Bible Explorer

Bincika › Littattafan Bishara gefe da gefe › A Galili

Littattafan Bishara gefe da gefe · A Galili

An warkar da mutane da yawa da yamma

Mat 8:16–17 · Mar 1:32–34 · Luk 4:40–41

Mattiyu

Mat 8:16–17

16Da yamma ta yi, aka kawo masa masu aljanu da yawa, ya kuwa fitar da ruhohin ta wurin magana, ya kuma warkar da dukan marasa lafiya.

17Wannan ya faru ne domin a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya cewa, “Ya ɗebi rashin lafiyarmu, ya kuma ɗauki cututtukanmu.”

Markus

Mar 1:32–34

32A wannan yamma, bayan fāɗuwar rana, mutane suka kawo wa Yesu dukan marasa lafiya, da masu aljanu.

33Duk garin ya taru a ƙofar gidan.

34Yesu kuwa ya warkar da marasa lafiya da yawa da suke da cututtuka iri-iri. Ya kuma fitar da aljanu da yawa, amma bai yarda aljanun suka yi magana ba, don sun san wane ne shi.

Luka

Luk 4:40–41

40Rana tana fāɗuwa, sai mutane suka yi ta kawo wa Yesu dukan waɗanda suke da cuta iri-iri, sai ya ɗibiya wa kowannensu hannuwansa, ya warkar da su.

41Bugu da ƙari, aljanu suka fiffita daga cikin mutane da yawa suna ihu suna cewa, “Kai Ɗan Allah ne!” Amma ya kwaɓe su, ya hana su magana, don sun san cewa shi ne Kiristi.

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY