Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Mayu 2027 › Mayu 10
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Mayu 10, 2027
Litinin · Mako na 7 na lokacin Ista
Bukukuwa da waliyyai
Litinin a mako na 7 na lokacin Ista
Tunawa da ba dole ba · Launin ibada: fari
Waliyyi John na Avila, firist kuma malamin Ikkilisiya · Tunawa da ba dole ba
Karatun yini
Karatu na farko
1Lokacin da Afollos yake a Korint, Bulus ya bi hanyar da ta ratsa ta Asiya ya zo Afisa. A can ya sadu da waɗansu almajirai, 2sai ya tambaye, su ya ce, “Kun karɓi Ruhu Mai Tsarki sa’ad da kuka gaskata?” Suka amsa suka ce, “A’a, ba mu ma san akwai Ruhu Mai Tsarki ba.” 3Saboda haka Bulus ya yi tambaya ya ce, “To, wace baftisma aka yi muku?” Suka ce, “Baftismar Yohanna.” 4Bulus ya ce, “Ai, baftismar Yohanna, baftisma ce ta tuba. Ya ce wa mutane su gaskata a wani wanda yake zuwa bayansa, wato, Yesu.” 5Da ji wannan, sai aka yi musu baftisma a cikin sunan Ubangiji Yesu. 6Da Bulus ya ɗibiya musu hannuwansa, sai Ruhu Mai Tsarki ya sauka musu, suka kuwa yi magana da harsuna, suka kuma yi annabci. 7Mutane kuwa su wajen mutum goma sha biyu ne. 8Bulus ya shiga majami’a ya yi magana gabagadi a can na watanni uku, yana muhawwara yana kuma rinjayarsu game da mulkin Allah.
Zaburar amsawa
1Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Zabura. Waƙa. Bari Allah yă tashi, bari a watsar da abokan gābansa; bari maƙiyansa su gudu a gabansa. 2Kamar yadda iska take hura hayaƙi, bari yă hura su haka; kamar yadda kaki kan narke a gaban wuta, bari mugaye su hallaka a gaban Allah. 3Amma bari adalai su yi murna su kuma yi farin ciki a gaban Allah; bari su yi murna da farin ciki. 4Rera wa Allah, rera yabo ga sunansa, ku ɗaukaka wanda yake hawa a kan gizagizai; sunansa Ubangiji ne, ku kuma yi farin ciki a gabansa. 5Uba ga marayu, mai kāre gwauraye, shi ne Allah a mazauninsa mai tsarki. 6Allah ya shirya masu kaɗaici a cikin iyalai, ya jagorance ’yan kurkuku da waƙoƙi; amma ’yan tawaye suna zama a ƙasa mai zafin rana.
Bishara
29Sai almajiran Yesu suka ce, “Haba, yanzu ne fa kake magana a sarari ba tare da misalai ba. 30Yanzu mun gane cewa ka san kome ba sai wani ya tambaye ka ba. Wannan ya sa muka gaskata ka fito daga Allah.” 31Yesu ya amsa ya ce, “A ƙarshe kun gaskata! 32Amma lokaci na zuwa, har ma ya yi, da za a warwatsa ku, kowa yă koma gidansa. Za ku bar ni ni kaɗai. Duk da haka ba ni kaɗai ba ne, gama Ubana yana tare da ni. 33“Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin a cikina ku sami salama. A duniyan nan za ku sha wahala. Amma ku yi ƙarfin hali! Na yi nasara a kan duniya.”
Tsarkakan ranar
- Waliyyi John na Avila, firist kuma malamin Ikkilisiya
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi