Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Maris 2027 › Maris 16
Kalandar Ortodoks · 3 ga Maris (tsohon lissafi)
Karatun Orthodox na ranar — Maris 16, 2027
Talata · Mako na 1 na Babban Azumi · Sauti na 8
Bukukuwa da waliyyai
Martyrs Eutropius, Cleonicus and Basiliscus of Amasea († c. 308)
Babban Azumi
Azumi mai tsanani (busasshen abinci: burodi, ganye, ’ya’yan itace)
Wannan yana bin dokar gidan zuhudu. A cikin ikkilisiya, ana tsara gwargwadon azumi tare da mai sauraron furcin zunubi, bisa ga lafiya, shekaru da yanayi.
Karatun yini
Sa’a ta 6
19In kuna da niyya kuna kuma yi mini biyayya, za ku ci abubuwa masu kyau daga ƙasar; 20amma in kuka yi tsayayya kuka kuma yi tayarwa, za a kashe ku da takobi.” Ni Ubangiji na faɗa. 21Dubi yadda amintacciyar birni ta zama karuwa! Dā ta cika da yin gaskiya; dā masu adalci a can suke zama, amma yanzu sai masu kisankai kaɗai! 22Azurfarki ta zama jebu, an gauraye ruwan inabinki mafi kyau da ruwa. 23Masu mulkinki ’yan tawaye ne, abokan ɓarayi; dukansu suna ƙaunar cin hanci suna bin kyautai. Ba sa taɓa tsare marayu a ɗakin shari’a; ba sa taimakon gwauruwa. 24Saboda haka Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, Mai Iko nan na Isra’ila, ya furta, “Kai, zan sami hutu daga maƙiyana in kuma yi ramuwa a kan abokan gābana. 25Zan juye hannuna a kanki; zan wanke ke sarai in fitar da dukan ƙazantarki. 26Zan maido da alƙalanki kamar yadda suke a dā can, mashawartanki kamar yadda suke da fari. Bayan haka za a ce da ke Birnin Masu Adalci, Amintacciyar Birni.” 27Za a fanshi Sihiyona da adalci, masu tubanta kuma da aikin gaskiya. 28Amma za a karye ’yan tawaye da masu zunubi, waɗanda suka rabu da Ubangiji kuma za su hallaka. 29“Za ku ji kunya saboda masujadan ƙarƙashin itatuwan oak da kuka yi farin ciki; za a kunyata ku saboda lambun da kuka zaɓa. 30Za ku zama kamar itacen oak mai busasshen ganyaye, kamar lambu marar ruwa. 31Mutum mai ƙarfi zai zama kamar rama, aikinsa kuma kamar tartsatsin wuta; duka za su ƙone tare, ba kuwa wanda zai kashe wutar.” 2:1Ga abin da Ishaya ɗan Amoz ya gani game da Yahuda da Urushalima. 2A kwanaki masu zuwa za a kafa dutsen haikalin Ubangiji a matsayin babba cikin duwatsu; za a daga shi bisa tuddai, kuma dukan al’ummai za su bumbunto zuwa gare shi. 3Mutane da yawa za su zo su ce, “Ku zo, bari mu haura zuwa dutsen Ubangiji, zuwa gidan Allah na Yaƙub. Zai koya mana hanyoyinsa, domin mu yi tafiya cikin hanyoyinsa.” Dokar za tă fito daga Sihiyona, maganar Ubangiji daga Urushalima.
Addu’ar yamma: karatu
14Allah kuma ya ce, “Bari haskoki su kasance a sararin sama domin su raba yini da dare, bari su zama alamu domin su nuna yanayi, da ranaku, da kuma shekaru, 15bari kuma haskokin su kasance a sararin sama domin su ba da haske a duniya.” Haka kuwa ya kasance. 16Allah ya yi manyan haskoki biyu, babban hasken yă mallaki yini, ƙaramin kuma yă mallaki dare. Ya kuma yi taurari. 17Allah ya sa su a sararin sama domin su ba da haske a duniya, 18su mallaki yini da kuma dare, su kuma raba haske da duhu. Allah kuwa ya ga yana da kyau. 19Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta huɗu ke nan. 20Allah ya ce, “Bari ruwa yă cika da halittu masu rai, bari tsuntsaye kuma su tashi sama a bisa duniya a sararin sama.” 21Allah ya halicci manyan halittun teku, da kowane mai rai da abin da yake motsi a ruwa, bisa ga irinsu, da kuma kowane tsuntsu mai fiffike bisa ga irinsa. Allah kuwa ya ga yana da kyau. 22Allah ya albarkace su ya ce, “Ku yi ta haihuwa ku kuma ƙaru da yawa, ku cika ruwan tekuna, bari kuma tsuntsaye su yi yawa a bisa duniya.” 23Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta biyar ke nan.
Addu’ar yamma: karatu
20Hikima tana kira da ƙarfi a kan titi, tana ɗaga muryarta a dandalin taron jama’a; 21tana kira da ƙarfi a kan tituna masu surutu, tana yin jawabinta a hanyoyin shiga gari. 22“Har yaushe ku da kuke marasa azanci za ku ci gaba a hanyoyinku marasa azanci? Har yaushe ku masu ba’a za ku yi ta murna cikin ba’arku wawaye kuma ku ƙi ilimi? 23Da a ce kun saurari tsawatata, da na faɗa muku dukan abin da yake zuciyata in kuma sanar da ku tunanina. 24Amma da yake kun ƙi ni sa’ad da na yi kira ba kuma wanda ya saurara sa’ad da na miƙa hannuna, 25da yake kun ƙi dukan shawarata ba ku kuma yarda da tsawatata ba, 26Zan yi muku dariya sa’ad da masifa ta same ku, zan yi muku ba’a sa’ad da bala’i ya same ku, 27sa’ad da bala’i ya sha kanku kamar hadiri, sa’ad da masifa ta share ku kamar guguwa, sa’ad damuwa da wahala suka mamaye ku. 28“Sa’an nan za su kira gare ni amma ba zan amsa ba; za su neme ni amma ba za su same ni ba. 29Da yake sun ƙi sani ba su kuwa zaɓi tsoron Ubangiji ba, 30da yake ba su karɓi shawarata ba suka kuwa yi kunnen ƙashi ga tsawatata, 31za su sami sakayyar abubuwan da suka yi su kuma ƙoshi da sakayyar makircinsu. 32Gama rashin hankalin marasa azanci zai kashe su, rashin kulawar wawaye kuma zai hallaka su; 33amma duk wanda ya saurare ni, zai zauna lafiya yă kuma kasance da rai kwance, ba tare da tsoron lahani ba.”
Kwanakin suna bin kalandar Julian ta Ikilisiyar Rasha (kamar Ikilisiyoyin Serbia da Georgia da Dutsen Athos): Maris 3 a kalandar ikilisiya shi ne Maris 16 a kalandar gari. Ikilisiyoyin da ke amfani da sabuwar kalanda (Girka, Romania, Bulgaria, Ukraine…) suna yin bukukuwan da ba sa canzawa da na tsarkaka a ainihin ranar gari, kwanaki 13 kafin haka, kuma wasu karatunsu sun bambanta; Ista da kwanakin da suka dogara da ita iri ɗaya ne.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi