Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Afirilu 2027 › Afirilu 30
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Afirilu 30, 2027
Juma’a · Mako na 5 na lokacin Ista
Bukukuwa da waliyyai
Juma’a a mako na 5 na lokacin Ista
Tunawa da ba dole ba · Launin ibada: fari
Waliyyi Pius na V, Fafaroma · Tunawa da ba dole ba
Azumi da tuba
Ranar tuba
Kowace Juma’a ranar tuba ce; kowace taron bishop-bishop yana tsara yadda ake kiyaye ta: kamewa daga nama ko wani aikin tuba. Azumi ya wajaba daga shekara 18 zuwa 59, kamewa daga shekara 14.
Karatun yini
Karatu na farko
22Sai manzanni da dattawa, tare da dukan ikkilisiya, suka yanke shawara su zaɓi waɗansu daga cikin mutanensu su kuma aike su zuwa Antiyok tare da Bulus da Barnabas. Sai suka zaɓi Yahuda (wanda ake kira Barsabbas) da kuma Sila, mutum biyu da suke shugabanni cikin ’yan’uwa. 23Tare da su suka aika da wannan wasiƙa. Daga manzanni da dattawa, ’yan’uwanku. Zuwa ga Al’ummai masu bi a Antiyok, Suriya da Silisiya. Gaisuwa. 24Mun ji cewa, waɗansu da sun fita daga cikinmu ba tare da izininmu ba suka kuma dame ku, suna tā da hankalinku ta wurin abin da suka ce. 25Saboda haka dukanmu mun yarda mu zaɓi waɗansu mutane mu kuma aike su wurinku tare da ƙaunatattun abokanmu Barnabas da Bulus 26mutanen da suka sa rayukansu cikin hatsari saboda sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi. 27Saboda haka muna aika Yahuda da Sila don su tabbatar muku da baki abin da muka rubuta. 28Ya gamshe Ruhu Mai Tsarki da mu ma kada a ɗora muku nauyi fiye da na waɗannan abubuwa. 29Ku guji abincin da aka yi wa alloli hadaya, da jini, da naman dabbar da aka murɗe da kuma fasikanci. Za ku kyauta in kun kiyaye waɗannan abubuwa. Ku huta lafiya. 30Aka sallami mutanen sai suka gangara zuwa Antiyok, inda suka tara ikkilisiya wuri ɗaya suka ba da wasiƙar. 31Mutanen suka karantata suka kuma yi farin ciki saboda saƙonta mai ƙarfafawa.
Zaburar amsawa
7Zuciyata tana nan daram, ya Allah, zuciyata tana nan daram; zan rera in kuma yi kaɗe-kaɗe. 8Ka farka, raina! Ku farka, garaya da molo! Zan sa safe yă farka. 9Zan yabe ka, ya Ubangiji, a cikin al’ummai; zan rera game da kai a cikin mutane. 10Gama ƙaunarka mai girma ce, tana kaiwa sammai; amincinka na kaiwa sarari. 11Bari a ɗaukaka ka, ya Allah, bisa sammai; bari ɗaukakarka ta kasance a dukan duniya.
Bishara
12Umarnina shi ne, Ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku. 13Babu ƙaunar da ta fi wannan, a ce mutum ya ba da ransa saboda abokansa. 14Ku abokaina ne, in kun yi abin da na umarta. 15Ba zan ƙara ce da ku bayi ba, don bawa bai san abin da maigidansa yake yi ba. A maimako in ce da ku abokai, domin na sanar da ku duk abin da na ji daga wurin Ubana. 16Ba ku kuka zaɓe ni ba, a’a, ni ne na zaɓe ku na kuma naɗa ku ku je ku ba da ’ya’ya-’ya’yan da za su dawwama. Uba kuwa zai ba ku duk abin da kuka roƙa cikin sunana. 17Umarnina ke nan. Ku ƙaunaci juna.
Tsarkakan ranar
- Waliyyi Pius na V, Fafaroma
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi