Gida › Shahararrun ayoyin Littafi Mai Tsarki › Romawa 16:17
Ayar Littafi Mai Tsarki · SRK
Romawa 16:17
Ina roƙonku, ’yan’uwa, ku yi hankali fa da masu raba tsakani, saɓanin koyarwar da kuka koya, suna sa tuntuɓe. Ku yi nesa da su.
Karanta dukan babin: Romawa 16
A cikin mahallinsa
14Ku gai da Asinkiritus, Filegon, Hermes, Faturobas, Hermas da kuma ’yan’uwan da suke tare da su.
15Ku gai da Filologus, Yuliya, Nereyus da ’yar’uwarsa, da kuma Olimfas da dukan tsarkakan da suke tare da su.
16Ku gaggai da juna da sumba mai tsarki. Dukan ikkilisiyoyin Kiristi suna gaishe ku.
17Ina roƙonku, ’yan’uwa, ku yi hankali fa da masu raba tsakani, saɓanin koyarwar da kuka koya, suna sa tuntuɓe. Ku yi nesa da su.
18Gama irin waɗannan mutane ba sa bautar Ubangijinmu Kiristi, sai dai cikinsu. Ta wurin yaudara da kuma daɗin baki, suna ruɗin marasa wayo.
19Kowa ya riga ya ji game da biyayyarku, don haka ina cike da farin ciki game da ku; amma ina so ku zama masu hikima game da abin da yake nagari, ku kuma zama marasa laifi ga abin da yake mugu.
20Allah na salama zai tattake Shaiɗan ba da daɗewa ba yă kuma sa shi a ƙarƙashin sawunku. Alherin Ubangijinmu Yesu kuma yă kasance tare da ku.
Da Turanci
Now I urge you, brothers, to watch out for those who create divisions and obstacles that are contrary to the teaching you have learned. Turn away from them.Nassoshi masu alaƙa
Sassan da masu karatu suka fi danganta wa da wannan.
Waɗannan mutanen ne, suke kawo rabe-rabe, masu bin abin da jiki yake so, marasa Ruhu.A cikin sunan Ubangiji Yesu Kiristi, muna muku umarni, ’yan’uwa, da ku kiyaye kanku daga kowane ɗan’uwa mai zaman banza da ba ya rayuwa bisa ga koyarwar da kuka karɓa daga wurinmu.In wani yana koyarwar ƙarya bai kuma yarda da sahihiyar koyarwar Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma koyarwa ta tsoron Allah ba, yana cike da girman kai bai kuma san kome ba. Yana da mugun halin son gardama da muhawwara game da kalmomin da suke kawo kishi, rikici, maganar ƙeta, da mugayen zace-zace da yawan tankiya tsakanin mutane masu mugun hali, waɗanda aka raba su da gaskiya, suke kuma tsammani cewa bin Allah wata hanya ce ta samun kuɗi.suna riƙe da siffofin ibada, amma suna mūsun ikonta. Kada wani abu yă haɗa ka da su.Ku lura kada wani yă ruɗe ku da ilimin banza da wofi. Wannan koyarwa ta mutane ce kawai. Ta fito daga ikokin wannan duniya ne ba daga Kiristi ba.Ka gargaɗe mutumin da yake kawo tsattsaguwa sau ɗaya, ka kuma gargaɗe shi sau na biyu. Bayan haka, kada wani abu yă haɗa ka da shi.Masu ruɗi da yawa, waɗanda ba su yarda da zuwan Yesu Kiristi cikin jiki ba, sun riga sun fito a duniya. Duk irin mutumin nan mai ruɗi ne kuma magabcin Kiristi. Ku lura don kada ku yi hasarar aikin da kuka yi, sai dai ku sami cikakken lada. Duk mutumin da bai tsaya a kan koyarwar Kiristi ba, amma ya yi ƙari a kanta, mutumin nan ba shi da Allah. Amma wanda ya tsaya a kan koyarwar Kiristi, yana da Uban da kuma Ɗan. Duk wanda ya zo wurinku bai kuma kawo koyarwan nan ba, kada ku karɓe shi a gidanku ko ku marabce shi. Duk wanda ya karɓe shi yana tarayya da mugun aikinsa ke nan.In wani bai yi biyayya da umarninmu a wannan wasiƙa ba, sai fa ku lura da shi. Kada ku haɗa kai da shi, don yă ji kunya. Duk da haka kada ku mai da shi abokin gāba, sai dai ku gargaɗe shi a matsayin ɗan’uwa.Tushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi