Bincika › Sarakuna da Tarihi gefe da gefe › Sarakunan Yahuda
Sarakuna da Tarihi gefe da gefe · Sarakunan Yahuda
Shemahiya ya hana yaƙin
1Sar 12:21–24 · 2Tar 11:1–4
1Sar 12:21–2421Da Rehobowam ya isa Urushalima, ya tattara dukan gidan Yahuda da kabilar Benyamin, ya sami sun kai mayaƙa dubu da tamanin. Sai aka shirya don su yaƙi gidan Isra’ila, su kuma mayar da masarautar wa Rehobowam ɗan Solomon.
22Amma waɗannan kalmomin Allah suka zo wa Shemahiya, mutumin Allah, cewa,
23“Faɗa wa Rehobowam ɗan Solomon, sarkin Yahuda, ka faɗa wa dukan gidan Yahuda da Benyamin, da kuma dukan sauran mutane,
24‘Ga abin da Ubangiji ya ce, “Kada ku haura don ku yi yaƙi da ’yan’uwanku, Isra’ilawa. Ku koma gida, kowannenku, gama wannan aikina ne.” ’ ” Saboda haka suka yi biyayya da maganar Ubangiji, suka sāke watse zuwa gida, yadda Ubangiji ya umarta.
2Tar 11:1–41Sa’ad da Rehobowam ya iso Urushalima, ya tattara mayaƙa dubu ɗari takwas daga gidan Yahuda da Benyamin, don su yi yaƙi da Isra’ila su sāke mai da mulki wa Rehobowam.
2Amma wannan maganar Ubangiji ta zo ga Shemahiya mutumin Allah.
3“Faɗa wa Rehobowam ɗan Solomon sarkin Yahuda da kuma dukan Isra’ilawan da suke a Yahuda da Benyamin,
4‘Ga abin da Ubangiji ya ce kada ku haura don ku yi yaƙi da ’yan’uwanku. Ku tafi gida kowannenku, gama wannan yi na ne.’ ” Saboda haka suka yi biyayya ga maganar Ubangiji suka kuma koma daga takawa don yaƙi da Yerobowam.
An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY