Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Maris 2027 › Maris 23
Kalandar Ortodoks · 10 ga Maris (tsohon lissafi)
Karatun Orthodox na ranar — Maris 23, 2027
Talata · Mako na 2 na Babban Azumi · Sauti na 1
Bukukuwa da waliyyai
Martyr Quadratus and those with him at Corinth († 250-258): Cyprian, Dionysius, Anectus, Paul, Criscentus, another Dionysius, Victorinus, Victor, Niciphorus, Claudius, Diodorus, Serapion, Papius, Leonidus, and the holy women Chariessa, Nunechia, Basilissa, Nica, Calisa, Gala, Galina, Theodora, and many others
Babban Azumi
Azumi mai tsanani (busasshen abinci: burodi, ganye, ’ya’yan itace)
Wannan yana bin dokar gidan zuhudu. A cikin ikkilisiya, ana tsara gwargwadon azumi tare da mai sauraron furcin zunubi, bisa ga lafiya, shekaru da yanayi.
Karatun yini
Sa’a ta 6
7Gonar inabin Ubangiji Maɗaukaki ita ce gidan Isra’ila, mutanen Yahuda kuma su ne lambun farin cikinsa. Yana kuma nema ganin gaskiya, amma sai ga zub da jini; yana neman adalci, amma sai ga shi kukan azaba yake ji. 8Kaitonku ku waɗanda kuke ƙara wa kanku gidaje kuke kuma haɗa gonaki da gonaki har babu sauran filin da ya rage ku kuma zauna ku kaɗai a ƙasar. 9Ubangiji Maɗaukaki ya furta a kunnuwana, “Tabbatacce manyan gidajen za su zama kango, za a bar kyawawan gidajen nan ba kowa. 10Kadada goma na gonar inabi zai ba da garwan ruwan inabi ɗaya kaɗai, mudu guda na iri kuma zai ba da efa na hatsi guda kurum.” 11Kaiton waɗanda suke tashi da sassafe don su nufi wurin shaye-shaye, waɗanda suke raba dare har sai sun bugu da ruwan inabi. 12Suna kaɗa garaya, da molaye a bukukkuwansu, ganguna da busa da ruwan inabi, amma ba su kula da ayyukan Ubangiji ba, ba sa biyayya ga aikin hannuwansa. 13Saboda haka mutanena za su yi zaman bauta domin rashin fahimi; manyan mutanensu za su mutu da yunwa talakawansu kuma su mutu da ƙishirwa. 14Saboda haka kabari ya fadada marmarinsa ya kuma buɗe bakinsa babu iyaka; cikinsa manyan mutanensu da talakawansu za su gangara tare da dukan masu hayaniyarsu da masu murnansu. 15Ta haka za a ƙasƙantar da mutum kuma za a ƙasƙantar da ’yan adam, za a ƙasƙanta da masu girman kai. 16Amma Ubangiji Maɗaukaki zai sami ɗaukaka ta wurin aikata gaskiya, kuma Allah mai tsarki zai nuna kansa ta wurin adalcinsa.
Addu’ar yamma: karatu
8To, Kayinu ya ce wa ɗan’uwansa Habila, “Mu tafi gona.” Yayinda suke a gona, sai Kayinu ya tasar wa Habila ya buge shi ya kashe. 9Sai Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Ina ɗan’uwanka Habila?” Sai Kayinu ya ce, “Ban sani ba, ni mai gadin ɗan’uwana ne?” 10Ubangiji ya ce, “Me ke nan ka yi? Saurara! Ga jinin ɗan’uwanka yana mini kuka daga ƙasa. 11Yanzu, kai la’ananne ne, an kuma kore ka daga ƙasa wadda ta buɗe bakinta ta shanye jinin ɗan’uwanka daga hannunka. 12In ka nome ƙasa, ba za tă ƙara ba ka hatsinta ba. Za ka kuma zama mai yawo barkatai a duniya.” 13Kayinu ya ce wa Ubangiji, “Horon nan ya sha ƙarfina. 14Ga shi, yau kana kori na daga ƙasar, zan zama a ɓoye daga fuskarka, zan kuma zama mai yawo barkatai, duk wanda ya same ni kuwa zai kashe ni.” 15Amma Ubangiji ya ce masa, “Ba haka ba ne! Duk wanda ya kashe Kayinu, za a ninƙa hukuncinsa har sau bakwai.” Sa’an nan Ubangiji ya sa wa Kayinu alama don duk wanda ya same shi kada yă kashe shi.
Addu’ar yamma: karatu
1Ɗana, ka mai da hankali ga hikimata ka saurara da kyau ga kalmomin basirata, 2don ka ci gaba da yin kome daidai leɓunanka za su adana sani. 3Gama leɓunan mazinaciya na ɗigan zuma, maganarta tana da sulɓi fiye da mai; 4amma a ƙarshe tana da ɗaci kamar tafashiya, mai ci kamar takobi mai kaifi biyu. 5Ƙafafunta na kaiwa ga mutuwa; sawunta na jagora kai tsaye zuwa kabari. 6Ba ta wani tunanin rayuwa; hanyoyinta karkatacce ne, amma ba tă sani ba. 7Yanzu fa, ’ya’yana, ku saurare ni; kada ku juye daga abin da nake faɗa. 8Ku yi nesa da hanyarta, kana ku je kusa da ƙofar gidanta, 9don kada ku ba da ƙarfi mafi kyau ga waɗansu da kuma shekarunku ga wani marar imani, 10don kada baƙi su yi biki a kan dukiyarku wahalarku ta azurta gidan wani mutum dabam. 11A ƙarshen rayuwarku za ku yi ta nishi, sa’ad da namanku da jikinku suka zagwanye. 12Za ku ce, “Me ya sa na ƙi horo! Me ya sa zuciyata ta ƙi gyara! 13Ban yi biyayya da malamaina ba ko in saurari masu koyar da ni. 14Na zo gab da hallaka gaba ɗaya a tsakiyar dukan taron.” 15Ku sha ruwa daga tankinku, ruwa mai gudu daga rijiyarku.
Kwanakin suna bin kalandar Julian ta Ikilisiyar Rasha (kamar Ikilisiyoyin Serbia da Georgia da Dutsen Athos): Maris 10 a kalandar ikilisiya shi ne Maris 23 a kalandar gari. Ikilisiyoyin da ke amfani da sabuwar kalanda (Girka, Romania, Bulgaria, Ukraine…) suna yin bukukuwan da ba sa canzawa da na tsarkaka a ainihin ranar gari, kwanaki 13 kafin haka, kuma wasu karatunsu sun bambanta; Ista da kwanakin da suka dogara da ita iri ɗaya ne.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi