Bincika › Sarakuna da Tarihi gefe da gefe › Shawulu da Dawuda
Sarakuna da Tarihi gefe da gefe · Shawulu da Dawuda
Manyan ma’aikatan Dawuda
2Sam 8:15–18 · 1Tar 18:14–17
2Sam 8:15–1815Dawuda ya yi mulkin dukan ƙasar Isra’ila, yana yin wa dukan jama’arsa shari’ar gaskiya da adalci.
16Yowab ɗan Zeruhiya ya zama shugaban sojoji; Yehoshafat ɗan Ahilud kuwa shi ne marubucin tarihi;
17Zadok ɗan Ahitub da Ahimelek ɗan Abiyatar, su ne firistoci; Serahiya kuma sakatare;
18Benahiya ɗan Yehohiyada ne shugaban Keretawa da Feletiyawa, wato, sojoji masu gadin Dawuda, sa’an nan ’ya’yan Dawuda maza su ne mashawartan sarki.
1Tar 18:14–1714Dawuda ya yi mulki a bisa dukan Isra’ila, yana yin abin da yake daidai da kuma gaskiya saboda dukan mutanensa.
15Yowab ɗan Zeruhiya shi ne shugaban mayaƙa; Yehoshafat ɗan Ahilud shi ne marubuci;
16Zadok ɗan Ahitub da Abimelek ɗan Abiyatar su ne firistoci; Shafsha shi ne magatakarda;
17Benahiya ɗan Yehohiyada shi ne shugaban Keretawa da Feletiyawa; ’ya’yan Dawuda maza su ne manyan ma’aikata a gefen sarki.
An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY