Bible Explorer

Bincika › Sarakuna da Tarihi gefe da gefe › Sarakunan Yahuda

Sarakuna da Tarihi gefe da gefe · Sarakunan Yahuda

Isra’ila suka yi wa Rehobowam tawaye

1Sar 12:1–19 · 2Tar 10:1–19

1 Sarakuna

1Sar 12:1–19

1Rehobowam ya tafi Shekem, gama dukan Isra’ila sun je can don su naɗa shi sarki.

2Sa’ad da Yerobowam ɗan Nebat ya ji labari (gama har yanzu yana a Masar, inda ya gudu daga Sarki Solomon), sai ya dawo daga Masar.

3Saboda haka mutane suka aika Yerobowam yă zo, sai shi da dukan taron Isra’ila suka tafi wurin Rehobowam, suka ce masa,

4“Mahaifinka ya sa mana kaya mai nauyin gaske, amma yanzu ka sassauta wannan aiki mai zafi, da kuma kaya masu nauyin da ya sa a kanmu, mu kuwa za mu bauta maka.”

5Rehobowam ya amsa, “Ku tafi, bayan kwana uku, ku dawo.” Sai mutane suka watse.

6Sai Sarki Rehobowam ya nemi shawarar dattawa waɗanda suka yi wa mahaifinsa Solomon, hidima a kwanakinsa. Ya ce, “Wace shawara ce za ku ba ni don in amsa wa waɗannan mutane?”

7Suka amsa, “In a yau za ka zama bawan waɗannan mutane, ka kuma yi musu hidima, ka ba su amsa mai kyau, kullum za su kasance bayinka.”

8Amma Rehobowam ya ƙi shawarar da dattawan suka ba shi, sai ya nemi shawarar matasa waɗanda suka yi girma tare, waɗanda kuma suke masa hidima.

9Ya tambaye su, “Mece ce shawararku? Yaya za mu amsa wa waɗannan mutane masu cewa, ‘Ka sassauta nauyin da mahaifinka ya sa a kanmu’?”

10Matasan, waɗanda suka yi girma tare da shi, suka amsa, “Faɗa wa waɗannan mutanen da suka ce maka, ‘Mahaifinka ya sa kaya masu nauyi a kanmu, amma ka sassauta kayanka.’ Ka ce musu, ‘Ƙaramin yatsana ya fi ƙugun tsohona kauri.

11Mahaifina ya sa muku kaya masu nauyi; ni zan ma sa su fi haka nauyi. Mahaifina ya hore ku da bulala; ni kuwa zan hore ku da kunamai.’ ”

12Bayan kwana uku, Yerobowam da dukan mutane suka dawo wurin Rehobowam yadda sarki ya faɗa, “Ku dawo gare ni cikin kwana uku.”

13Sai Sarki ya amsa wa mutane da zafi. Yana ƙin shawarar da dattawa suka ba shi.

14Ya bi shawarar matasa, ya ce, “Mahaifina ya sa muku kaya masu nauyi; ni zan ma sa su fi haka nauyi. Mahaifina ya hore ku da bulala; ni kuwa zan hore ku da kunamai.”

15Saboda haka sarki bai saurare mutane ba, gama wannan abin da ya faru daga wurin Ubangiji ne, don a cika maganar Ubangiji da ya yi wa Yerobowam ɗan Nebat ta wurin Ahiya, mutumin Shilo.

16Da dukan Isra’ila suka ga sarki ya ƙi yă saurare su, sai suka amsa wa sarki, “Ina ruwanmu da Dawuda! Ai! Ba mu da gādo wurin ɗan Yesse. Ya Isra’ila, kowa yă koma tentinsa! Dawuda, sai ka lura da gidanka!” Saboda haka Isra’ilawa suka watse zuwa gida.

17Amma ga Isra’ilawan da suke zama a garuruwan Yahuda kuwa, Rehobowam ya ci gaba da mulki a kansu.

18Sarki Rehobowam ya aiki Adoniram wanda yake shugaban aikin gandu, amma Isra’ila suka jajjefe shi da dutse har ya mutu. Sarki Rehobowam, ya sullale ya hau keken yaƙinsa ya tsere zuwa Urushalima.

19Tun daga wannan ranar ne mutanen Isra’ila suka shiga gāba da gidan Dawuda har wa yau.

2 Tarihi

2Tar 10:1–19

1Rehobowam ya tafi Shekem, gama dukan Isra’ilawa sun je can don su naɗa shi sarki.

2Da Yerobowam ɗan Nebat ya ji wannan (a lokacin yana a Masar, inda ya gudu daga Sarki Solomon ya tafi), sai ya dawo daga Masar.

3Saboda haka suka aika a zo da Yerobowam, sai shi da dukan Isra’ila suka je wurin Rehobowam suka ce masa.

4“Mahaifinka ya sa mana kaya masu nauyi a kanmu, amma yanzu ka sauƙaƙa mana aiki mai zafin nan da kuma kaya masu nauyin da ya sa a kanmu, mu kuwa za mu bauta maka.”

5Rehobowam ya amsa, “Ku dawo gare ni cikin kwana uku.” Saboda haka mutanen suka watse.

6Sai Sarki Rehobowam ya nemi shawarar dattawan da suka yi wa mahaifinsa Solomon hidima a lokacin da yake da rai, ya tambaye suya ce, “Wace shawara za ku ba ni don in amsa wa waɗannan mutane?”

7Suka amsa suka ce, “In za ka ji tausayi waɗannan mutane ka kuma gamshe su, ka kuma ba su amsar da ta dace, kullum za su zama bayinka.”

8Amma Rehobowam ya ƙi shawarar da dattawa suka ba shi ya kuma nemi shawarar matasan da suka yi girma tare, suke kuma yin masa hidima.

9Ya tambaye su ya ce, “Mece ce shawararku? Yaya zan amsa wa waɗannan mutanen da suke ce mini, ‘Ka sauƙaƙa nauyin da mahaifinka ya sa a kanmu’?”

10Matasan da suka yi girma tare shi suka amsa, “Faɗa wa mutanen da suke ce maka, ‘Mahaifinka ya sa kaya masu nauyi a kanmu, amma ka sauƙaƙa nauyinmu.’ Ka faɗa musu, ‘Ƙaramin yatsana ya fi ƙugun mahaifina kauri.

11Mahaifina ya sa muku kaya masu nauyi; zan ma sa mafi nauyi. Mahaifina ya bulale ku da bulala; zan bulale ku da kunamai.’ ”

12Bayan kwana uku sai Yerobowam da dukan mutane suka dawo wurin Rehobowam, yadda sarki ya ce, “Ku dawo gare ni cikin kwana uku.”

13Sarki ya amsa musu da kakkausar murya. Ya ƙi shawarar dattawan,

14ya kuma bi shawarar matasan ya ce, “Mahaifina ya sa muku kaya masu nauyi; zan ma sa mafi nauyi. Mahaifina ya bulale ku da bulala; zan bulale ku da kunamai.”

15Saboda haka sarki bai saurari mutane ba, gama wannan juyin al’amura daga Allah ne, don a cika maganar Ubangiji da ya yi ga Yerobowam ɗan Nebat ta wurin Ahiya mutumin Shilo.

16Sa’ad da Isra’ila suka ga sarki ya ƙi yă saurare su, sai suka amsa wa sarki, suka ce, “Wanda rabo muke da shi a wurin Dawuda, wanda sashe muke da shi daga ɗan Yesse? Kowa yă koma tentinsa, ya Isra’ila! Ka lura da gidanka, ya Dawuda!” Saboda haka dukan Isra’ilawa suka tafi gida.

17Amma game da Isra’ilawan da suke zama a garuruwan Yahuda kuwa, Rehobowam ya ci gaba da yin mulki a bisansu.

18Sarki Rehobowam ya aiki Hadoram wanda yake lura da aikin dole, amma Isra’ilawa suka jajjefe shi da duwatsu har ya mutu. Sarki Rehobowam kuwa ya gaggauta ya shiga keken yaƙinsa ya gudu zuwa Urushalima.

19Ta haka Isra’ila ya kasance cikin tawaye a kan gidan Dawuda har yă zuwa wannan rana.

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY