Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Faburairu 2027 › Faburairu 13

Kalandar Katolika

Karatun Mass (Katolika) — Faburairu 13, 2027

Asabar · Lokacin Azumi: kwanakin bayan Laraba ta Toka

Bukukuwa da waliyyai

Asabar bayan Laraba ta Toka

Ranar mako · Launin ibada: shunayya

Karatun yini

Karatu na farko

Ish 58:9–14

9Sa’an nan za ku yi kira, Ubangiji kuma zai amsa; za ku yi kuka don neman taimako, zai kuwa ce ga ni nan. “In kuka kawar da karkiyar zalunci, kuka daina nuna wa juna yatsa da kuma faɗar mugayen maganganu, 10in kuma kuka ɗauki lokaci kuka ƙosar da mayunwata kuka kuma biya bukatun waɗanda suke shan tsanani, sa’an nan ne haskenku zai haskaka cikin duhu darenku kuma zai zama kamar tsakar rana. 11Ubangiji zai bishe ku kullum; zai biya muku bukatunku a ƙasa mai zafin rana ya kuma ƙarfafa ƙasusuwanku. Za ku zama kamar lambun da aka yi masa banruwa, kamar rafin da ruwansa ba ya ƙafewa. 12Mutanenku za su sāke gina kufai na da su kuma daga tsofaffin harsashai; za a ce da ku Masu Gyaran Katangar da ta Rushe, Masu Farfaɗo da Tituna da kuma Wuraren zama. 13“In kun kiyaye ƙafafunku daga take Asabbaci da kuma daga aikata abin da kuka gan dama a ranata mai tsarki, in kuka kira Asabbaci ranar murna rana mai tsarki ta Ubangiji kuma mai bangirma, in kuka girmama ta ta wurin ƙin yin abin da kuka gan dama da kuma yin al’amuranku ko yin mugayen maganganu, 14sa’an nan za ku yi farin ciki a cikin Ubangiji, zan kuma sa ku a kan maɗaukaka ƙasashe ku kuma yi biki a gādon mahaifinku Yaƙub.” Ni Ubangiji ne na faɗa.

Zaburar amsawa

Zab 86:1–6

1Addu’ar Dawuda. Ka ji, ya Ubangiji, ka kuma amsa mini, gama ni matalauci ne mai bukata kuma. 2Ka tsare raina, gama na ba da kaina gare ka. Kai ne Allahna; ka ceci bawanka wanda ya dogara gare ka. 3Ka yi mini jinƙai, ya Ubangiji, gama na yi kira gare ka dukan yini. 4Ka ba bawanka farin ciki gama gare ka, ya Ubangiji, na miƙa raina. 5Kai mai gafartawa da kuma mai alheri ne, ya Ubangiji, cike da ƙauna ga dukan waɗanda suke kira gare ka. 6Ka ji addu’ata, ya Ubangiji; ka saurari kukata na neman jinƙai.

Bishara

Luk 5:27–32

27Bayan wannan, sai Yesu ya fita, ya ga wani mai karɓar haraji, mai suna Lawi, yana zaune a wurin da ake karɓar haraji. Yesu ya ce masa, “Bi ni.” 28Sai Lawi ya tashi, ya bar kome da kome, ya bi shi. 29Sai Lawi ya shirya wa Yesu wani babban liyafa a gidansa. Wani babban taron na masu karɓar haraji, tare da waɗansu suna cin abinci tare da su. 30Amma Farisiyawa da malaman dokokin da suke a ƙungiyarsu, suka yi wa almajiransa gunaguni, suna cewa, “Don me kuke ci, kuke sha tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?” 31Yesu ya amsa musu ya ce, “Ai, masu lafiya ba sa bukatar likita, sai dai marasa lafiya. 32Ban zo don in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi zuwa ga tuba.”

Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi