai ba, zunubi zai yi fakonka don yă rinjaye ka kamar naman jeji. Yana so yă mallake ka, amma tilas ka rinjaye shi.”

Addu’ar yamma: karatu

K Mag 3:34–4:22

34Yakan yi wa masu girman kai ba’a amma yakan yi wa mai sauƙinkai alheri. 35Masu hikima sukan sami kyakkyawan suna, amma wawaye sukan ƙara wa kansu shan kunya. 4:1Ku saurara ’ya’yana ga koyarwar mahaifinku; ku mai da hankali, ku sami fahimi. 2Ina ba ku sahihiyar koyarwa, saboda haka kada ku ƙyale koyarwata. 3Sa’ad da nake yaro a gidan mahaifina, yaro kaɗai kuma na mahaifiyata, 4ya koya mini ya ce, “Ka riƙe kalmomina da dukan zuciyarka; ka kiyaye umarnaina za ka kuwa rayu. 5Ka nemi hikima, ka nemi fahimi; kada ka manta da kalmomina ko ka kauce daga gare su. 6Kada ka ƙyale hikima, za tă kuwa tsare ka; ka ƙaunace ta, za tă kuwa lura da kai. 7Hikima ce mafi girma duka; saboda haka ka nemi hikima. Ko da za tă ci duk abin da kake da shi, ka dai nemi fahimi. 8Ka ƙaunace ta, za tă ɗaukaka ka; ka rungume ta, za tă kuwa girmama ka. 9Za tă zama kayan ado da za su inganta kanka tă kuma zamar maka rawanin ɗaukaka.” 10Ka saurara, ɗana, ka yarda da abin da na faɗa, shekarun rayuwarka kuwa za su zama masu yawa. 11Na bishe ka a hanyar hikima na kuma jagorance ka a miƙaƙƙun hanyoyi. 12Sa’ad da kake tafiya, ba abin da zai sa ka tuntuɓe; sa’ad da kake gudu, ba za ka fāɗi ba. 13Ka riƙe umarni, kada ka bari yă kuɓuce; ka tsare shi sosai, gama ranka ne. 14Kada ka sa ƙafa a kan hanyar mugaye kada ka bi gurbin mugaye. 15Ka guji mugunta, kada ka yi tafiya a kanta; juya daga gare ta ka yi tafiyarka. 16Mugaye ba sa iya barci, sai sun aikata mugunta; ba su barci sai sun cuci wani. 17Mugunta da ta’adi kamar ci da sha suke a gare su. 18Hanyar adali kamar fitowar rana ce, sai ƙara haske take yi, har ta kai tsaka. 19Amma hanyar mugaye kamar zurfin duhu ne; ba sa sanin abin da ya sa suke tuntuɓe. 20Ɗana, ka kula da abin da nake faɗa, ka saurara sosai ga kalmomina. 21Kada ka bari su rabu da kai, ka kiyaye su a cikin zuciyarka; 22gama rai ne ga waɗanda suke nemansu da kuma lafiya ga dukan jikin mutum.

Addu’ar yamma: karatu (domin shahidai)

Ish 43:9–14

9Dukan al’ummai su taru mutane kuma su tattaru. Wane ne a cikinsu ya yi faɗar wannan ya kuma yi mana shelar abubuwan da suka riga suka faru? Bari su kawo shaidunsu don su tabbatar cewa sun yi daidai, don waɗansu su ji su kuma ce, “Gaskiya ne.” 10“Ku ne shaiduna,” in ji Ubangiji, “bawana kuma wanda na zaɓa, saboda ka sani ka kuma gaskata ni ka kuma fahimci cewa ni ne shi. Kafin ni babu allahn da aka siffanta, ba kuwa za a yi wani a bayana ba. 11Ni kaɗai, ni ne Ubangiji, kuma in ban da ni babu wani mai ceto. 12Na bayyana na ceci na kuma furta, Ni ne, ba wani baƙon allah a cikinku. Ku ne shaiduna,” in ji Ubangiji, “cewa ni ne Allah. 13I, kuma tun fil azal ni ne shi. Babu wani da zai amshi daga hannuna. Sa’ad da na aikata, wa zai iya sauyawa?” 14Ga abin da Ubangiji yana cewa, Mai Fansarku, Mai Tsarkin nan na Isra’ila, “Saboda ku zan aika Babilon in kawo dukan Babiloniyawa kamar masu gudun hijira, a cikin jiragen ruwa waɗanda suke taƙama da su.

Addu’ar yamma: karatu (domin shahidai)

Ba ya cikin wannan fassara

Addu’ar yamma: karatu (domin shahidai)

Ba ya cikin wannan fassara

Wasiƙa (domin shahidai)

Ibr 12:1–10

1Saboda haka, da yake muna kewaye da irin wannan taron shaidu mai girma, sai mu yar da duk abin da yake hana mu da kuma zunubin da yake saurin daure mu, mu kuma yi tseren da aka sa a gabanmu da nacewa. 2Bari mu kafa idanunmu a kan Yesu, tushe da kuma kammalar bangaskiyarmu, wanda ya jure kunyar gicciye da aka yi masa, domin ya san cewa daga baya zai yi farin ciki ya yi haka. Yanzu kuma yana zaune a hannun dama na kursiyin Allah. 3Ku lura da wannan wanda ya jure da irin hamayyan nan daga masu zunubi, don kada ku gaji, har ku fid da zuciya. 4Cikin famanku da zunubi, ba ku yi tsayayya har ga zub da jininku ba tukuna. 5Kun kuma manta da kalmar ƙarfafawan nan da tana ce da ku ’ya’ya, “Ɗana kada ka rena horon Ubangiji, kada kuma ka fid da zuciya sa’ad da ya kwaɓe ka, 6domin Ubangiji yakan hori waɗanda yake ƙauna, yakan kuma hori duk wanda yakan karɓa a matsayin ɗa.” 7Ku jimre shan wahala a matsayin horo; Allah yana yi da ku kamar ’ya’ya. Gama wane ɗa ne mahaifinsa ba ya horonsa? 8In ba a hore ku ba (kowa kuwa yakan sami horo), to, ku shegu ne ba ’ya’yan gida ba. 9Ban da haka ma, dukanmu mun kasance da ubannin jiki waɗanda suka hore mu muka kuma yi musu ladabi. Ashe, bai kamata mu yi wa Uban ruhohinmu biyayya mu kuwa rayu ba! 10Ubanninmu sun hore mu na ɗan lokaci yadda suka ga ya fi kyau; amma Allah yakan hore mu don amfaninmu, domin mu sami rabo cikin tsarkinsa.

Bishara (domin shahidai)

Mat 20:1–16

1“Mulkin sama yana kama da wani mai gona, wanda ya fita da sassafe don yă yi hayar mutane su yi aiki a gonar inabinsa. 2Ya yarda yă biya su dinari guda a yini, sai ya tura su gonar inabinsa. 3“Wajen sa’a ta uku, ya fita sai ya ga waɗansu suna tsattsaye a bakin kasuwa ba sa kome. 4Ya ce musu, ‘Ku ma ku tafi gonar inabina ku yi aiki, zan kuwa biya ku abin da ya dace.’ 5Saboda haka suka tafi. “Ya sāke fita a sa’a ta shida da kuma sa’a ta tara, ya sāke yin haka. 6Wajen sa’a ta goma sha ɗaya, ya sāke fita, ya tarar da waɗansu har yanzu suna tsattsaye. Ya tambaye su, ‘Don me kuke yini tsattsaye a nan ba kwa kome?’ 7“Suka amsa, ‘Don ba wanda ya ɗauke mu aiki.’ “Ya ce musu, ‘Ku ma ku je ku yi aiki a gonar inabina.’ 8“Sa’ad da yamma ta yi, sai mai gonar inabin ya ce wa wakilinsa, ‘Kira ma’aikatan, ka biya su hakkin aikinsu, fara daga waɗanda aka ɗauke su a ƙarshe har zuwa na farko.’ 9“Ma’aikatan da ka ɗauka wajen sa’a ta goma sha ɗaya suka zo, kowannensu kuwa ya karɓi dinari guda. 10Saboda haka da waɗanda aka ɗauka da fari suka zo, sun zaci za su sami fiye da haka. Amma kowannensu ma ya karɓi dinari guda. 11Sa’ad da suka karɓa, sai suka fara yin gunaguni a kan mai gonar. 12Suna cewa, ‘Waɗannan mutanen da aka ɗauka a ƙarshe sun yi aikin sa’a ɗaya ne kawai, ka kuma mai da su daidai da mu da muka yini muna faman aiki, muka kuma sha zafin rana.’ 13“Amma ya amsa wa ɗayansu ya ce, ‘Aboki, ban cuce ka ba. Ba ka yarda ka yi aiki a kan dinari guda ba? 14Ka karɓi hakkinka ka tafi. Ni na ga damar ba waɗannan na ƙarshe daidai da yadda na ba ka. 15Ba ni da ikon yin abin da na ga dama da kuɗina ne? Ko kana kishi saboda ni mai kyauta ne?’ 16“Saboda haka fa, na ƙarshe za su zama na farko, na farko kuma su zama na ƙarshe.”

Kwanakin suna bin kalandar Julian ta Ikilisiyar Rasha (kamar Ikilisiyoyin Serbia da Georgia da Dutsen Athos): Maris 9 a kalandar ikilisiya shi ne Maris 22 a kalandar gari. Ikilisiyoyin da ke amfani da sabuwar kalanda (Girka, Romania, Bulgaria, Ukraine…) suna yin bukukuwan da ba sa canzawa da na tsarkaka a ainihin ranar gari, kwanaki 13 kafin haka, kuma wasu karatunsu sun bambanta; Ista da kwanakin da suka dogara da ita iri ɗaya ne.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi