Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Oktoba 2026 › Oktoba 18

Kalandar Katolika

Karatun Mass (Katolika) — Oktoba 18, 2026

Lahadi · Mako na 29 na lokacin yau da kullum

Bukukuwa da waliyyai

Lahadi ta 29 ta lokacin yau da kullum

Lahadi · Launin ibada: kore

Karatun yini

Karatu na farko

Ish 45:1, 4–6

1“Ga abin da Ubangiji ya faɗa wa shafaffensa, ga Sairus, wanda hannun damansa yana riƙe da shi don yă ci al’ummai a gabansa ya kuma tuɓe makaman sarakuna, don yă buɗe ƙofofi a gabansa don kada a kulle ƙofofi. 4Saboda sunan Yaƙub bawana, Isra’ila zaɓaɓɓena, na kira ka da suna na ba ka matsayin bangirma, ko da yake ba ka san ni ba. 5Ni ne Ubangiji, kuma babu wani; in ban da ni babu wani Allah. Zan ƙarfafa ka, ko da yake ba ka san ni ba, 6saboda daga fitowar rana har zuwa fāɗuwarta mutane za su san cewa babu wani in ban da ni. Ni ne Ubangiji, kuma babu wani.

Zaburar amsawa

Zab 96:1, 3–5, 7–10

1Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji; ku rera ga Ubangiji, ku duniya duka. 3Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai, manyan ayyukansa a cikin dukan mutane. 4Gama da girma Ubangiji yake, ya kuma cancanci yabo; tilas a ji tsoronsa fiye da dukan alloli. 5Gama dukan allolin al’ummai gumaka ne, amma Ubangiji ne ya yi sammai. 7Ku ba wa Ubangiji, ya iyalan al’ummai ku ba wa Ubangiji ɗaukaka da kuma ƙarfi. 8Ku ba wa Ubangiji ɗaukakar da ta dace da sunansa; ku kawo sadaka ku kuma zo cikin filayen gidansa. 9Ku bauta wa Ubangiji da darajar tsarkinsa; ku yi rawar jiki a gabansa, dukan duniya. 10Ku faɗa cikin al’ummai, “ Ubangiji yana mulki.” Duniya ta kahu daram, ba za a iya matsar da ita ba; zai yi wa mutane hukunci da gaskiya.

Karatu na biyu

1Tes 1:1–5

1Bulus, Sila da Timoti, Zuwa ga ikkilisiyar Tessalonikawa ta Allah Uba da Ubangiji Yesu Kiristi. Alheri da salama su kasance tare da ku. 2Kullum muna gode wa Allah dominku duka, muna ambatonku cikin addu’o’inmu. 3Muna tunawa da aikinku ba fasawa a gaban Allah da Ubanmu ta wurin bangaskiya, da famar da kuke yi domin ƙauna, da kuma begenku marar gushewa ga Ubangijinmu Yesu Kiristi. 4Gama mun sani, ’yan’uwa, ƙaunatattu na Allah, cewa ya zaɓe ku, 5domin bishararmu ba tă zo gare ku da kalmomi kawai ba, amma da iko, da Ruhu Mai Tsarki, da kuma cikakken tabbaci. Kun san irin rayuwar da muka yi a cikinku don amfaninku.

Bishara

Mat 22:15–21

15Sai Farisiyawa suka yi waje, suka ƙulla yadda za su yi masa tarko cikin maganarsa. 16Suka aiki almajiransu tare da mutanen Hiridus wurinsa. Suka ce, “Malam, mun san kai mutum ne mai mutunci, kuma kana koyar da maganar Allah bisa gaskiya. Mutane ba sa ɗaukan hankalinka, domin ba ka kula ko su wane ne ba. 17To, ka gaya mana, a ra’ayinka? Ya dace a biya Kaisar haraji ko a’a?” 18Amma Yesu da yake ya san mugun nufinsu, sai ya ce, “Ku munafukai, don me kuke ƙoƙarin sa mini tarko? 19Ku nuna mini kuɗin da ake biyan haraji da shi.” Sai suka kawo masa dinari, 20sai ya tambaye su ya ce, “Hoton wane ne wannan? Kuma rubutun wane ne?” 21Suka amsa, “Na Kaisar ne.” Sai ya ce musu, “Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba wa Allah abin da yake na Allah.”

Tsarkakan ranar

Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi A, shekarar ranakun mako II.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi