Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Mayu 2027 › Mayu 9

Kalandar Katolika

Karatun Mass (Katolika) — Mayu 9, 2027

Lahadi · Mako na 7 na lokacin Ista

Bukukuwa da waliyyai

Lahadi ta 7 ta lokacin Ista

Lahadi · Launin ibada: fari

Karatun yini

Karatu na farko

Ayy M 1:15–17, 20–26

15A waɗancan kwanakin Bitrus ya miƙe tsaye cikin ’yan’uwa masu bi (taron da ya yi kusan mutum ɗari da ashirin) 16ya ce, “’Yan’uwana, dole a cika Nassin nan da Ruhu Mai Tsarki ya yi magana tun da daɗewa ta bakin Dawuda game da Yahuda, wanda ya zama jagora ga waɗanda suka kama Yesu 17dā shi ɗaya ne cikinmu, ya kuma yi hidima a cikin aikin nan.” 20Bitrus ya ce, “Gama yana a rubuce a cikin Littafin Zabura cewa, “ ‘Bari wurinsa yă zama babu kowa; kada kowa ya zauna a cikinsa,’ kuma, “ ‘Bari wani ya ɗauki matsayinsa na shugabanci.’ 21Saboda haka dole a zaɓi ɗaya daga cikin mutanen da suke tare da mu duk lokacin da Ubangiji Yesu yake shiga da fita a cikinmu, 22farawa daga baftisma ta Yohanna har zuwa sa’ad da aka ɗauke Yesu daga gare mu. Gama dole ɗaya daga waɗannan ya zama shaidar tashinsa daga matattu tare da mu.” 23Saboda haka suka gabatar da mutane biyu. Yusuf mai suna Barsabbas (da aka kuma sani da Yustus) da kuma Mattiyas. 24Sai suka yi addu’a suka ce, “Ubangiji, ka san zuciyar kowa. Nuna mana wanne a cikin waɗannan biyu da ka zaɓa 25ya karɓi wannan aikin manzanci, wanda Yahuda ya bari don yă tafi wurin da yake nasa.” 26Sa’an nan suka jefa ƙuri’u, ƙuri’ar kuwa ta fāɗo a kan Mattiyas; sai aka sa shi cikin manzannin nan goma sha ɗaya.

Zaburar amsawa

Zab 103:1–2, 11–12, 19–20

1Ta Dawuda. Yabi Ubangiji, ya raina; dukan abin da yake cikin cikina, yabi sunansa mai tsarki. 2Yabi Ubangiji, ya raina, kada kuma ka manta dukan alheransa, 11Gama kamar yadda sammai suke can bisa duniya, haka girmar ƙaunarsa yake wa masu tsoronsa; 12kamar yadda gabas yake daga yamma, haka ya cire laifofinmu daga gare mu. 19Ubangiji ya kafa kursiyinsa a sama, masarautarsa kuwa na mulki a bisa duka. 20Yabi Ubangiji, ku mala’ikunsa, ku jarumawa masu yi masa aiki, waɗanda suke yin biyayya da maganarsa.

Karatu na biyu

1Yoh 4:11–16

11Abokaina ƙaunatattu, da yake Allah ya ƙaunace mu haka, ya kamata mu ma mu ƙaunaci juna. 12Ba wanda ya taɓa ganin Allah; amma in muna ƙaunar juna, Allah yana raye a cikinmu, ƙaunarsa kuwa ta zama cikakkiya a cikinmu ke nan. 13Mun san cewa muna rayuwa a cikinsa shi kuma a cikinmu, domin ya ba mu Ruhunsa. 14Mun gani, mun kuma shaida cewa Uba ya aiko Ɗansa domin yă zama Mai Ceton duniya. 15Duk wanda ya yarda cewa Yesu Ɗan Allah ne, Allah yana raye a cikinsa, shi kuma a cikin Allah. 16Ta haka muka sani, muke kuma dogara ga ƙaunar da Allah yake mana. Allah ƙauna ne. Duk wanda yake rayuwa cikin ƙauna, yana rayuwa a cikin Allah ne, Allah kuma a cikinsa.

Bishara

Yoh 17:11–19

11Ba sauran zamana a duniya, amma waɗannan a duniya suke, ni kuwa ina zuwa wurinka. Ya Uba Mai Tsarki, ka kiyaye su ta wurin ikon sunanka, sunan da ka ba ni, don su zama ɗaya kamar yadda muke ɗaya. 12Yayinda nake tare da su, na kāre su na kuma kiyaye su ta wurin sunan nan da ka ba ni. Ba ko ɗayan da ya ɓace, sai dai wannan da aka ƙaddara zuwa ga hallaka don Nassi yă cika. 13“Yanzu ina zuwa wurinka, sai dai na faɗi waɗannan abubuwa ne tun ina a duniya domin farin ciki yă zama cikakke a cikinsu. 14Na gaya musu maganarka duniya kuwa ta ƙi su, don su ba na duniya ba ne yadda ni ma ba na duniya ba ne. 15Ba addu’ata ba ce ka ɗauke su daga duniya ba, sai dai ka kāre su daga mugun nan. 16Su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ma ba na duniya ba ne. 17Ka tsarkake su ta wurin gaskiya; maganarka ce gaskiya. 18Kamar yadda ka aiko ni cikin duniya, haka ni ma na aike su cikin duniya. 19Saboda su ne na tsarkake kaina, domin su ma a tsarkake su da gaske.

Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi