Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Oktoba 2027 › Oktoba 3

Kalandar Ortodoks · 20 ga Satumba (tsohon lissafi)

Karatun Orthodox na ranar — Oktoba 3, 2027

Lahadi · Sauti na 6

Bukukuwa da waliyyai

Lahadi ta 15 bayan Fentekos

Lahadi bayan Ɗaukaka Gicciye

Azumi

Babu azumi

Wannan yana bin dokar gidan zuhudu. A cikin ikkilisiya, ana tsara gwargwadon azumi tare da mai sauraron furcin zunubi, bisa ga lafiya, shekaru da yanayi.

Karatun yini

Bisharar addu’ar asuba ta 4

Luk 24:1–12

1Da sassafe a ranar farko ta mako, matan suka je kabarin, da kayan ƙanshin da suka shirya. 2Suka iske an riga an gungurar da dutsen daga bakin kabarin. 3Amma da suka shiga ciki, ba su iske jikin Ubangiji Yesu ba. 4Yayinda suna cikin tunani a kan wannan, nan take, ga waɗansu mutum biyu tsaye kusa da su, sanye da kaya masu ƙyalli, kamar walƙiya. 5A cikin tsoro, matan suka fāɗi da fuskokinsu a ƙasa, amma mutanen suka ce musu, “Me ya sa kuke neman mai rai a cikin matattu? 6Ba ya nan, ya tashi! Ku tuna yadda ya gaya muku tun yana tare da ku a Galili cewa, 7‘Dole a ba da Ɗan Mutum ga hannun masu zunubi, a kuma gicciye shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.’ ” 8Sai suka tuna da maganarsa. 9Da suka dawo daga kabarin, sai suka faɗa wa Sha Ɗayan nan da sauransu, dukan waɗannan abubuwa. 10Matan da suka gaya wa manzannin waɗannan abubuwa su ne, Maryamu Magdalin, da Yowanna, da Maryamu uwar Yaƙub, da waɗansu da suke tare da su. 11Amma ba su gaskata matan ba, domin sun ɗauki kalmominsu wani zancen banza ne. 12Duk da haka, Bitrus ya tashi a guje zuwa kabarin. Da ya sunkuya, sai ya ga ƙyallayen lilin kaɗai a kwance. Sai ya koma yana tunani a ransa, a kan abin da ya faru.

Wasiƙa (domin Lahadi bayan Ɗaukaka Gicciye)

Gal 2:16–20

16mun san cewa mutum ba ya samun kuɓuta ta wurin kiyaye Doka, sai dai ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu. Saboda haka, mu ma, muka sa bangaskiyarmu cikin Kiristi Yesu don mu sami kuɓuta ta wurin bangaskiya cikin Kiristi ba ta wurin kiyaye Doka ba, domin ba wanda zai kuɓuta ta wurin bin Doka. 17“In kuwa ya zama muna so mu sami zaman marasa laifi a gaban Allah ta wurin dogara ga Kiristi, sa’an nan an same mu mu kanmu ma masu zunubi ne, ashe, ko wannan zai nuna Kiristi yana ƙarfafa zunubi ke nan? A’a, ko kusa! 18In na sāke gina abin da na rushe, na zama mai karyar Doka ke nan. 19“Gama ta wurin Doka na mutu ga Doka saboda in rayu ga Allah. 20An gicciye ni tare da Kiristi. Yanzu ba ni ne nake raye ba, Kiristi ne yake raye a cikina. Rayuwar da nake yi a jiki, ina rayuwa ce ta wurin bangaskiya cikin Ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni ya kuma ba da kansa domina.

Wasiƙa

2Kor 4:6–15

6Domin shi Allah wanda ya ce, “Bari haske yă haskaka daga duhu,” ya sa haskensa ya haskaka a cikin zukatanmu, don yă ba mu hasken sanin ɗaukakar Allah a fuskar Kiristi. 7Amma muna da wannan dukiya a cikin tulunan yumɓu, don a nuna wannan mafificin ikon nan daga Allah ne, ba daga gare mu ba. 8A matse muke a kowane gefe, sai dai ba a gurgunta mu ba. An rikitar da mu, amma ba mu fid da zuciya ba. 9An tsananta mana, amma ba a yashe mu ba, an fyaɗe mu da ƙasa, amma ba a hallaka mu ba. 10Kullum muna ɗauke da mutuwar Yesu a jikinmu, domin ran Yesu yă bayyana a jikinmu. 11Muddin muna a raye, kullum zaman mutuwa muke yi saboda Yesu, don a bayyana ran Yesu ta wurin jikin nan namu mai mutuwa. 12Ta haka, mutuwa tana aiki a cikinmu, ku kuwa rai a cikinku. 13A rubuce yake cewa, “Na gaskata; saboda haka na yi magana.” Da wannan ruhun bangaskiya ne mu ma muka gaskata, saboda haka muke magana. 14Domin mun san cewa shi da ya tā da Ubangiji Yesu daga matattu, zai tashe mu mu ma tare da Kiristi, yă kuma miƙa mu a gabansa tare da ku. 15Duk wannan fa don amfaninku ne, domin alherin nan da yake bazuwa zuwa ga mutane masu yawa, yă zama dalilin godiya mai yawa ga ɗaukakar Allah.

Bishara (domin Lahadi bayan Ɗaukaka Gicciye)

Mar 8:34–9:1

34Sai ya kira taron wurinsa tare da almajiransa ya ce, “Duk wanda zai bi ni, dole yă ƙi kansa, yă ɗauki gicciyensa yă bi ni. 35Domin duk mai son ceton ransa zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni, da kuma bishara, zai same shi. 36Me mutum zai amfana, in ya ribato duniya duka a bakin ransa? 37Ko kuma, me mutum zai bayar a musayar ransa? 38Duk wanda ya ji kunyata, da na kalmomina a wannan zamani na fasikanci da zunubi, Ɗan Mutum ma zai ji kunyarsa lokacin da ya shiga cikin ɗaukakar Ubansa, tare da tsarkakan mala’iku.” 9:1Ya kuma ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, waɗansu da suke tsattsaye a nan ba za su mutu ba, sai sun ga mulkin Allah ya bayyana da iko.”

Bishara

Mat 22:35–46

35Ɗaya daga cikinsu, wani masanin Doka, ya gwada shi da wannan tambaya. 36“Malam, wace doka ce mafi girma a cikin dokoki?” 37Yesu ya amsa ya ce, “ ‘Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka da dukan ranka da kuma dukan hankalinka.’ 38Wannan, ita ce doka ta fari da kuma mafi girma. 39Ta biye kuma kamar ta farkon take. ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’ 40Dukan Doka da Annabawa suna rataya ne a kan waɗannan dokoki biyu.” 41Yayinda Farisiyawa suke a tattare wuri ɗaya, sai Yesu ya tambaye su, 42“Me kuke tsammani game da Kiristi? Ɗan wane ne shi?” Suka amsa suka ce, “Ɗan Dawuda.” 43Ya ce musu, “To, ta yaya Dawuda ya yi magana ta wurin Ruhu Mai Tsarki, ya kira shi ‘Ubangiji’? Gama ya ce, 44“ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna a hannun damana, sai na sa abokan gābanka su zama matashin sawunka.” ’ 45To, in Dawuda ya kira shi ‘Ubangiji,’ yaya zai zama ɗansa?” 46Ba wanda ya iya tanka masa, daga wannan rana kuwa ba wanda ya sāke yin karambanin yin masa wata tambaya.

Kwanakin suna bin kalandar Julian ta Ikilisiyar Rasha (kamar Ikilisiyoyin Serbia da Georgia da Dutsen Athos): Satumba 20 a kalandar ikilisiya shi ne Oktoba 3 a kalandar gari. Ikilisiyoyin da ke amfani da sabuwar kalanda (Girka, Romania, Bulgaria, Ukraine…) suna yin bukukuwan da ba sa canzawa da na tsarkaka a ainihin ranar gari, kwanaki 13 kafin haka, kuma wasu karatunsu sun bambanta; Ista da kwanakin da suka dogara da ita iri ɗaya ne.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi