Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Oktoba 2026 › Oktoba 19
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Oktoba 19, 2026
Litinin · Mako na 29 na lokacin yau da kullum
Bukukuwa da waliyyai
Litinin a mako na 29 na lokacin yau da kullum
Tunawa da ba dole ba · Launin ibada: kore
Waliyyi Paul na Gicciye, firist · Tunawa da ba dole ba
Waliyyi John de Brébeuf da Waliyyi Isaac Jogues, firistoci, da abokansu, shahidai · Tunawa da ba dole ba
Karatun yini
Karatu na farko
1Ku kam, a dā ku matattu ne saboda laifofinku da kuma zunubanku. 2Kun yi rayuwa kamar yadda sauran mutanen duniya suke yi, cike da zunubi, kuna biyayya ga sarki masu ikon sarari sama, wato, ruhun nan da yanzu yake aiki a cikin masu ƙin biyayya ga Allah. 3Dukanmu a dā mun yi irin rayuwan nan a cikinsu, muna bin kwaɗayi da sha’awace-sha’awacen jikunanmu da tunaninmu. Kamar sauran mutane, mun cancanci fushin Allah. 4Amma saboda yawan ƙaunar da yake mana, Allah, wanda yake mai yawan jinƙai, 5ya ba mu rai sa’ad da ya tashe Kiristi daga matattu. Ta wurin alherin Allah ne aka cece ku. 6Allah ya tashe mu tare da Kiristi, ya kuma ba mu wurin zama tare da shi a cikin mulkin samaniya. 7Allah ya yi haka domin a tsararraki masu zuwa yă nuna yalwar alherinsa da ya wuce misali, an bayyana alheransa da ya yi mana ta wurin Kiristi Yesu. 8Allah ya cece ku ta wurin alheri sa’ad da kuka ba da gaskiya. Wannan kuwa ba yinku ba ne, kyauta ce daga Allah. 9Ba kuwa saboda aikin lada ba, don kada wani yă ɗaga kai. 10Ai, mu aikinsa ne, an sāke halittarmu a cikin Kiristi Yesu musamman domin mu yi kyawawan ayyuka, waɗanda Allah ya tanadar mana tun da fari, mu yi.
Zaburar amsawa
1Zabura ce. Don yin godiya. Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, dukan duniya. 2Yi wa Ubangiji sujada da murna; ku zo gabansa da waƙoƙin farin ciki. 3Ku san cewa Ubangiji shi ne Allah. Shi ne ya yi mu, mu kuwa nasa ne; mu mutanensa ne, tumakin makiyayarsa. 4Ku shiga ƙofofinsa da godiya filayen gidansa kuma da yabo; ku gode masa ku kuma yabi sunansa. 5Gama Ubangiji yana da kyau kuma ƙaunarsa madawwamiya ce har abada; amincinsa na cin gaba a dukan zamanai.
Bishara
13Sai wani mutum daga cikin taron ya ce masa, “Malam, ka ce wa ɗan’uwana ya raba gādon da ni.” 14Yesu ya amsa masa ya ce, “Kai, wa ya naɗa ni alƙali, ko mai sulhu a tsakaninku?” 15Sai ya ce musu, “Ku lura fa! Ku tsare kanku daga dukan kowane irin kwaɗayi. Ran mutum ba ya danganta a kan yawan dukiyarsa ba.” 16Sai ya gaya musu wannan misali ya ce, “Gonar wani mai arziki ta ba da amfani sosai. 17Ya yi tunani a ransa ya ce, ‘Ba ni da inda zan ajiye amfanin gonana. Me zan yi ke nan?’ 18“Sai ya ce, ‘Ga abin da zan yi. Zan rushe rumbunana, in gina manya, in zuba dukan hatsina da kayana a ciki. 19Ni kuma zan ce wa raina, “Kana da kaya da yawa masu kyau, da aka yi ajiyarsu domin shekaru da dama masu zuwa. Yi hutunka, ka ci, ka sha, ka yi annashuwa.” ’ 20“Amma Allah ya ce masa, ‘Kai wawa! A wannan dare za a nemi ranka. Bayan haka, wa zai gāji abin da ka tara wa kanka?’ 21“Haka zai zama ga duk wanda ya tara wa kansa dukiya, amma ba shi da arziki a gaban Allah.”
Tsarkakan ranar
- Waliyyi Paul na Gicciye, firist
- Waliyyi John de Brébeuf da Waliyyi Isaac Jogues, firistoci, da abokansu, shahidai
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi A, shekarar ranakun mako II.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi