Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Satumba 2027 › Satumba 24

Kalandar Katolika

Karatun Mass (Katolika) — Satumba 24, 2027

Juma’a · Mako na 25 na lokacin yau da kullum

Bukukuwa da waliyyai

Juma’a a mako na 25 na lokacin yau da kullum

Ranar mako · Launin ibada: kore

Azumi da tuba

Ranar tuba

Kowace Juma’a ranar tuba ce; kowace taron bishop-bishop yana tsara yadda ake kiyaye ta: kamewa daga nama ko wani aikin tuba. Azumi ya wajaba daga shekara 18 zuwa 59, kamewa daga shekara 14.

Karatun yini

Karatu na farko

Hag 2:1–9

1a ranar ashirin da ɗaya ga watan bakwai, maganar Ubangiji ta zo ta wurin annabi Haggai cewa, 2“Ka yi magana da Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel wanda yake gwamna a Yahuda, da Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist, da kuma dukan raguwar mutane. Ka tambaye su ka ce, 3‘Wane ne a cikinku ya ragu da ya ga wannan gida a darajarsa ta dā? Yaya yake a gare ku a yanzu? Bai yi kamar a bakin kome ba, ko ba haka ba? 4Amma yanzu ka ƙarfafa, ya Zerubbabel,’ in ji Ubangiji. ‘Ka ƙarfafa, ya Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist. Ku ƙarfafa, dukanku mutanen ƙasar,’ in ji Ubangiji, ‘ku yi aiki. Gama ina tare da ku,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki. 5‘Wannan shi ne alkawarin da na yi da ku a lokacin da kuka fito daga Masar. Ruhuna kuwa yana tare da ku. Kada ku ji tsoro.’ 6“Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ba da jimawa ba zan sāke girgiza sammai da kuma ƙasa, teku da busasshiyar ƙasa. 7Zan girgiza dukan al’ummai, marmarin kowace al’umma kuma zai taso, sa’an nan zan cika gidan nan da ɗaukaka,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki. 8‘Da zinariya da azurfa duka nawa ne,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki. 9‘Ɗaukakar gidan nan na yanzu za tă fi ɗaukakar gidan nan na dā,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki. ‘A wannan wuri kuma zan ba da salama,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.”

Zaburar amsawa

Zab 43:1–4

1Ka nuna ni marar laifi ne, ya Allah, ka kuma nemi hakkina a kan al’ummai marasa sanin Allah. Ka kuɓutar da ni daga masu ruɗu da mugayen mutane. 2Kai ne Allah mafakata. Me ya sa ka ƙi ni? Me zai sa in yi ta yawo ina makoki, a danne a hannun abokin gāba? 3Ka aiko da haskenka da gaskiyarka, bari su bishe ni bari su kawo ni ga dutsenka mai tsarki, zuwa wurin da kake zama. 4Sa’an nan zan tafi bagaden Allah, ga Allah, farin cikina da murnata. Zan yabe ka da garaya, Ya Allah, Allahna.

Bishara

Luk 9:18–22

18Wata rana sa’ad da Yesu yana addu’a a ɓoye, almajiransa kuma suna tare da shi, sai ya tambaye, su ya ce, “Wa, taron mutane ke ce da ni?” 19Suka amsa, suka ce, “Waɗansu suna cewa, Yohanna Mai Baftisma, waɗansu kuma annabi Iliya, har wa yau waɗansu suna cewa, kai ɗaya daga cikin annabawan da ne, da ya tashi da rai.” 20“Amma ku fa, wa, kuke ce da ni?” Bitrus ya amsa ya ce, “Kiristi na Allah.” 21Yesu ya gargaɗe su da ƙarfi, kada su gaya wa kowa wannan magana. 22Ya sāke cewa, “Dole ne Ɗan mutum ya sha wahaloli da yawa, dattawa, da manyan firistoci, da malaman dokoki kuma su ƙi shi, kuma dole a kashe shi, a rana ta uku kuma a tā da shi da rai.”

Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi