Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Disamba 2027 › Disamba 16

Kalandar Katolika

Karatun Mass (Katolika) — Disamba 16, 2027

Alhamis · Mako na 3 na lokacin Zuwan Ubangiji

Bukukuwa da waliyyai

Alhamis a mako na 3 na lokacin Zuwan Ubangiji

Ranar mako · Launin ibada: shunayya

Karatun yini

Karatu na farko

Ish 54:1–10

1“Ki rera, ya ke bakararriya, ke da ba ki taɓa haihuwa ba; ki ɓarke da waƙa, ki yi sowa don farin ciki, ke da ba ki taɓa naƙuda ba; domin ’ya’yan mace mai kaɗaici sun fi na mai miji yawa,” in ji Ubangiji. 2“Ki fadada wurin tentinki, ki miƙe labulen tentinki da fāɗi, kada ki janye; ƙara tsawon igiyoyinta, ki kuma ƙara ƙarfin turakunta. 3Gama za ki fadada zuwa dama da hagu; zuriyarki za su kori al’ummai su kuma zauna a kufan biranensu. 4“Kada ki ji tsoro; ba za ki sha kunya ba. Kada ki ji tsoron wulaƙanci, ba za a ƙasƙantar da ke ba. Za ki manta da kunyar ƙuruciyarki ba kuwa za ki tuna da zargin zaman gwauruwarki ba. 5Gama Mahaliccinki shi ne mijinki, Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa, Mai Tsarkin nan na Isra’ila ne Mai Fansarki; ana ce da shi Allahn dukan duniya. 6Ubangiji zai kira sai ka ce ke mace ce da aka yashe ta tana kuma damuwa a ranta, macen da ta yi aure a ƙuruciya, sai kawai aka ƙi ta,” in ji Allahnki. 7“Gama a ɗan ƙanƙanen lokaci na rabu da ke, amma da ƙauna mai zurfi zan sāke dawo da ke. 8Cikin fushi mai zafi na ɓoye fuskata daga gare ki na ɗan lokaci, amma da madawwamin alheri zan ji tausayinki,” in ji Ubangiji Mai Fansarki. 9“A gare ni wannan ya yi kamar kwanakin Nuhu, sa’ad da na rantse cewa ruwan Nuhu ba za su ƙara rufe duniya ba. Yanzu fa na rantse ba zan yi fushi da ke ba, ba zan ƙara tsawata miki kuma ba. 10Ko da duwatsu za su girgiza a kuma tumɓuke tuddai, duk da haka madawwamiyar ƙaunata da nake yi miki ba za tă jijjigu ba ba kuwa za a kawar da alkawarin salamata ba,” in ji Ubangiji, wanda ya ji tausayinki.

Zaburar amsawa

Zab 30:1, 3–5, 10–12

1Zabura ce. Wata waƙa. Don keɓewar haikali. Ta Dawuda. Zan girmama ka Ya Ubangiji, gama ka tsamo ni daga zurfafa ba ka bar abokan gābana sun yi farin ciki a kaina ba. 3Ya Ubangiji, ka dawo da ni daga kabari; ka kiyaye ni daga gangarawa zuwa cikin rami. 4Ku rera ga Ubangiji, ku tsarkakansa; ku yabi sunansa mai tsarki. 5Gama fushinsa na ɗan lokaci ne amma alherinsa har matuƙa ne; mai yiwuwa a yi kuka da dare amma farin ciki kan zo da safe. 10Ka ji, ya Ubangiji, ka kuwa yi mini jinƙai; Ya Ubangiji, ka zama taimakona.” 11Ka mai da kukata ta zama rawa; ka tuɓe rigar makokina ka sa mini na farin ciki, 12don zuciyata za tă iya rera gare ka ba kuwa za tă yi shiru ba. Ya Ubangiji Allahna, zan yi maka godiya har abada.

Bishara

Luk 7:24–30

24Bayan almajiran Yohanna suka tafi, sai Yesu ya fara yi wa taron magana game da Yohanna ya ce, “Me kuka je kallo a hamada? Ciyawar da iska take kaɗawa ne? 25In ba haka ba, to, me kuka je kallo? Mutum mai sanye da tufafi masu kyau ne? A’a, masu sa kayan tsada da suke cikin annashuwa, ai, a fada suke. 26Amma me kuka je kallo? Annabi? I, ina kuma faɗa muku, ya ma fi annabi. 27Wannan shi ne wanda aka rubuta game da shi cewa, “ ‘Zan aiko da ɗan saƙona yă sha gabanka, wanda zai shirya hanya, a gabanka.’ 28Ina faɗa muku, a cikin duk waɗanda mata suka haifa, ba wanda ya fi Yohanna girma. Duk da haka wanda ya fi ƙasƙanta a Mulkin Allah ya fi shi.” 29(Dukan mutane, har da masu karɓar haraji, da suka ji kalmomin Yesu, sai suka yarda cewa hanyar Allah gaskiya ce, domin Yohanna ne ya yi musu baftisma. 30Amma Farisiyawa da masanan dokoki, suka ƙi nufin Allah game da su, domin Yohanna bai yi musu baftisma ba.)

Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi C, shekarar ranakun mako II.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi