Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Agusta 2027 › Agusta 13

Kalandar Ortodoks · 31 ga Yuli (tsohon lissafi)

Karatun Orthodox na ranar — Agusta 13, 2027

Juma’a · Mako na 8 bayan Fentekos · Sauti na 6

Bukukuwa da waliyyai

Forefeast of the Procession of the Venerable and Life-Creating Cross of the Lord

Ranar azumi

Azumi: da mai

Wannan yana bin dokar gidan zuhudu. A cikin ikkilisiya, ana tsara gwargwadon azumi tare da mai sauraron furcin zunubi, bisa ga lafiya, shekaru da yanayi.

Karatun yini

Wasiƙa

1Kor 11:8–22

8Gama namiji bai fito daga mace ba, sai dai mace ce ta fito daga namiji. 9Ba a kuma halicci namiji don mace ba, sai dai mace don namiji. 10Don haka, saboda wannan, da kuma saboda mala’iku, dole mace ta ɗaura wani abu a kanta. 11Duk da haka a cikin Ubangiji, mace ba a rabe take da namiji ba, namiji kuma ba a rabe yake da mace ba. 12Kamar yadda mace ta fito daga namiji, haka kuma aka haifi namiji ta wurin mace. Sai dai kowane abu daga Allah yake. 13Ku kanku duba mana. Ya yi kyau mace tă yi addu’a ga Allah da kanta a buɗe? 14Kai, yadda halitta take ma, ai, ta koya muku cewa in namiji yana da dogon gashi, abin kunya ne a gare shi, 15amma in mace tana da dogon gashi, ai, daraja ce a gare ta. Gama an ba ta dogon gashi saboda rufe kanta ne. 16In akwai mai gardama da wannan, to, mu dai ba mu da wata al’ada, haka ma ikkilisiyoyin Allah. 17Game da umarnan nan dai, ban yaba muku ba, domin taruwarku ba ta kirki ba ce, ɓarna ce. 18Da farko dai, na ji cewa sa’ad da kuka taru a matsayin ikkilisiya, akwai tsattsaguwa a tsakaninku, har na fara yarda da zancen. 19Ba shakka dole a sami bambanci a tsakaninku don a nuna wa Allah ya amince da shi a cikinku. 20Sa’ad da kuka taru, ba Cimar Ubangiji kuke ci ba, 21gama yayinda kuke ci, kowa yakan ci gaba ba tare da jiran wani ba. Wani yă zauna da yunwa, wani kuma yă bugu. 22Kai, ba ku da gidajen da za ku ci ku sha ne? Ko dai kun rena ikkilisiyar Allah ne, kuna kuma wulaƙanta waɗanda ba su da kome? Me zan ce muku? In yabe ku ne game da wannan? A’a, ko kaɗan!

Wasiƙa (domin Asabar)

Rom 13:1–10

1Dole kowa yă yi biyayya ga masu mulki, gama babu wani iko sai ko in Allah ya yarda. Duk hukumomin da muke su, naɗin Allah ne. 2Saboda haka, duk wanda ya yi tawaye ga hukuma yana yin tawaye da abin da Allah ya naɗa ne, waɗanda kuwa suke aikata haka, za su jawo wa kansu hukunci. 3Gama masu mulki ba abin tsoro ba ne ga waɗanda suke yin abin da yake daidai, sai dai ga waɗanda suke aikata laifi. Kana so ka rabu da jin tsoron wanda yake mulki? To, sai ka aikata abin da yake daidai, zai kuwa yabe ka. 4Gama shi bawan Allah ne don kyautata rayuwarka. Amma in ka aikata mugunta, to, sai ka ji tsoro, don ba a banza ne shugaba yake ɗaukan takobinsa ba. Shi fa bawan Allah ne, ta wurinsa ne fushin Allah yakan hukunta masu laifi. 5Saboda haka, dole a yi biyayya ga hukumomi, ba don gudun horo kawai ba amma don lamirinku. 6Shi ne ma ya sa kuke biyan haraji, gama hukumomin nan bayin Allah ne, waɗanda suke ba da dukan lokacinsu don aikin shugabanci. 7Ku ba wa kowa hakkinsa. In kuna da bashin haraji, sai ku biya; in kuɗin shiga ne, ku biya kuɗin shiga; in ladabi ne, ku yi ladabi; in kuma girmamawa ne, ku ba da girma. 8Kada hakkin kowa yă zauna a kanku, sai dai na ƙaunar juna, don mai ƙaunar maƙwabcinsa ya cika Doka ke nan. 9Umarnan nan, “Kada ka yi zina.” “Kada ka yi kisankai.” “Kada ka yi sata.” “Kada kuma ka yi ƙyashi.” Da dai duk sauran umarnai an ƙunshe su ne a wannan kalma “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.” 10Ƙauna ba ta cutar da maƙwabci. Saboda haka ƙauna cika Doka ce.

Bishara

Mat 17:10–18

10Almajiran suka tambaye shi suka ce, “To, me ya sa malaman dokoki suke cewa, dole sai Iliya ya fara zuwa?” 11Yesu ya amsa ya ce, “Tabbatacce, Iliya zai zo, zai kuma gyara dukan abubuwa. 12Amma ina faɗa muku, Iliya ya riga ya zo, ba su kuwa gane shi ba, amma suka yi masa duk abin da suka ga dama. Haka ma Ɗan Mutum zai sha wahala a hannunsu.” 13Sa’an nan almajiran suka gane cewa yana musu zancen Yohanna Mai Baftisma ne. 14Da suka isa wajen taron, sai wani mutum ya zo ya durƙusa a gabansa. 15Ya ce, “Ubangiji, ka yi wa ɗana jinƙai. Yana da farfaɗiya yana kuma shan wahala ƙwarai. Ya sha fāɗuwa cikin wuta ko ruwa. 16Na kuma kawo shi wurin almajiranka, amma ba su iya warkar da shi ba.” 17Yesu ya amsa ya ce, “Ya ku zamani marasa bangaskiya da kuma masu taurinkai, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe kuma zan yi haƙuri da ku? Kawo mini yaron a nan.” 18Yesu ya tsawata wa aljanin, ya kuwa rabu da yaron, nan take yaron ya warke.

Bishara (domin Asabar)

Mat 12:30–37

30“Wanda ba ya tare da ni, yana gāba da ni ne, kuma wanda ba ya taya ni tarawa, watsarwa yake yi. 31Saboda haka ina gaya muku, za a gafarta wa mutane kowane zunubi da kuma saɓo, amma saɓo game da Ruhu, ba za a gafarta ba. 32Duk wanda ya zargi Ɗan Mutum, za a gafarta masa, amma duk wanda ya zargi Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba, ko a wannan zamani ko a zamani mai zuwa. 33“Itace mai kyau, yakan ba da ’ya’ya masu kyau. Itace marar kyau kuma, yakan ba da ’ya’ya marasa kyau. Itace dai, da irin ’ya’yansa ne ake gane shi. 34Ku macizai, ta yaya ku da kuke mugaye za ku iya magana kirki? Gama daga baki, mutum yakan faɗi abin da yake cikin zuciya. 35Mutumin kirki yakan fito da abubuwa masu kyau daga ajiyar da aka a yi cikinsa, mugun mutum kuwa yakan fito da mugayen abubuwa daga cikin muguntar da aka yi ajiya a cikinsa. 36Amma ina gaya muku cewa mutane za su ba da lissafi a ranar shari’a a kan kowace kalmar banza da suka faɗa. 37Gama ta wurin kalmominka za a kuɓutar da kai, kuma ta wurin kalmominka za a hukunta ka.”

Kwanakin suna bin kalandar Julian ta Ikilisiyar Rasha (kamar Ikilisiyoyin Serbia da Georgia da Dutsen Athos): Yuli 31 a kalandar ikilisiya shi ne Agusta 13 a kalandar gari. Ikilisiyoyin da ke amfani da sabuwar kalanda (Girka, Romania, Bulgaria, Ukraine…) suna yin bukukuwan da ba sa canzawa da na tsarkaka a ainihin ranar gari, kwanaki 13 kafin haka, kuma wasu karatunsu sun bambanta; Ista da kwanakin da suka dogara da ita iri ɗaya ne.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi