Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Maris 2027 › Maris 24
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Maris 24, 2027
Laraba · Mako Mai Tsarki
Bukukuwa da waliyyai
Laraba a Mako Mai Tsarki
Ranar mako · Launin ibada: shunayya
Karatun yini
Karatu na farko
4Ubangiji Mai Iko Duka ya ba ni harshen umarni, don in san maganar da za tă ƙarfafa gajiyayye. Ya farkar da ni da safe, ya farkar da kunnena don in saurara kamar wanda ake koya masa. 5Ubangiji Mai Iko Duka ya buɗe kunnuwana, kuma ban yi tayarwa ba; ban ja da baya ba. 6Na ba da bayana ga masu dūkana, kumatuna ga masu jan gemuna; ban ɓoye fuskata daga masu ba’a da masu tofa mini miyau ba. 7Gama Ubangiji Mai Iko Duka zai taimake ni, ba zan sha kunya ba. Saboda haka na kafa fuskata kamar dutsen ƙanƙara, na kuma sani ba zan sha kunya ba. 8Gama shi da zai tabbatar da ni, marar laifi ne yana kusa. Wane ne zai kawo ƙararraki game da ni? Bari mu je ɗakin shari’a tare! Wane ne mai zargina? Bari yă kalubalance ni! 9Ubangiji Mai Iko Duka ne zai taimake ni. Wane ne zai iya tabbatar da ni mai laifi? Duk za su koɗe kamar riga; asu za su cinye su.
Zaburar amsawa
7Gama na jimre da ba’a saboda kai, kunya kuma ta rufe fuskata. 8Ni baƙo ne a cikin ’yan’uwana, bare kuma ga ’ya’yan mahaifiyata maza; 9gama himma da nake yi wa gidanka yana ƙunata, kuma zagi na masu zaginka yana fāɗuwa a kaina. 20Ba’a ta sa zuciyata ta karai ta bar ni ba mataimaki; Na nemi a ji tausayina, amma ban sami ko ɗaya ba, na nemi masu ta’aziyya, amma ban sami ko ɗaya ba. 21Sun sa abin ɗaci cikin abincina suka kuma ba ni ruwan inabi mai tsami sa’ad da nake jin ƙishi. 30Zan yabe sunan Allah cikin waƙa in kuma ɗaukaka shi tare wurin yin godiya. 32Matalauta za su gani su kuma yi murna, ku da kuke neman Allah, bari zukatanku su rayu! 33Ubangiji yakan ji masu bukata ba ya kuwa ƙyale kamammun mutanensa.
Bishara
14Sai ɗaya daga cikin Sha Biyun nan, wanda ake kira Yahuda Iskariyot, ya je wurin manyan firistoci 15ya ce, “Me za ku ba ni, in na bashe shi gare ku?” Sai suka ƙirga masa kuɗi azurfa talatin. 16Daga wannan lokaci, Yahuda ya yi ta neman zarafin da zai miƙa shi. 17A rana ta fari ta Bikin Burodi Marar Yisti, sai almajiran suka zo wurin Yesu suka yi tambaya suka ce, “Ina kake so mu je mu shirya maka wurin da za ka ci Bikin Ƙetarewa?” 18Ya amsa ya ce, “Ku shiga gari wurin wāne, ku ce masa, ‘Malam ya ce, lokacina ya yi kusa. Zan ci Bikin Ƙetarewa tare da almajiraina a gidanka.’ ” 19Saboda haka almajiran suka yi yadda Yesu ya umarce su, suka kuwa shirya Bikin Ƙetarewa. 20Da yamma ta yi, sai Yesu ya zauna don cin abinci tare da Sha Biyun. 21Yayinda suke cin abinci, sai ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.” 22Suka yi baƙin ciki ƙwarai, suka fara ce masa da ɗaya-ɗaya, “Gaskiya nake gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.” 23Yesu ya amsa ya ce, “Wanda ya sa hannunsa a kwano tare da ni ne, zai bashe ni. 24Ɗan Mutum zai tafi kamar yadda aka rubuta game da shi. Amma kaiton mutumin da zai bashe Ɗan Mutum! Da ma ba a haifi mutumin nan ba, da ya fi masa.” 25Sa’an nan Yahuda, wanda zai bashe shi ya ce, “Tabbatacce ba ni ba ne, ko, Rabbi?” Yesu ya amsa ya ce, “I, kai ma ka fada.”
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi