Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Satumba 2027 › Satumba 23
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Satumba 23, 2027
Alhamis · Mako na 25 na lokacin yau da kullum
Bukukuwa da waliyyai
Alhamis a mako na 25 na lokacin yau da kullum
Tunawa · Launin ibada: fari
Waliyyi Pio na Pietrelcina (Padre Pio), firist · Tunawa
Karatun yini
Karatu na farko
1A shekara ta biyu ta mulkin Sarki Dariyus, a rana ta fari ga watan shida, maganar Ubangiji ta zo ta wurin annabi Haggai zuwa ga Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel, gwamnan Yahuda, da kuma Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist. 2Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Waɗannan mutane sun ce, ‘Lokaci bai yi ba tukuna da za a gina gidan Ubangiji.’ ” 3Sa’an nan maganar Ubangiji ta zo ta wurin annabi Haggai cewa, 4“Ashe, lokaci ya yi da za ku zauna a ɗakunan da kuka yi da rufin katako, amma haikalin nan yana zaman kufai?” 5To, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Ku lura da al’amuranku. 6Kun shuka da yawa, amma kun girbe kaɗan. Kun ci, amma ba ku ƙoshi ba. Kun sha, amma ba ku kashe ƙishirwa ba. Kun sa tufafi, amma ba ku ji ɗumi ba. Kuna karɓar albashi, ya zama sai ka ce kuna zuba a hudajjen aljihu.” 7Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Ku lura da al’amuranku. 8Ku haura zuwa kan duwatsu ku sauko da katakai don ku gina gidan, don ni ma in ji daɗinsa, in kuma sami ɗaukaka,” in ji Ubangiji.
Zaburar amsawa
1Yabi Ubangiji. Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji, yabonsa a cikin taron tsarkaka. 2Bari Isra’ila su yi farin ciki da Mahaliccinsu; bari mutanen Sihiyona su yi murna da Sarkinsu. 3Bari su yabi sunansa tare da rawa suna kuma yin kiɗi gare shi da ganga da garaya. 4Gama Ubangiji yana jin daɗin mutanensa; yakan darjanta masu sauƙinkai da ceto. 5Bari tsarkaka su yi farin ciki a wannan bangirma su kuma rera don farin ciki a kan gadajensu. 6Bari yabon Allah yă kasance a bakunansu takobi mai kaifi kuma a hannuwansu, 9don su yi hukuncin da aka rubuta a kansu. Wannan ne ɗaukakar dukan tsarkakansa. Yabi Ubangiji.
Bishara
7Yanzu fa, Hiridus mai sarauta ya ji labarin dukan abubuwan da suke faruwa. Sai ya rikice, don waɗansu mutane suna cewa, Yohanna Mai Baftisma ne ya tashi daga matattu, 8waɗansu kuma suna cewa, annabi Iliya ne ya sāke bayyana. Waɗansu kuma har wa yau, suna cewa, ɗaya daga cikin annabawa na dā ne, ya tashi. 9Amma Hiridus ya ce, “Yohanna dai na yanke kansa, amma wanne mutum ne nake jin labarin abubuwan nan a kansa?” Sai ya yi ƙoƙari ya ga Yesu.
Tsarkakan ranar
- Waliyyi Pio na Pietrelcina (Padre Pio), firist
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi