Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Yuni 2027 › Yuni 13
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Yuni 13, 2027
Lahadi · Mako na 11 na lokacin yau da kullum
Bukukuwa da waliyyai
Lahadi ta 11 ta lokacin yau da kullum
Lahadi · Launin ibada: kore
Karatun yini
Karatu na farko
22“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ni kaina zan cire toho a kan itacen al’ul da yake can bisa in shuka; zan kuma karya ƙanƙanin reshe daga can bisan tohon in shuka a dutse mai tsayi. 23A ƙwanƙolin dutsen Isra’ila zan shuka shi; zai yi rassa yă ba da ’ya’ya yă kuma zama al’ul mai daraja. Tsuntsaye iri-iri za su yi sheƙa a cikinsa; za su sami mafaka a inuwar rassansa. 24Dukan itatuwan jeji za su san cewa Ni Ubangiji ne mai sa manyan itatuwa su zama ƙanana in kuma sa ƙananan itatuwa su zama manya. Nakan sa ɗanyen itace ya bushe, busasshen itace kuma ya zama ɗanye. “ ‘Ni Ubangiji na faɗa, zan kuma aikata.’ ”
Zaburar amsawa
1Zabura ce. Waƙa ce. Domin ranar Asabbaci. Yana da kyau a yabi Ubangiji a kuma yi kiɗi ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka, 2don a yi shelar ƙaunarka da safe amincinka kuma da dare, 12Adalai za su haɓaka kamar itacen dabino, za su yi girma kama al’ul na Lebanon; 13da aka daddasa a gidan Ubangiji, za su haɓaka a filayen gidan Allahnmu. 14Za su ci gaba da ba da ’ya’ya a tsufansu, za su kasance ɗanye kuma kore shar, 15suna shela cewa, “ Ubangiji adali ne; shi ne Dutsena, kuma babu mugunta a cikinsa.”
Karatu na biyu
6Saboda haka, kullum muna da tabbaci mun kuma san cewa, muddin muna a duniya cikin jikin nan, ana raba mu da Ubangiji. 7Rayuwa bangaskiya muke, ba ta ganin ido ba. 8Ina cewa muna da tabbaci, za mu fi so mu rabu da jikin nan, mu kuma kasance a sama tare da Ubangiji. 9Saboda haka, niyyarmu ita ce, mu gamshe shi, ko muna a duniya cikin jikin nan, ko ba mu nan. 10Gama dole dukanmu mu bayyana a gaban kujerar shari’ar Kiristi, domin kowannenmu yă karɓi ladan aikin da ya yi a wannan jiki, ko mai kyau ne ko marar kyau.
Bishara
26Ya sāke cewa, “Mulkin Allah yana kama da haka. Wani mutum ya yafa iri a gona. 27A kwana a tashi har irin yă tsiro, yă yi girma, bai kuwa santa yadda aka yi ba. 28Ƙasar da kanta takan ba da ƙwaya, da farko takan fid da ƙara, sa’an nan ta fid da kai, sa’an nan kan yă fid da ƙwaya. 29Da ƙwayan ya nuna, sai yă sa lauje yă yanka, domin lokacin girbi ya yi.” 30Ya kuma ce, “Da me za mu kwatanta mulkin Allah, ko kuwa da wane misali za mu bayyana shi? 31Yana kama da ƙwayar mustad, wadda ita ce ƙwaya mafi ƙanƙanta da akan shuka a gona. 32Duk da haka, in aka shuka ƙwayar, sai tă yi girma, tă zama mafi girma a itatuwan lambu. Har itacen yă kasance da manyan rassa, inda tsuntsayen sararin sama sukan iya huta a inuwarsa.” 33Da misalai da yawa irin waɗannan, Yesu ya yi magana da su, daidai yadda za su iya fahimta. 34Ba abin da ya faɗa musu, da ba da misali ba. Amma lokacin da yake shi kaɗai tare da almajiransa, sai yă bayyana kome.
Tsarkakan ranar
- Waliyyi Anthony na Padua, firist kuma malamin Ikkilisiya
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi