Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Afirilu 2027 › Afirilu 19
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Afirilu 19, 2027
Litinin · Mako na 4 na lokacin Ista
Bukukuwa da waliyyai
Litinin a mako na 4 na lokacin Ista
Ranar mako · Launin ibada: fari
Karatun yini
Karatu na farko
1Manzanni da ’yan’uwa ko’ina a Yahudiya suka ji cewa Al’ummai ma sun karɓi maganar Allah. 2Saboda haka sa’ad da Bitrus ya haura zuwa Urushalima, masu bin da suke da kaciya suka zarge shi 3suka ce, “Ka je gidan mutanen da suke marasa kaciya ka kuwa ci tare da su.” 4Bitrus ya fara yin musu bayani dalla-dalla yadda ya faru cewa, 5“Ina a birnin Yoffa ina addu’a, sai ga wahayi ya zo mini. Na ga ana sauko da wani abu kamar babban mayafi daga sama ta kusurwansa huɗu, ya kuma sauko inda nake. 6Na duba cikinsa na ga dabbobi masu ƙafa huɗu na duniya, da namun jeji, da masu ja da ciki, da kuma tsuntsayen sararin sama. 7Sa’an nan na ji wata murya tana ce mini, ‘Bitrus, ka tashi. Ka yanka ka ci.’ 8“Na amsa na ce, ‘Sam, Ubangiji! Ban taɓa cin wani abu marar tsarki ko marar tsabta ba.’ 9“Sai muryar daga sama ta yi magana sau na biyu, ta ce, ‘Kada ka ce da abin da Allah ya tsarkake marar tsarki.’ 10Wannan ya faru har sau uku, sa’an nan duk aka sāke ɗauke shi zuwa sama. 11“Nan take sai ga mutum uku da aka aika wurina daga Kaisariya a tsaye a ƙofar gidan da nake. 12Ruhu ya ce mini kada in yi wata-wata game da tafiya tare da su. Waɗannan ’yan’uwa guda shida su ma suka rako ni, muka kuwa shiga gidan mutumin. 13Ya kuma gaya mana yadda wani mala’ika ya bayyana a gidansa ya ce masa, ‘Ka aika zuwa Yoffa a kira Siman wanda ake ce da shi Bitrus. 14Zai kawo maka saƙo wanda ta wurinsa kai da dukan iyalinka za ku sami ceto.’ 15“Na fara magana ke nan, sai Ruhu Mai Tsarki ya sauko musu yadda ya sauko mana a farko. 16Sa’an nan na tuna da abin da Ubangiji ya ce, ‘Yohanna ya yi baftisma da ruwa, amma za a yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki.’ 17To, in Allah ya ba su kyauta yadda ya ba mu, mu da muka gaskata da Ubangiji Yesu Kiristi, wane ni da zan yi hamayya da Allah?” 18Sa’ad da suka ji haka, ba su ƙara yin faɗa ba, suka kuma ɗaukaka Allah, suna cewa, “To, fa, har Al’ummai ma Allah ya sa suka tuba zuwa rai.”
Zaburar amsawa
1Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Maskil ne na ’Ya’yan Kora maza. Kamar yadda barewa take marmarin ruwan rafuffuka, haka raina yake marmarinka, ya Allah. 2Raina yana ƙishin Allah, Allah mai rai. Yaushe zan tafi in sadu da Allah ne? 43:3Ka aiko da haskenka da gaskiyarka, bari su bishe ni bari su kawo ni ga dutsenka mai tsarki, zuwa wurin da kake zama. 4Sa’an nan zan tafi bagaden Allah, ga Allah, farin cikina da murnata. Zan yabe ka da garaya, Ya Allah, Allahna.
Bishara
1“Gaskiya nake gaya muku, mutumin da bai shiga inda ake ajiye garken tumaki ta ƙofa ba, amma ya hau ta katanga, ɓarawo ne, ɗan fashi kuma. 2Mutumin da ya shiga ta ƙofa makiyayin tumakinsa ne. 3Mai gadin yakan buɗe wa makiyayin ƙofa, tumakin kuma sukan saurari muryarsa. Yakan kira tumakinsa da suna, yă kuma fid da su waje. 4Sa’ad da ya fitar da dukan nasa waje, sai ya ja gabansu, tumakinsa kuma sukan bi shi domin sun san muryarsa. 5Amma ba za su taɓa bin baƙo ba; sai dai ma su guje masa don ba su san muryar baƙo ba.” 6Yesu ya yi musu wannan misali, amma ba su fahimci abin da yake faɗa musu ba. 7Saboda haka Yesu ya sāke cewa, “Gaskiya nake gaya muku, ni ne ƙofar tumakin. 8Duk waɗanda suka riga ni zuwa ɓarayi ne, ’yan fashi kuma, amma tumakin ba su saurare su ba. 9Ni ne ƙofar; duk wanda ya shiga ta wurina zai sami ceto. Zai riƙa shiga yă fita yă kuwa sami wurin kiwo. 10Ɓarawo yakan zo don yă yi sata ne kawai da kisa da kuma ɓarna. Ni kuwa na zo ne don su sami rai, su kuma same shi a yalwace.
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi