Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Nuwamba 2026 › Nuwamba 7
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Nuwamba 7, 2026
Asabar · Mako na 31 na lokacin yau da kullum
Bukukuwa da waliyyai
Asabar a mako na 31 na lokacin yau da kullum
Tunawa da ba dole ba · Launin ibada: kore
Tunawa da Budurwa Maryamu Mai Albarka a ranar Asabar · Tunawa da ba dole ba
Karatun yini
Karatu na farko
10Na yi farin ciki sosai ga Ubangiji don yanzu kun sāke nuna kun kula da ni. Ko da yake dā ma kun kula da ni sai dai ba ku sami dama ku nuna mini ba. 11Ba na faɗin haka domin ina cikin bukata, gama na koya yadda zan gamsu a cikin kowane hali. 12Na san mene ne zaman rashi, na kuma san mene ne zaman samu. Zan iya zama cikin kowane hali, ko cikin ƙoshi ko cikin yunwa, ko cikin yalwa ko kuma cikin fatara. 13Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi. 14Duk da haka kun kyauta da kuka yi tarayya da ni cikin wahalolina. 15Ban da haka, kamar yadda ku Filibbiyawa kuka sani, a farkon kwanakin da kuka ji bishara, sa’ad da na tashi daga Makidoniya, babu wata ikkilisiyar da tă yi tarayya da ni a fannin bayarwa da karɓa, sai ku kaɗai; 16gama ko sa’ad da nake a Tessalonika ma, kun aiko mini da taimako sau da sau sa’ad da nake cikin bukata. 17Ba cewa ina neman kyauta ba ne, sai dai ina neman abin da za a ƙara a kan ribarku. 18An biya ni duka, biyan da ya wuce misali. Bukatata ta biya, da yake na karɓi kyautarku da kuka aiko ta hannun Afaforiditus. Baiwa mai ƙanshi, hadaya abar karɓa, mai faranta wa Allah rai. 19Allahna kuma zai biya dukan bukatunku bisa ga ɗaukakar wadatarsa cikin Kiristi Yesu.
Zaburar amsawa
1Yabi Ubangiji. Mai albarka ne mutumin da yake tsoron Ubangiji, wanda yakan sami farin ciki mai girma a umarnansa. 2’Ya’yansa za su zama manya a ƙasar; tsaran masu aikata gaskiya za su sami albarka. 5Abu mai kyau zai zo masa shi da yake kyauta yake kuma ba da bashi hannu sake, shi da yake yin al’amuransa cikin gaskiya. 6Tabbatacce ba zai taɓa jijjigu ba; za a tuna da mai adalci har abada. 8Zuciyarsa tana da kāriya, ba zai ji tsoro ba; a ƙarshe zai zama mai nasara a kan maƙiyansa. 9Ya rarraba kyautansa ga matalauta, adalcinsa zai dawwama har abada; za a ɗaga ƙahonsa sama da bangirma.
Bishara
9Ina gaya muku, ku yi amfani da dukiya na wannan duniya, domin ku sami wa kanku abokai. Saboda bayan dukiyar ta ƙare, za a karɓe ku a wuraren zama da sun dawwama. 10“Duk wanda ana amincewa da shi cikin ƙaramin abu, ana kuma amincewa da shi cikin babba. Kuma duk marar gaskiya cikin ƙaramin abu, zai zama marar gaskiya cikin babba. 11In fa ku ba amintattu ne cikin tafiyar da dukiya ta wannan duniya ba, wa zai amince muku da dukiya ta gaskiya? 12In fa ku ba amintattu ne cikin tafiyar da dukiyar wani ba, wa zai ba ku dukiya naku, na kanku? 13“Babu wani bawa mai iya bauta wa iyayengiji biyu ba. Ko dai ya ƙi ɗaya, ya so ɗayan, ko kuwa ya dāge ga yi wa ɗaya bauta, sa’an nan ya rena ɗayan. Ba za ku iya ku bauta wa Allah tare da bauta wa Mammon (wato, Kuɗi) a lokaci ɗaya ba.” 14Da Farisiyawa masu son kuɗi suka ji wannan duka, sai suka yi wa Yesu tsaki. 15Ya ce musu, “Ku ne masu mai da kanku marasa laifi a gaban mutane, amma Allah ya san zuciyarku. Abu mai daraja a gaban mutane, abin ƙyama ne a gaban Allah.
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi A, shekarar ranakun mako II.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi