Gida › Shahararrun ayoyin Littafi Mai Tsarki › Mai Hadishi 3:1–8
Ayar Littafi Mai Tsarki · SRK
Mai Hadishi 3:1–8
1Akwai lokaci domin kowane abu, da kuma lokaci domin kowane aiki a duniya.
2Lokacin haihuwa da lokacin mutuwa, lokacin shuki da lokacin tumɓukewa.
3Lokacin kisa da lokacin warkarwa, lokacin rushewa da lokacin ginawa.
4Lokacin kuka da lokacin dariya, lokacin makoki da lokacin rawa.
5Lokacin warwatsa duwatsu da lokacin tara su, lokacin runguma da lokacin dainawa.
6Lokacin nema, da lokacin fid da zuciya, lokacin ajiyewa da lokacin zubarwa.
7Lokacin yagewa da lokacin ɗinkewa, lokacin yin shiru da lokacin magana.
8Lokacin ƙauna da lokacin ƙiyayya, lokacin yaƙi da lokacin salama.
Karanta dukan babin: Mai Hadishi 3
A cikin mahallinsa
1Akwai lokaci domin kowane abu, da kuma lokaci domin kowane aiki a duniya.
2Lokacin haihuwa da lokacin mutuwa, lokacin shuki da lokacin tumɓukewa.
3Lokacin kisa da lokacin warkarwa, lokacin rushewa da lokacin ginawa.
4Lokacin kuka da lokacin dariya, lokacin makoki da lokacin rawa.
5Lokacin warwatsa duwatsu da lokacin tara su, lokacin runguma da lokacin dainawa.
6Lokacin nema, da lokacin fid da zuciya, lokacin ajiyewa da lokacin zubarwa.
7Lokacin yagewa da lokacin ɗinkewa, lokacin yin shiru da lokacin magana.
8Lokacin ƙauna da lokacin ƙiyayya, lokacin yaƙi da lokacin salama.
9Wace riba ce ma’aikaci yake da ita saboda wahalarsa?
10Na ga nawayar da Allah ya ɗora a kan mutane.
11Ya yi kowane abu da kyau a lokacinsa. Ya kuma sa matuƙa a zukatan mutane, duk da haka sun kāsa gane abin da Allah ya yi daga farko zuwa ƙarshe.
Da Turanci
To everything there is a season, and a time for every purpose under heaven: a time to be born and a time to die, a time to plant and a time to uproot, a time to kill and a time to heal, a time to break down and a time to build, a time to weep and a time to laugh, a time to mourn and a time to dance, a time to cast away stones and a time to gather stones together, a time to embrace and a time to refrain from embracing, a time to search and a time to count as lost, a time to keep and a time to discard, a time to tear and a time to mend, a time to be silent and a time to speak, a time to love and a time to hate, a time for war and a time for peace.Nassoshi masu alaƙa
Sassan da masu karatu suka fi danganta wa da wannan.
Sai na yi tunani a zuciyata, “Allah zai shari’anta masu adalci da masu mugunta, gama za a kasance da lokaci domin kowane aiki, lokaci domin kowane abu.”da safe kuma, ku ce, ‘Yau kam za a yi hadari, gama sararin sama ya yi ja, ya kuma ɓata fuska.’ Kun san yadda za ku fassara yanayin sararin sama, amma ba kwa iya fassarar alamun lokuta.Duk wanda ya yi biyayya da umarninsa ba zai sami lahani ba, zuciya mai hikima kuma zai san lokacin da ya dace da kuma hanyoyin da suka fi. Gama akwai lokaci da hanyoyin da suka dace da yin kowane abu, ko da yake wahalar mutum ta yi masa yawa.Sa’ad da al’amura suke tafiya daidai, ka yi farin ciki, amma sa’ad da suka lalace, ka tuna, Allah ne ya yi wancan shi ne kuma ya yi wannan. Saboda haka, mutum ba zai san wani abu game da nan gabansa ba.Amma Elisha ya ce masa, “Ashe, ba ina tare da kai a ruhu ba sa’ad da mutumin ya sauko daga keken yaƙinsa ya tarye ka. Kana gani wannan lokaci ne da za a karɓi kuɗi, da riguna, da gonar inabi, da tumaki, da bijimai, da bayi maza da mata?Mutum yakan yi farin ciki a ba da amsar da take daidai, kuma ina misali a yi magana a lokacin da ya dace!Cikin wahalarsa ya nemi tagomashin Ubangiji Allahnsa ya kuma ƙasƙantar da kansa sosai a gaban Allah na kakanninsa.Na yi ƙoƙari in sa raina yă yi farin ciki da ruwan inabi, in kuma rungumi wauta, hankalina kuma yana yin mini jagora da hikima. Na so in ga abin da yake da daraja ga mutane a duniya a ’yan kwanakinsu.Tushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi