Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Maris 2027 › Maris 31

Kalandar Katolika

Karatun Mass (Katolika) — Maris 31, 2027

Laraba · Kwana takwas na Ista

Bukukuwa da waliyyai

Laraba a cikin kwana takwas na Ista

Babban biki · Launin ibada: fari

Karatun yini

Karatu na farko

Ayy M 3:1–10

1Wata rana, Bitrus da Yohanna suna haurawa zuwa haikali a lokacin addu’a da ƙarfe uku na rana. 2To, sai ga wani da aka haifa gurgu ana ɗauke da shi zuwa ƙofar haikalin da ake kira Kyakkyawa, inda akan ajiye kowace rana, don yă yi bara daga masu shigowa cikin filayen haikali. 3Da ya ga Bitrus da Yohanna suna gab da shiga, sai ya roƙe su kuɗi. 4Bitrus kuwa ya kafa masa ido, haka ma Yohanna. Sai Bitrus ya ce, “Dube mu!” 5Saboda haka mutumin ya mai da hankalinsa a kansu, yana fata samun wani abu daga gare su. 6Sai Bitrus ya ce, “Azurfa ko zinariya ba ni da su, amma abin da nake da shi, shi zan ba ka. A cikin sunan Yesu Kiristi Banazare, ka yi tafiya.” 7Ta wurin kama hannunsa na dama, ya taimake shi ya miƙe, nan take ƙafafu da idon sawun mutumin suka yi ƙarfi. 8Sai ya yi wuf da ƙafafunsa ya fara tafiya. Ya tafi tare da su ya shiga cikin filin haikali yana tafiya yana tsalle, yana kuma yabon Allah. 9Sa’ad da dukan mutane suka gan shi yana tafiya yana yabon Allah, 10sai suka gane cewa shi ne mutumin nan wanda dā yake zama yana bara a bakin ƙofar haikalin da ake kira Kyakkyawa, suka kuwa cika da mamaki da tsoro a kan abin da ya faru gare shi.

Zaburar amsawa

Zab 105:1–4, 6–9

1Ku yi godiya ga Ubangiji, ku kira bisa sunansa; ku sanar a cikin al’ummai abin da ya yi. 2Ku rera gare shi, ku rera yabo gare shi; ku faɗa dukan abubuwan mamakin da ya aikata. 3Ku ɗaukaka a cikin sunansa mai tsarki; bari zukatan waɗanda suke neman Ubangiji su yi farin ciki. 4Ku sa rai ga Ubangiji da kuma ƙarfinsa; ku nemi fuskarsa kullum. 6Ya ku zuriyar Ibrahim bawansa, Ya ku ’ya’yan Yaƙub, zaɓaɓɓensa. 7Shi ne Ubangiji Allahnmu; kuma hukunce-hukuncensa suna a cikin dukan duniya. 8Yana tuna da alkawarinsa har abada, maganar da ya umarta, har tsararraki dubu, 9alkawarin da ya yi da Ibrahim, rantsuwar da ya yi wa Ishaku.

Bishara

Luk 24:13–35

13A wannan rana kuma, biyu daga cikinsu suna tafiya zuwa wani ƙauye, da ake kira Emmawus, da suke kusan mil bakwai daga Urushalima. 14Suna magana da juna a kan dukan abubuwan da suka faru. 15Da suna magana, kuma suna tattauna waɗannan abubuwa da junansu, sai Yesu da kansa ya zo yana tafiya tare da su. 16Amma ba a ba su ikon gane shi ba. 17Sai ya tambaye, su ya ce, “Mene ne kuke tattaunawa da juna a cikin tafiyarku?” Suka tsaya shiru, da damuwa a fuskarsu. 18Ɗaya daga cikinsu, mai suna Kiliyobas, ya tambaye shi ya ce, “Ashe, kai baƙo ne a Urushalima, da ba ka san abubuwan da suka faru a can, a cikin kwanakin nan ba?” 19Sai ya yi tambaya, “Waɗanne abubuwa?” Suka amsa suka ce, “Game da Yesu Banazare. Shi annabi ne, mai iko ne kuma cikin ayyukansa da maganarsa, a gaban Allah da kuma dukan mutane. 20Manyan firistoci da masu mulkinmu sun ba da shi a yi masa hukuncin mutuwa, suka kuwa gicciye shi. 21Amma da, muna sa zuciya cewa, shi ne wanda zai fanshi Isra’ila. Bugu da ƙari kuma yau kwana uku ke nan tun da wannan abin ya faru. 22Har wa yau, waɗansu daga cikin matanmu sun ba mu mamaki. Sun je kabarin da sassafen nan, 23amma ba su sami jikinsa ba. Sun dawo sun faɗa mana cewa, sun ga wahayi na mala’iku, da suka ce yana da rai. 24Sa’an nan, waɗansu abokanmu suka je kabarin, suka kuma tarar da kome kamar yadda matan suka faɗa, amma shi, ba su gan shi ba.” 25Sai ya ce musu, “Ashe, ku marasa azanci ne, masu nauyin zuciyar gaskata, da dukan abin da annabawa suka faɗa! 26Ai, dole Kiristi yă sha waɗannan wahalolin, kafin yă shiga ɗaukakarsa. 27Sai ya fara bayyana musu daga Musa da dukan Annabawa, abin da dukan Nassi ya faɗa a kansa.” 28Da suka yi kusa da ƙauyen da za su, sai Yesu ya yi kamar zai ci gaba. 29Amma suka matsa masa suka ce, “Sauka wurinmu, don dare ya kusa, rana ta kusa fāɗuwa.” Sai ya sauka wurinsu. 30Da ya zauna a tebur tare da su, sai ya ɗauki burodi, ya yi godiya, ya kakkarya ya fara ba su. 31Sa’an nan idanunsu suka buɗe, suka gane shi. Sai ya ɓace musu. 32Suka tambayi juna, “Ashe, shi ya sa zukatanmu suka kuna a cikinmu, sa’ad da yake magana da mu a hanya, yana bayyana mana Nassi.” 33Suka tashi nan da nan suka koma Urushalima. A can suka sami Sha Ɗayan nan da waɗanda suke tare da su a wuri ɗaya, 34suna cewa, “Gaskiya ne! Ubangiji ya tashi, ya kuma bayyana ga Siman” 35Sai su biyun nan suka ba da labarin abin da ya faru a hanya, da kuma yadda suka gane Yesu yayinda ya kakkarya burodin.

Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi